Masu Rura Wutar Rikici Za Su Fuskanci Fushin Hukuma, Cewar Osinbajo

0
90

Mukaddashin shugaban Nijeriya Yemi Osinbajo yayi kira ga ‘yan kasar masu yin kalaman da ka iya jawo tashin hankali da asarar rayuka da dukiyoyin al’umma, da su daina, ko kuma su fuskanci fushin hukuma.

Mukaddashin shugaban kasar ya yi wannan kiran ne a Abuja lokacin wata ganawar tuntuba da shugabanni da dattawan arewaci da kudu maso gabashin Naijeriya a ranar Talata.

Ya ce, “Zamantakewa tsakanin al’umomin Najeriya, kamar yadda yawancinmu muka sani, ta haifar da kalubale iri-iri”. Yawancin masu halartar wannan taron na yau, shaidu ne ga irin gwagwarmayar da Najeriya ta sha a tarihinta, kawo yanzu. Wannan shi ne dalilin gayyatarku a yau.”

“Wasu kungiyoyi daga kudu maso gabas, kamar IPOB da masu goya masu baya, sun yi ikirarin ballewa daga Najeriya, kuma wata kungiya ta matasa daga arewa sun ba kabilar Ibo mazauna arewacin kasar nan zuwa 1 ga watan Oktoba, shekara ta 2017 da su kwashe inasu-inasu, su bar yankin”, in ji shugaba Osinbajo.

Wannan taron tuntubar shi ne na farko a jerin taruka da mukaddashin shugaban ya shirya yi da shugabanni daga sassa daban-daban na kasar.

Ana sa ran zai gana da sarakunan gargajiya daga arewa, daga baya kuma ya gana da wasu shugabannin al’umomin da na addini daga yankin kudu maso gabas.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here