BABBAN LABARI: Tsakanin Sarki Muhammadu Sanusi II Da Majalisar Dokokin Jihar Kano: Dattawan Da Suka Sasanta Lamarin

0
90

Daga Musa Muhammad, Abuja

Ga dukkan alamu tataburzar da ta barke tsakanin Majalisar Dokokin jihar Kano da Masarautar Kanon ta kawo karshe, inda a ranar Litinin da ta gabata Majalisar ta bayyana cewa ta janye kudurin da take da shi na binciken masarautar bisa zargin da ake mata na almubazzaranci da dukiyar al’umma, sakamakon wata takardar roko da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya aike mata, wanda kuma Shugaban Majalisar, Hon. Kabiru Alasan Rurum ya karanta.

Majalisar da ta dauki wannan mataki ne bisa rokon Gwamnan, inda ya bayyana mata irin manya, kuma fitattun mutane a kasar nan da suka yi ta rokonsa da a dakatar da wannan bincike, wanda kuma Majalisar ta karbi wannan roko na Gwamnan.

A cikin takardar, Gwamnan ya bayyana wa Majalisar cewa gwamnatin jihar Kano ta lura da tataburzar da ke faruwa, inda Majalisar Dokokin jihar ke neman binciken Masaurautar Kanon, “wanda wannan rikici ya samo asali ne sakamakon wani jawabi da Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yi a Kaduna, wanda shi ne ya jawo Majalisar daukar wannan mataki, sakamakon wani kurudin da aka gabatar mata kan haka,” in ji Gwamnan.

Saboda haka sai Gwamnan ya bayyana cewa wannan rikci ya jawo hankalin Gwamnonin Arewacin kasar nan, inda suka kira wani taro, kuma suka gayyaci shi Gwamnan da Sarki Muhammadu Sanusi II a gidan gwamnatin jihar Kaduna, inda aka tattauna muhimman batutuwa. “Wanda bayan nan kuma Mai martaba ya amsa laifinsa, kuma ya roki gafara, wanda kuma an karbi wannan roko nasa,” in ji Gwamnan.

Gwamna Ganduje ya ci gaba da bayyana cewa baya ga Gwamnonin Arewan, akwai kuma wasu kungiyoyi da dama da suka nemi a dakatar da wannan bincike, wadanda suka hada da kungiyar tuntuba ta Arewa, ACF, “da kuma wasu manyan masu fada a ji a kasar nan, musamman Tsohon mai ba Shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Janar Ali Gusau, Alhaji Aliko Dangote, Alhaji Aminu Dantata, Bola Ahmad Tinubu, Tsohon Shugaban kasa Ibrahim Babangida da Janar Abdulsalami Abubakar,” in ji shi.

Sauran manyan mutanen da suka roki a dakatar da wannan bincike, kamar yadda Gwamna Ganduje ya bayyana wa Majalisar, sun hada da Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar, Shugaban Jami’iyyar APC na kasa, Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, sannan da uwa-uba Mukaddashin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.”

Saboda haka sai Gwamnan ya roki Shugaban Majalisar da su dakatar da wannan bincike da suke shirin aiwatarwa. Ya ce, “saboda haka, Mai girma Shugaban Majalisar ina rokon wannan gida ku dakatar da wannan bincike. Ina tabbatar da cewa rufe wannan magana zai zama mai amfani ga kowa.”

In dai za a iya tunawa, a kwanakin baya mun kawo labarin yadda ake neman binciken Masarautar game da yadda ake zarginta da almundahana na Naira Biliyan Hudu, wanda kuma Hukumar yaki da cin hanci ta Kano ta bayyana cewa tana binciken lamarin, wanda daga baya ta bayyana dakatar da bincken nata. Duk da a lokacin Masarautar ta fito fili ta musanta wannan zargi.

Sannan kuma daga baya ita ma Majalisar Dokokin jihar ta bayyana aniyarta ta binciken Masarautar, sakamakon wani kuduri da dan Majalisa mai wakiltar Mazabar Karamar Hukumar Nasarawa, Hon. Ibrahim Ahmad Gama ya gabatar, kafin har aka cimma wannan matsaya.

Hon. Ibrahim Gama ya bayyana wa LEADSHIP cewa tun farko Gwamna Ganduje ya shaida masa irin matsain lambar da yake samu daga manya a kasar nan na a dakatar da wannan bincike. Ya ce kuma Gwamnan ya shaida masa cewa Sarkin ya amsa laifinsa, kuma ya roki gafara a wani taro da aka gudanar a Kaduna.

“Saboda haka sai karbi wannan roko na Gwamna da zuciya daya, na janye wannan kuduri da na gabatar tun farko na neman a abinciki Sarkin, amma na dage a kan bukata ta biyu, wato ta neman a sake fasalin Dokokin da suke lura da masarauta,” in ji Hon. Gama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here