RA’AYINMU Tsakanin Bankuna Da Kamfanoni Masu Zaman Kansu

0
76

Kwanan nan wasu labarai suka rika yaduwa kan yadda wasu bankuna a kasar nan suke kullewa kamfanoni masu zaman kansu asusunsu ba bisa ka’ida ba, tsawon lokaci su yi ta fama suna bibiyar yadda za a bude masu asusun nasu somin su koma ci gaba da gudanar da harkokinsu kamar yadda suka saba.

Cikin kamfanonin da suka tsinci kansu kansu a irin wannan badakala akwai Cashflow, wanda aka kafa domin tallafawa marasa karfi ta hanyar koya masu sana’a da ba su jari. Sai dai kusan shekaru bakwai asusun wannan kamfani da ke Banki Diamond an kulle shi, saboda haka ba su da ikon gudanar da wata hada-hada. Sun yi iya bakin kokarinsu don ganin an bude asusun amma lamarin ya ci tura, duk da cewa sun bi hanyoyi da suka dace bisa doka don dawo da dukiyarsu da ke neman kubucewa.

Daga cikin matakan da suka fara dauka sun hada da garzayawa babbar kotun Abuja, inda kotun ta bada umarni a bude masu asusun tun wasu lokuta a baya, amma dai wasu dalilai suka hana bankin bude asusun.

Wasu daga cikin manyan jaridun kasar nan sun rawaito, a makon da ya gabata, Majalisar Tarayya ta kafa wani kwamiti domin jin yadda Bankin Diamond ya rufe asusun kamfanin Cashflow tsawon shekaru, ta yadda ba su da damar ci gaba da hada-hada da abokan huldarsu akalla na tsawon shekaru bakwai, shugabannin kamfanin sun iya bakin kokarinsu don ganin an bude asusun domin su bawa abokan cinikiyyarsu damar hulda kamar yadda suke yi a baya.

Wannan lamari ya tagayyara dubunnan mutane, domin masu hulda irin wadannan bankuna suna da yawan gaske, kuma da suna kwastomomi a karkashinsu wadanda ke zuba hannayen jari ko karbar rance.

Abin lura shi a nan, mutane da yawa wadanda suke hulda da ire-iren wadannan kamfanoni sun shiga wani hali, wanda kamata ya yi a ce hukumomin da abin ya shafa su kalli lamari da idon basira domin fitar da jaki daga duma. Sha’anin kudi abu ne mai wuyar gaskiya, domin a wannan zamani suna cikin sinadaran gyara rayuwar dan adam da kuma lalata su.

Wadanda suka tsinci kansu a wannan yanayi sun shiga mummunan hali, da yawansu sun kasa biyawa ‘ya’yansu kudaden makaranta, wasu abinda za su saka a bakin salati ma gagararsu yake yi.

Daya daga cikin wanda bala’in kulle asusu da bankin Diamond ya shafa, a wata hira da aka yi da shi a gidan jaridu, ya bayyana irin wahalar da suka sha tsawon shekaru bakwai suna fama a bude masu asusu amma lamarin ya ci tura. Ya koka matuka, a cewarsa da kudinsu na haram ne ai da tuni hukuma ta kama su, amma kudaden da suke juyawa na hada-hadar ciniki ne da tallafawa mutane da jari, amma yanzu komai ya tsaya cak saboda makarkashiyar da aka shirya masu.

A wannan gabar, da lamarin ya kai Majalisar Wakilai, har ma ta gayyato Babban Bankin Kasa, Bankin Diamond da Hukumar EFCC, hatta jagoran kwamitin da Majalisa ta kafa don binciken badakalar, Nkem-Abonta, ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda CBN ke hada kai da bankunan ‘yan kasuwa ana cutar da kwastomomi, inda ya ce bankunan da suka yi kaurin suna a wannan fanin sun hada da First Bank, Sky Bank da sauran su.

A karshe ya bukaci a samar da wani wuri na musamman domin haduwa da dukkan wadanda abin ya shafa don duba yiwuwar dawo masu da hakkinsu. Cikin wadanda ake sa ran za su halarci zaman a 30 ga watan nan, akwai Babban Sufeton ‘Yan Sanda Ibrahim Idris.

A namu ra’ayin, muna ganin adalci ya kamata a yi wa ire-iren wadannan mutane da suka himmantu wajen neman na kansu da kuma tallafawa marasa karfi da sana’o’i ta yadda za su dogara da kansu. Bai kamata a ce mutumin da yake kokarin kafa kasuwancinsa har ma ya taimaki wani, a hada baki da wasu tsirarun mutane a tagayyara shi ba, wajibi ne ga mahukunta su yi nazarin halin da wadannan bayin Allah suke ciki domin fitar da su daga mummunan yanayi.

Kowa yana sane da irin halin da ake ciki a kasar nan na talauci da rashin gilmawar kudi, kuma gwamnati na iya bakin kokarinta wajen bullo da sabbin dabarun warware matsalolin da al’umma suke ciki, a hannu guda, daidaikun mutane suna amfani da nasu ikon domin ganin an hada hannu da karfe wajen samawa matasa ayyukan yi.

Lallai lokaci ya yi da ya kamata a daina kashin dankali a kasar nan, a sakarwa ‘yan kasa nagari mara su fitsari, ba wanda zai cutar da al’umma ba, wanda zai taimaka wajen ci gaban kasa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here