TATTAUNAWA: Yadda Ake Shirin Gudanar Da Azumi Cikin Matsin Rayuwa

0
98

Daga Abdullahi Usman, Kaduna, Muhammad Awwal Umar, Minna, Sagir Abubakar, Katsina, Khalid Idris Doya, Bauchi da Hussaini Ibrahim, Gusau

Gobe ake sa ran fara Azumin watan Ramadan wanda ya kasance wata mai alfarma ga daukacin Musulmin duniya. Azumi na daya daga cikin shika-shikan Musulunci. Kan haka wakilan mu suka zaga dan jin ra’ayin jama’a kan yadda suke fuskantar wannan watan.

  • Kaduna

Wakilinmu a Kaduna ya zanta da wani tsohon dan siyasa, Alhaji Umar Muhammad kuma tsohon ma’aikacin banki, ya shaida cewar “gaskiya sai dai mu gode wa Allah domin ban taba shiga halin rashi ba kamar yadda na shiga a wannan lokaci. Ban taba zaton zan wayi gari na abincin da za a ci a gidana ya gagara ba, sai a wannan lokaci. Domin ni yanzu ba ta azumi na ke yi ba. Ina ta abinda za a ci yau ne.

“Don haka ina kira ga gwamnatoci da su yi abin da ya kamata don tallafawa al’ummarsu a wannan lokaci da za mu fara azumin wata mai alfarma.  Domin tta wannan rayuwa gaba daya abu biyu ne. Wato ciyarwa da aminci, ko tsarin mulkin Nijeriya da abin da ya fara kenan, Wato Kyautatawa, Jin Dadi da kuma Tsaro, saboda haka akwai aiki babba ga Gwamnati don talkafawa al’umma.”

Shi ma Malam Ahmad Salihu, wanda dan kwangila ne, ya bayyana cewa suna cikin wani hali wanda ba abin da za su ce illa su gode wa Allah. Ya ce akwai bukatar masu hannu da shuni su taimakawa mara sa karfi a wannan lokaci da ake fama da talauci a kasar nan.

Sannan ya nemi gwamnati da ta hada karfi da ‘yan kasuwa don ganin ba a kara farashin kayayyakin masarufi ba a wannan lokaci. Ya ce akwai ‘yan kasuwar da suke jiran irin wannan lokaci don su uzzurawa al’umma.

Malam Huzaifa Muhammad, ma’aikacin gwamnatin tarayya ne. Ya bayyana cewa ba wanda ya kai su shan wahala a kasar nan. Ya ce albashin su na nan yadda yadda ke amma kayan abinci sun yi tsada.

Malam Muhammad Abubakar Auta, dan kasuwa ne a kasuwar Shaikh Abubakar Mahmud Gumi da ke Kaduna, ya bayyana wa Wakikinmu cewa su ma suna cikin tasku domin halin da ake ciki a kasar ya sanya ba sa samun ciniki yadda yadda kamata.

Ya ce a shekaru biyu da suka wuce akwai ranar da ya ke yin ciniki har na naira miliyan daya, amma yanzu da kyar yake samun cinikin dubu 10

Shi kuwa Alhaji Abubakar Usman cewa ya yi abin da ya kamata shine mutane su gode wa Allah a kodayaushe, domin kowane tsanani ya zo, to akwai sauki a bayansa. Don haka kada mutane su rinka cewa wani ne ya kawo matsalar da ake ciki. Ya ce da yardar Allah za a kammala azumi cikin wadata da karuwar arzikin.

 

  • Neja

Malam Nuhu Umar Muhammad dan kasuwa ne mazauni garin Kontagora, ya bayyana cewar maganar shirye-shiryen Azumin Ramadan, ai ba wani shiri illa duk yadda ta zo haka za a fuskance ta, irin halin matsin rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki, domin a matsayinsa na talaka kuma dan kasuwar da bai da wadataccen jari sannan ga yadda su ‘yan kasuwa suke fuskantar kalubale na rashin ciniki da matsi daga wajen gwamnati akan haraji abin ba a cewa komai.

Ya ce, “Idan kana maganar an yi noma an samu abinci ne, lallai idan ka shiga daji abin da sha’awa domin ga abinci nan ya yi albarka, amma idan ka shigo gari abincin bai tabuwa saboda tsada kuma ga rashin kudi a hannun jama’a. Ka ga abinda na fahimta Kundin Tsarin mulkin kasar nan babu ruwansa da addini amma kuma mafi yawan masu mulki kashi tamanin da biyar cikin dari masu addini ne, sai na ke gani kamar giyar mulki da keta irin na ‘yan jari hujja ba zai bawa talakan kasar nan ya samu walwalar da zai iya moriyar arzikin kasar ba.

“Babban abin farin ciki dai an fara samun sauki akan tashe-tashen hankula na zubar da jini amma yunwar da ke addabar talakawa yanzu na daya daga cikin abinda zai hana mu samun yalwa a Ramadan nan mai karatowa, amma muna shawartar Gwamnatoci da sanya tausayi da tsoron Allah a cikin lamurransu, su kuma manyan ‘yan kasuwa su daina boye kaya a cikin ma’ajiya da tunanin tsadanta shi a lokacin Ramadan.”

Shi ma Malam Musa Yakubu Maishayi, cewa ya yi ba wani shiri talaka zai yi, illa ya jira idan an ga wata ya dau Azumi idan an gani ya aje.

Ya ce, “idan ana maganar shiri to daman an yi tanadi ke nan. Ka wai gwamnatin jiha ta biya albashi ga alama abubuwan za su yi sauki, to wa aka biyawa albashin, ina ce ma’aikacin gwamnati ne ko, to nawa ne kudin, jihar nan na daya daga cikin jahohi mafi tauye albashin ma’aikata fa.

Malama Tani Haruna wata da ke goyon marayu ta shaida ma wakilin cewar ita kan maganar shiri ba ta shirya komai ba, a shekarar da ta gaba ta a irin wannan lokacin tana da wadataccen geron kunu da zai iya kai ta rabin Ramadan, amma a bana ko mudu ba ta ajiye ba balle ta yi tunanin shirya wani au, za dai ta yi amfani da abin ya zo hannunta ne kawai.

“Ina fatan masu hali da kwamitocin da ake kafawa a kungiyoyi zasu taimaka kamar yadda suka saba lallai da mun samu rahusa, amma dai a bana za mu yi Azumi ne cikin yanayi idan an samu a ci, idan kuma mun kai Azumin babu rungumi abinda Allah ya tsara mana.” In ji ta

 

  • Katsina

Tuni shirye-shirye sun kankama game da azumi a cikin birnin jihar Katsina. Sai dai wannan shekarar ta sha bamban da sauran shekarun da suka gabata saboda hauhawar farashin kayan abinci. Mafi yawan jama’a suna kokawa game da tashin gwauron zabi da abinci ya yi a kasuwanni da ma wasu sassan jihar nan.

A inda shinkafa, da gero, da masara, da wake suke neman fin karfin talakawa sakamakon matsin tattalin arziki da ya fuskanci talakawan kasar nan. Wanda jama’a da dama sun yi tsokaci akan hakan.

A sabili da haka ne ma su kansu malamai da limamai suka yi kira ga masu hannu da shuni na jihar Katsina da su dubi girman Allah su taimakawa talakawa watau fakirai domin samun falala daga Allah.

Kamar yadda wani malami ya bayyana cewa watan Ramadana a matsayin watan da ya fi kowa ne wata daraja kamar yadda aka bayyana a cikin Al-Kur’ani mai girma.

Babban malamin mai suna Malam Abdurrahman Sabi’u shi ne limamin masallachin juma’a na Kofar Kaura dake nan cikin birnin Katsina ya bayyana cewa sahabban manzon Allah (S.A.W) suna nuna zakuwa da kuma gudanar da addu’o’i dare da rana domin Allah ya kai su watan Ramadan don haka malamin ya yi kira ga al’ummar musulmi da su shiryama shigowar azumin watan ramadan domin samun gafara daga Allah subhanahu wata’ala game da matsalar tattalin arziki da mutane suke fuskanta yana faruwa ne a sanadiyar gudanar da ayyuka marasa kyau da mutane ke aikatawa. Saboda haka ya yi kira ga masu hannu da shuni domin taimakawa marasa galihu.

 

  • Bauchi

Wakilinmu ya zanta da daya daga cikin malaman addinin musulunci a jihar Bauchi Malam Muhamad Babangida Sulaiman, wanda kuma shi ne babban limamin masallacin Abu Huraira da ke GRA Bauchi domin jin abubuwan da azumin ya kunsa.

Malamin ya fara ne da bayyana cewar shi dai azumin watan Ramadan wajibi ne akan kowani musulmi, “watan azumi wata ne mai daraja, a cikinsa ne aka fara saukar da Alkur’ani mai girma, a cikinsa ne Allah ya taimaki musulmai suka yi nasara yakin Badara, haka kuma a cikinsa ne Allah ya albarci musulmai da wata dare kwara daya wacce ibada a cikinta ya fi ibada a cikin shekaru 83. A cikin watan nan ne ake sauki alkairai masu tarin yawa da kum yafiya.”

Ya ci gaba da cewa, “Akwai bukatar musulmai ya kasance yana ciyarwa a watan azumi, sadaka da kuma kyautata wa jama’a, ibada da kuma dagewa wajen cin halas a cikin wannan watan.”

Ya shawarci al’ummar musulmai da su kasance masu yin iya yinsu wajen yin bude baki da kuma yin suhur da halaliyarsu, ya ce an fi son mutum ya tarbi watan Ramadan da kyawawan dabi’u.

LEADERSHIP Hausa ta tuntubi wasu ma’aikatan jihar Bauchi don jin yanayin walwala da kuma hasashen shiga watan azumi, sun bayyana cewar ma’aikata sai dai su yi addu’a domin rayuwarsu na cikin garari, “akwai ma’aikatan da ke bin albashi ba a biya su ba; muna fatan gwamnatin jihar nan za ta taimaka wa ma’aikata domin mu samu mu shiga watan azumin cikin walwala da kuma jin dadi. ‘yan fansho kuma muna kara kiran gwaman jihar nan da yi kokari biyansu domin wasu na cikin damuwa wallahi”. A cewarsu

Ta fuskar hada-hadar kasuwanci kuwa, wakilinmu ya shaida mana cewar an yi nasara ta fuskokin yawan kara kudaden kaya da wasu manyan ‘yan kasuwa ke yi idan suka ga lokacin wasu bukukuwa ya karato, inda har zuwa yau ba a samu yawaitar wannan korafe-korafen a wajen masu sayen kayayyakin amfanin yau da gobe ba.

 

  • Zamfara

A Jihar Zamfara wadda ke kokarin kamanta Shari’ar Musulunci a Gwamnatance, tana bada tallafi ga marayu da marasa karfi a tun a farkon watan, kuma tana fidda cibiyoyi da manyan masallatai domin dafa abinci ga al’ummar fadin jihar, masu hannu da shuni, da wasu kofofin gidajen ana bude su domin ciyarwa a cikin watan, amma ga ‘yan kasuwa kadan ne masu saukaka farashi; da yawansu sukan karawa kayansu farashi musamman kayan abinci.

Haka zalika, Malam suna baje basirar karatun wajen gudanar da tafsiran Alkur’ani, inda wasu ke amfani da wannan damar wajen sukan wadanda suke da sabanin akida a tsakaninsu.

LEADERSHIP Hausa ta nemi jin ta bakin Malam Ali Fari Gusau kan ko wane tsokaci ne zai yi ga al’umma da Malamai game da wanna wata mai alfarma? Malamin ya fara da bayyana, “Tsoran Allah da tausayi, Allah ya sanya wa kowa, sai dai Dan’Adam ya yi butulci kan haka. Ita ciyawar hatta a lokacin da ba na azumi ba, sai mutumin da yake da tausayi da imani.

Batun Malamai masu Tafsiri kuwa Malam Ali Fari ya bayyana cewa, duk malamin da ya fasara aya don San ransa ko biya ma wani bukata lallai zai gamu da Fushin Allah.

Alhji Musa’Yar Dutse Gumi, shi ma ya yi kira musamman ga al’umar ‘yan kasuwa su zamo masu tausayi da jin-kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here