Me Ya Sa Sakataren Watsa Labaran PDP Na Sokoto Yin Murabus?

0
83

Daga Wakilinmu

Sakataren jam’iyyar PDP na jihar Sokoto, Alhaji Yusuf Dingyadi ya bayyana ajiye mukaminsa a ranar Lahadin da ta gabata bayan ya share fiye da shekara daya yana yi wa jam’iyyar hidima a jihar da ma kasa baki daya.

Alhaji Yusufa ya bayyana haka ne shafinsa na sada zumunta Facebook, inda ya bayyana cewa wannan ajiye aiki ya biyo bayan kammala wani taron shugabanin kwamitin zartaswa ne na masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a ranar Lahadin a  gidan Shugaban jam’iyyar, Alhaji Ibrahim Milgoma da ke Sokoto.

Alhaji Yusuf, wanda kuma sannanen dan jarida ne, ya bayyana daukar wannan mataki ne da ya samu a sanadiyyar wasu dalilai masu nauyi don kauce wa shiga wani yanayi, wanda yake daban da ci gaban zamantakewa. Ya ce, akwai dalilai da suka sanya ya ajiye mukamin bisa ga yadda tsarin shugabancin jam’iyyar ya nuna a fili ya kauce daga neman samar da hanyar ciyar da jam’iyyar PDP da magoya bayanta gaba, ta koma wata mahada na fadanci da biyan wata bukata, abin da ya kauce wa ainihin tafarkin adawa da jam’iyyar take a yanzu.

Ya ce jam’iyyar na ci gaba da fuskantar matsaloli a bayyane, amma an ki fahimta a karbi gyara ko daukar mataki, saboda wasu na ganin za su rasa abincinsu ko wata kima, abin da ya janyo ana hasarar magoya baya ko kuma yin ko oho da lamurran da suka shafi adawa; ba tare da bayyanawa a fili inda aka nufa ba, don kauce wa shiga rudu da rashin alkibla.

Alhaji Yusuf ya ce, “wasu ’yan kalilan sun zama duhu ga wannan tafiyar, don ba su bukatar wasu su matso a ci gaba, ta yadda kowa zai more da samar da ci gaban jam’iyya a jihar Sokoto, ta yadda nauyin zai yi sauki ga jagoran tafiyar da muke yi wa biyayya.”

Ya ce, “kusan koyaushe ana fitar da bayanai wadanda a zahirance ba haka lamarin yake ba, haka wasu sun yi watsi da amanar da aka dora masu ta komawa ga jama’arsu don ciyar da jam’iyya gaba; maimakon haka sun buge da fadanci da yawan karairayi na haddasa fitina da janyo wata kiyyaya tsakanin wasu da ke da muhimmanci ga bayar da taimako da ciyar da jam’iyyar gaba.”

Dingyadi, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin Sakatarorin Watsa Labarai na jihohin Arewa 19, ya bayyna cewar ajiye mukaminsa bai hana shi ci gaba da nuna goyon bayansa ga jam’iyyar PDP ba.

Alhaji Dingyadi ya kuma tabbatar da goyon bayansa da biyayya ga Alhaji Attahiru Bafarawa, ya nuna godiyarsa ga dukkan shugabani da magoya bayan jam’iyyar PDP na jihar Sokoto dangane da damar da suka ba shi wajen gudanar da ayyukansa. Sai dai ya ce dole ne yanzu ya dauki mataki daga irin abin da ke faruwa cikin jam’iyyar a jihar Sokoto saboda kauce wa fadawa cikin wani yanayin da magabata ba su koya masa ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here