KASASHEN WAJE: Kamaru Ta Tsare Sojojin Da Ke Yaki Da Boko Haram

0
41

Hukumomin Kamaru sun kama akalla sojoji 30 da ke yaki da kungiyar Boko Haram saboda boren da su ka yi kan kin biyan su wasu kudade na alawus da na hutu.

Sojojin sun yi bore a ranar Lahadin da ta gabata a yankin arewacin kasar, inda suka tare hanyoyin zirga-zirgar mota.

Ma’aikatar tsaron kasar ta ce, yanzu haka an kwashe sojojin daga yankin Zikue zuwa birnin Yaounde, in da ake tsare da su.

Rahotanni sun bayyana cewa, harkokin yau da kullum sun koma yadda aka saba bayan boren sojojin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here