Kotu Ta Kori Dan Sanda, Sanadiyyar Wawushe Gidan Jonathan

149

Rundunar ‘yan sandan Abuja, ta kori jami’in dan sanda Sajen Musa Musa wanda da ake zargi da hannu a wawushe wani gidan tsohon shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan, da ke unguwar Gwarimpa a Abuja.

A sanarwar da rundunar ta fitar ta ce bayan an gudanar da bincike kuma an samu dan sandan da ke gadin gidan tsohon shugaban kasan da hannu cikin satar da aka yi a gidan.

Rundunar ta kara da cewa, an gurfanar da wanda ake zargi da aikata laifin, Sajan Musa Musa, a gaban kuliya a kotun Majistare da ke unguwar Wuse ne yau a Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here