Zazzabin Lassa Ya Kashe Mutum Biyu A Lagos

112

Hukumomi a jihar Lagos sun  tabbatar da mutuwar mutum biyu  sakamakon  cutar zazzabin Lassa wadda bera ke yadawa.

An tabbatar da cutar ne sakamakon binciken da asibitin jami’ar Lagos ta yi a yau Talata.

Babban Darektan asibitin Jami’ar Jihar Lagos (LUTH) Chris Bode, ne ya bayyanawa manema labarai sakamakon binciken da likitocin su ka yi.

Rahotan ya kara da cewa, ma’aikatar lafiya ta jihar na kokarin dakile yaduwar cutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here