Ya Kamata Benzema Ya Dawo Buga Wa Faransa Wasa -Samir Nasri

190

Tsohon ɗan wasan ƙasar faransa, karim Benzema ya soki mai koyarda tawagar yan wasan ƙasar faransa, Didie Deschamp, inda yace bai kamata ace har yanzu ba’a kiran ɗan wasan ba domin yacigaba da wakiltar ƙasar.

Ɗan wasa  Benzema dai an dena kiransa a ƙasar faransa ne kusan tsawon shekara daya tun bayan da aka fara tuhumarsa da daukar wani fefen bidiyo wanda ya nuna ɗan wasan ƙasar ta faransa, Mathieu Balbuena yana lalata da wata yarinya.

Tun daga wannan lokaci dai ƙasar faransa ta dena kiran ɗan wasan sakamakon wannan fefen bidiyo inda tuni ɗan wasan, Balbuena yace maganar ta wuce.

Nasri, wanda rabon da ƙasar faransa ta kirashi wasa tun shekara ta 2013 yace abinda akeyiwa Benzema bai kamata ba kuma yakamata ace komai yawuce ancigaba da buga wasa dashi.

Yaci gaba da cewa ina tausayawa Benzema, domin yanason bugawa ƙasar sa wasa amma andena kiransa saboda wani dalili wanda tuni ya wuce.

Yace idan faransa tayi amfani da Mbappe da Griezman da Ousman Dembele sannan ga Benzema zasu taimakawa ƙasar sosai, amma sun nuna basason hakan.

Nasri dai a yanzu haka yana taka leda a ƙasar Turkiyya da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Galatassary.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here