Kasafin Kudin Shekarar 2018: Gwamna Badaru Ya Gabatar Da Naira Bilyan N134.17

51

Daga Munkaila T. Abdullah, Dutse

A Jiya ne Gwamna Muhammad Abubakar Badaru ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2018 naira bilyan N134.17 gaban majalisar Jihar Jigawa.

Kasafin kudin wadda ya karu da kaso 3.3 cikin dari kan Kasafin kudin shekarar 2017, an yi masa lakabi da ’Kasafin kudi dan habaka tattalin arziki da jindadin al’umma’.

Gwamna Badaru ya bayyana cewa, gwamnatin tasa zata shiga shekara ta 2018 da rarar zunzurutun kudi har kimanin naira bilyan goma.

Haka kuma ya ce, kimanin naira bilyan N65.535 wadda yayi dai dai da kaso 48.8 cikin dari na jimillar kasafin kudin za a yi amfani dasu wajen gudanar da manyan ayyuka da kuma gudanar da ayyukan yau da kullum.

Kasafin kudin wadda aka warewa fannin Ilimi zunzurutun kudi har kimanin naira bilyan N17.76 dai dai da kaso 26 cikin dari na kasafin, ya kasance fannin da ya zarta kowanne fanni samun kaso mafi tsoka a kasafin kudin na wannan shekara.

Sannan Gwamanan ya kuma ayyana tsabar kudi har kimanin naira bilyan N6.76 wadda yayi dai dai da kaso goma cikin dari na kafatanin kasafin kudin a matsayin kudaded da aka ware domin fannin lafiya a shekarar ta 2018.

Harwayau an ware tsabar kudi har kimanin naira bilyan N9..3 domin fannin noma da kuma naira bilyan N7.2 domin fannin tituna, gamida naira bilyan 2.24 wadda aka warewa fanin mata da walwalar jama\’a, da kuma naira bilyan N2.76 domin fannin samarda ruwan sha.

Haka kuma gwamnan ya gabatar da zunzurutun kudi har kimanin naira bilyan N56.496 a matsayin kasafin kudin kananan hukumomi 27 dake fadin wannan shekara wadda ya karu da kaso 14 cikin dari akan shekarar da ta gabata ta 2017.

Shi kuwa bayan karbar kasafin kudin na wannan shekara ta 2018, shugaban majalisar jihar ta Jigawa Alhaji Isah Idris Gwaram, ya yabawa gwamnan bisa gabatar da wannan kasafin kudi akan lokaci, gamida shan alwashin bibiyar kasafin kudin akan lokaci tareda amincewa da shi domin al’ummar jihar Jigawa su cigaba da kwankwadar romon dimokradiyya karkashin wannan gwamnati ta APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here