Baiwar Da Allah Ya Yi Wa Rakumi A Cikin Dabbobi

1005

Allah Mai halitta. Ba dukkanin sassan Arewacin kasarnan ne suka san baiwar da Allah Ya yi masu ta hanyar samar masu da dabbar gida da ake kira Rakumi ba. Har gobe, a wasu sassan ma na Arewacin Kasarnan, Rakumi bako ne kuma abin kallo. Amma da al’ummanmu sun fahimci irin baiwar da Allah Ya yi wa wannan dabba da ake kira Rakumi, tabbas da zai yi wuya ka sami gidan da babu Rakumin.

LEADERSHIP A Yau Juma’a ta lura cewa duk wani abu da ke tattare da Rakumi yana da nasa sirrin na fa’idantarwa kamar yadda masana suka bayyana. Kar ka ce Namansa kawai nake nufi sam, Kashinsa, Fitsarinsa, Jininsa, Gashin Jikinsa da duka abin da ke tare da shi na boye da na sarari, duk ba bu na yarwa, sai in ba ka ilmantu da sanin alfanunsa ba.

A cikin wannan gajeren binciken da Wakilinmu HUSAINI YARO ya yi a kan Rakumin, mai karatu za ka iya fahimtar kadan daga cikin fa’idojin da ke tattare da wannan dabba ta Rakumi.

A sha karatu lafiya:

 

Ya zo a cikin Litattafan addini, musamman a cikin littattafan da suka gabata kamar su Attaura da Linjila, wadanda a yanzun ake cewa, Baibul, kamar dai yadda ya zo a cikin Alkur’ani Mai Girma, yanda Allah Ya bayyana darajojin Rakumi da kuma sirrukan da yake dauke da su.

A binciken da na yi a takaice, Sama da shekaru Dari Biyu ne Tarihi ya yi bayanin zuwan Rakumi Kasar Hausa, Kuma an zo da shi ne daga Kasar Aljeriya, ta fuskacin yankin Borno da ke gabashin Kasarnan. Larabawa ne ke Safara da Rakumai don jigilar Hajojinsu daga Aljeriya zuwa nan, a shekara ta, 1862.

Haka ma daga Agadas ta Kasar Jamhuriyar Nijar, Buzaye sukan kawo Rakumma zuwa Jihar Sakkwato inda suke jigila da su a wasu sassan Kasarnan. Da jimawa Rakumi b abako ne ba musamman a Kananan Hukumomin Kware, Gwadabawa, Tambuwal, Raba, da Karamar Hukumar Gada. Kasantuwa wadannan Kananan Hukumomin kusan duk cikansu a cikin Sahara ne suke, shi ya sanya suka fi amfani da Rakumin wajen zirga-zirga da kuma jigilar kayayyakinsu.

Babu shakka Jihohin da ke makwabtaka da Kasashe masu Sahara kamar,  Jihar Borno, Jigawa, Sakkwato da Kebbi ,suna matukar amfana da Rakumma, wajen jigilar kayayyaki, kuma ya taimkawa masu safarar da ake kira da Fasakwari, wajen kauce wa Jami’an tsaro. Kasantuwar Rakumma din sub a ruwansu da Boda. Dalili Kenan da a yanzun haka, yawancin masu Fasakwarin Shinkafa, Man girki da makamantansu, duk Rakumma ne hanya mafi saukI a garesu wajen aiwatar da Sana’o’in nasu, daga Jamhuriyar Nijar zuwa cikin wannan Kasa ta mu.

Kuma tabbas Safara da Rakumma, ya bunkasa arzikin Jihohin da ke makwabtaka da Jamhuriyar Nijar, Cadi da Kamaru.

Kuma zuwan Rakumma sun saukakawa Shanu ayyukan gona, irin su huda da Noma da daukar kayan amfanin gona. A yanzun haka, Matasan Jihar Sakkwato, Zamfara, Kebbi, Jigawa da Borno, duk sun fi dogara da Rakumma wajen jigilar kayayyaki.

Muhammadu Giwa Tabanni, Matashi ne wanda ya dogara da Rakumi wajen kawo masa kudin shiga, da Rakumin ne kuma yake jigilar daukar kaya, kamar dai yadda yake amfani da shi a dukkanin ayyukan Nomansa.

Muhammad Giwa tabanni da ke cikin Karamar Hukumar Tsafe, ya bayyana wa Wakilinmu cewa, ‘Shekaru Takwas kenan da yake amfani da Rakumi wajen jigilar daukar kaya da Noma. Don a kullum yana aikin Naira Dubu Bakwai shi kadai, ba kamar Shanu ba, sai ka hada guda biyu za su iya maka huda ko Noma. Amma shi Rakumi Daya tal, yana aikin da Shanu Biyu ba sa iya yi. Yana da juriyar aiki idan ka fita tun da Asuba, kana iya kaiwa karfe Uku na Rana kana aiki da shi, sabanin Shanu da zaran Rana ta fito zuwa goma na safe ko Shadaya dole ka tashi. Idan ba haka ba lallai suna iya durkushewa, karshe ma su mutu, don haka mai hudar Shanu kodayaushe yana tare da wuka, da zaran Shanun sun sare suna iya mutuwa sai ya yi sauri ya yanka don kar ya yi asara.

Kuma shi Rakumi, yana da juriyan gaske da daure wa wahala, kuma ya lura da yadda ka ke tafiyar da rayuwarsa ba ya daukar wulakanci. Kuma shi Rakumi ya fi Shanu tsada, don wannan da ka ke gani, Naira Dubu Dari biyu da Hamsin (N 250,000.00) na saye shi, yau shekaru takwas kenan ina aiki da shi.

Kuma yana rashin lafiya kamar sauran dabobi, kuma ana yi masa allura, idan kuma Jini ya yi masa yawa sai a tsattsaga wuyansa, ta haka jinin ke raguwa, har ya kara samun cikakken lafiya. Batun abinci kuwa, yana cin kayoyi da ganyaryaki da hakukuwa. Don haka ma komai nasa magani ne, misalin Fitsarinsa idan yana yin sa, yana zuba a jikin bindinsa ne. Idan yara suna yin tarin lala aka sa bindin Rakumin a cikin ruwa aka girgiza aka baiwa mai ciwon, shikenan sai ka ga Allah Ya dauke ciwon. Batun shan ruwansa shi ma yana da ban al’ajabi, idan ya sha sau daya, sai ya yi sati daya bai sha ba. Musamman lokacin sanyi, amma a lokacin zafi, ba ya sati guda. Kai Malam Rakumi yana da abubuwan al’ajuba da yawa wadanda ba sa kidayuwa.

Sama’ila Rabi’u, shi ma gidansu sun tashi sun ga iyayensu na amfani da Rakumma ne wajen daukar kaya da Noma, ga abin da yake cewa, “Lallai idan kana da Rakumi, Allah Ya ba ka rufin asiri, don mu shi ne harkar da iyayenmu suka dogara a kai. Kuma shi Rakumi idan ya balaga, yana da riko don haka kyautata masa shine ya fi, ba ya mantuwa kuma baya yafiya, ko-ba-dade-ko-ba-jima, in dai ka yi masa abu da gangan, lallai sai ya hakeka kuma ya rama. Kuma muna taimakawa Jama’a da Fitsarinsa da bayan gidansa, don yin magungunan cututuka daban-daban.

Dakta Bello Mai Nasara, na daga cikin masu kula da lafiyar dabbobin da ake yankawa a Abatuwa da ke cikin Gusau Hedikwatar Jihar Zamfara, ya yi mani tsokaci a takaice, a kan Rakumi kamar haka, Shi Rakumi wata halitta ce da Allah Ya yi shi na musamman, kuma Allah Ya kebance shi da wasu abubuwan al’ajibai a kan dabbobi. Don haka shi Rakumi, Allah Ya hore masa rayuwa a cikin Sahara da inda ma ba Saharan ba.

Tsawon da Allah Ya yi wa Rakumi, yana taimaka masa wajen dauke zafin Sahara da zafin yashi, idan zafin Sahara ya taso kafin ya kai ga jikinsa iska ta yi gaba da shi, sabanin Shanu da sauran dabbobi, da su ke dab da kasa ba sa iya rayuwa a Sahara.

Takonsa kuwa, garkuwa ne a wajen tafiya, saboda yadda Allah Ya yi sa da fadI, wannan fadin takon, na hana shi nutsewa a cikin Sahara da kuma tabo, don haka babu inda bai iya shiga da kafarsa.

Kuma abin da ya sa Rakumi yake kwanaki bai sha ruwa bas hi ne, a cikinsa yana da sassa uku ne, sabanin na sauran dabbobi  kamar su Shanu, Awakai da Jakai, su duk suna da sassa Hudu ne, ba su da karfin aje Ruwa. Shi kuwa a sassansa yana da abin da ake cewa, ‘Papilla’ watau muna iya kiran ta da Rizabuwa, wacce ke aje masa ruwa ya yi kwana da kwanaki.

Kuma tabbas masana kiwon lafiya sun tabbatar da cewa, akwai magunguna dauke da Rakumi, misalin a hantarsa da Kodarsa, akwai magungunan da su ke yi.

Kuma abin da ya sa shi Rakumi ba a yanka shi shi ne, Babbar jijiyar sa na cikin madaciyarsa, kuma can take a ciki ba kamar ta Shanu ba da sauran dabbobi ba, da suke a fili. Don haka shi Rakumi soke Jijiyoyin a ke yi, kuma da zaran an soke nan da nan yake mutuwa cikin mintuna da ba su wuce biyu ba zuwa uku. Amma shanu da sauran dabbobi wadanda jijiyoyinsu ke a fili, su kan kwashe mintuna biyar har zuwa bakwai ba su mutu ba.

Shi ma Dakta Nura Salihu Gwale Kano, Malami ne na Addinin Musulunci, ya bayyana mana cewa, ‘Rakumi ba shi da madaciya, amma akwai wata jaka a jikin hancinsa mai kama da madaciya, wannan jakar jikinta miyau ne, wanda yake tahowa cikin bakin Rakumin, yake zuba wa sauran halittu sinadarin da ke jikinka, ka zauna lafiya yana cikin wannan miyau, don Allah a jaraba idan aka je aka samu hantar Rakumi, a ciro wannan miyau din a zuba shi a cikin kwalba, a kaiwa mai ciwon idon da ba ya gani, ya dinga yin tozali a idan yana sawa, kuma ya dauki kwali ya sa a ciki ya zuke wannan ruwan, ya sa a maida shi kwalli, zuwa sati biyu sati uku ya ga abin mamaki.

Likitan ya kara bayyana cewa, ‘Miyan jikin hantar Rakumi jama’a, ga rantsatsun sinadari mu taimakawa jama’a da tsaffi, ko mai gani hazo-hazo daga dan shekara Arba’in zuwa shekaru arba’in da biyar, koma kan Rakumi, duk cutar da take kassara mutum ya nemi Hantar Rakumi, zai nemi ciwon hantar mai tsanani ya rasa. Wanda idan ka je asibiti shi ne ake cewa kana da HIB. Hantar Rakumi kaca-kaca take da wadannan cututtuka guda bakwai, da fatan za a jarraba.

Da ya koma kan batun fitsarin Rakumi, Daktan ya bayyana cewa, ‘Ana ta kace-nace, a kan shan fitsarin Rakumi, Kasar Saudiyya ta yi kokari da ta dauki manyan likitoci, da manyan Farfesoshi, da yawansu ya kai ashirin da biyar, suka binciko fitsarin Rakumi, babu abin da suka gani na cutarwa. Annabi (SAW) Ya shayar da fitsarin Rakumi, sannan kuma hae wani ya ce wai guba ne? Annabi shi ne Ya yi umarni da shan fitsarin Rakumi da Nonon Rakumi.

A cikin tunbin Rakumi akwai wasu tukwane wanda Allah Ya zuba su a ciki, wadanda kai ma kana da shigen su, amma ba irin na su ba. Da za ka busar da kashinsa ka nika idan mutum yana farfadiya, sai a kwaba  ana shafa masa, ya kuma rinka sha tare da nonon Rakumin,  idan yana faduwar sai ya samu sausauci a kan wannna faduwar. Idan Allah ya taimake ka ma ka neme ta ka rasa a sanadin kashin Rakumi. Farfadiya cuta ce mai wuyar warkewa, amma kashin Rakumi ragargaza ta ya ke yi. Tunbin Rakumi a tafasa shi, idan aka samu wanda ya sha guba, yana sha gubar ba za ta kara tasiri a jikinsa ba, kuma zamu iya busar da shi idan za mu ci abinci mu rika zubawa a ciki, idan akwai guba babu abin da za ta yi maka. Wata kuma fa’idar ga matsalar maza, wajen maganar rike fitsari, shan fitsarin Rakumi yana maganin wannan matsalar.

Sani Umar Abatuwa Gusau, shi ne mai kula da bangaren Rakumma wanda ya kwashe sama da shekaru Hamsin yana wannan aikin a cikin kwatar,  ya tabbatar mana da cewa, ‘Rakumma na da saukin sarrafawa wajen kula da su. Duk da su ma ana samun mahaukata a cikinsu, wadanda idan haukan ya tashi, sai ya kori kowa daga gidan nan. Kuma idan yana fada da Dan’uwansa Rakumi, suna iya kashe junansu. Amma ni tun da na ke, ban taba samun matsala da su ba, tsawon shekaru Hamsin da na ke aiki a cikin Rakumman, ni ke kula da su har zuwa wajen suka.

Aminu Na Manu, aikin sa shi ne soke Rakumi da fede shi, ya bayyana ma wakilinmu cewa, ‘Sama da shekaru Ashirin yana aikin Soke Rakumma da fidarsu a Abatuwa da cikin garin Gusau. Kyautatawar da Allah Ya ce a yi wa dabba wajen yanka da suka, ya sa muke durkusar da shi mu daure kafafuwansa, mu juyo  wuyansa saitin inda Jijiyoyin da ake yanke wa suke, sai mu sanya wukar mu soke shi, cikin mintuna biyu za ka ga ya mutu, ba kamar sauran dabbobi ba, da sai sun kwashe mintuna biyar zuwa bakwai suke mutuwa, amma shi kan, nan da nan yake mutuwa. Kuma a kullum mukan soke biyar zuwa goma, wannan shi ne aikin mu, ga shi nan muna yi da yara na. Kuma aikinsa ya fi kawo kudI, don idan za ka fede Saniya a kan Naira 3000, shi yana kaiwa Naira 6000, saboda wahalar aikinsa. Kuma ina mai tabbatar maka cewa, ‘ya fi Shanu nama, yawa da auki.

Sunday, da ke Abatuwan Gusau, shi ma aikin sa yin Abincin kaji da Jinin dabbobi, ya tabbatar mana da cewa, ‘Jinin Rakumi da shi suke sarrafawa zuwa abincin kaji, ya fi gina jiki, ko da kuwa sun hada shi da jinin Shanu da Tumakai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here