Soyayya Da Shakuwa: Shagwabar Masoya

403

Tare da Muhievert Abdullahi08083104306 (Tes kawai)

Assalmu alaikum Barkanku da kasancewa tare da ni cikin wannan shafi na SOYAYYA DA SHAKUWA kamar kowanne mako yauma dai ina tafe tare da wani tunasarwar.

A yau zan yi magana ne kan shagwabar masoya, da yawa wasu nasan zasu iya cewa “shagwaba kuma?” Eh! kwarai shagwaba, kamar yadda aka sani akwai shagwaba ta masoya bayan an yi aure, akwai kuma shagwabar masoya kafin aure wadda ba lallai sai bayan an tare za a yi wa masoyi ko masoyiya ba.

Ita dai shagwaba cikin soyayya na kara armashin soyayya. Tana kara dankon soyayya. Tana kara shakuwa ga masoya.  Da yawan wasu basu san ya za su yi shagwabar ba, wani ko wata garin yin shagwabar sai ta janyo abunda zai raba soyayyar ga masoyin ko ga masoyiyar, toh! Ta ware murya kamar wadda za ta rusa kuka, don me hakan ba zai kona masa zuciya ba. Idan kai din ne ma hakan take ka ware murya kana kokarin rusa mata kuka wai sunan shagwaba kake mata dole hakan ya kona mata zuciya don takaici.

Ita shagwaba na zuwa ne cikin salon hira irin ta masoya yayin da za a yi shagwabar ana kwantar da murya ta yadda in masoyin ko masoyiyar ta ji za ta rika tuno da salon shagwabar musamman a lokacin da ake kewar masoyin ko masoyiyar.

Iya shagwaba cikin soyayya wani sirri ne na daban wajen kara shakuwa da juna da kuma kasa rabuwa da juna, wani namijin na son shagwaba yayin da kuke hira kina hada masa da shagwaba zai rika jin baya son yayi nesa da hirarki, haka kuma idan har shi me son hakan ne bakya masa in ya hadu da me yi masa labari na iya canjawa sai mace ta rasa me ya sa saurayin ya gujeta alhalin suna zaman su lafiya babu wani bacin rai nan kuwa yana can ya koma wajen wadda ta fita iya salon soyayya ne. Kaima kuma hakan ne wani namijin ya iya shagwaba me kwantar da zuciya yayin da mace ta ci karo da shi sai ka ji zance ya sha bamban.

Hmm! Ban ce masoya su rika canja masoyansu ba yayin da daya ya rasa wani abu cikin soyayya, koya masa ya kamata a yi cikin salo na so da kauna.

Shagwaba bayan aure daban take haka kuma shagwabar masoya kafin aure ita ma daban take, dan haka ina magana ne akan shagwabar masoya kafin aure, ba laifi bane yin shagwaba cikin soyayya sai dai shagwabar ba irin wadda ta keta shari’a ba, shagwaba me tsafta dan karawa juna so da shakuwa.

Idan kuna tare da ni a hankali zanci gaba da kawo muku abubuwan suka shafi masoya, zan dan takaita bayanina sabida wajen yayi kadan na ci gaba da yi muku bayani, da fatan masoya za su rika gyara abubuwan da yake na gyara.

Ku kasance tare da ni a wani makon da yardar Allah don jin da me zan tawo muku.

Samfurin Kalaman Soyayya

Idan na ganka ina jin shauki cikin zuciyata, indai da so soyayyarka ba zata gushe gareni ba.

Kai dan baiwa ne domin na dade da sanin hakan.

Kai ne mallakina, sirrin zuciya, soyayyarka ba ta misaltuwa tare da ni kamar yadda ruwa baya kidayuwa.

Komai kankantarsa haka ma soyayyarka take gareni, ba za ta taba misaltuwa ba, kamar yadda ruwan sama ke zuba a lokacin zubarsa, haka soyayyarka take kara ruruwa a duk lokacin da idanuwana suka yi arba da kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here