Kaucin Kaba Sha Nema: Miji Nagari

361

Daga Malam Hamza Dawaki

Mafarkin kowace mace nitsattsiya  da kuma kowadanne iyaye akilai a rayuwa, ba ya wuce Miji nagari. Domin shi ne mafi dacen da ‘ya mace za ta yi a rayuwa. Kasancewar shi miji ba wai abokin zama ne kadai ba. Sau da dama yakan zama kamar malami mai tarbiyya ne ga mace.

Kodayake, abu ne da ba kasafai akan yi rubutu a kai ba. Amma ina ganin kamar yadda ake yawan yin rubutu game da mace tagari, haka nan ya dace a rika yi a kan miji nagari. Ko kuma ma fiye da hakan. Dalili a nan shi ne, macen da ta yi rashin katari ta auri mijin da ba nagari ba, ta fi shiga hadari a kan namijin da ya auri macen da ba tagari ba. Saboda shi idan ya ji wuya zai iya yakice ta, ya huta. Amma ita (musamman in ba wayayyiya ba ce sosai), ba ta da wata mafita illa dai ta ci gaba da irin zaman nan da suke cewa zaman hakuri. Tun da ita ba ta da damar saki, kamar yadda namiji ke da ita.

Akwai abubuwa da dama da ya kamata mu duba a tare da mutum don kokarin gano shin zai iya kasancewa miji nagari, ko kuwa dai miji gama-gari. Wadannan suffofi za mu iya dubansu ta mahangu da dama. Kamar mahangar addini da al’ada da kuma kimiyyar halayyar bil’adama da sauransu. Haka nan kuma za mu kalli yanayi ko suffar mazan da ake sa ran za su iya zama maza nagarin, kafin da kuma bayan aurensu.

Siffofin Miji Nagari Kafin Aure.

Da yake addini shi ne mafi girman mizani da za mu iya auna komai na rayuwa da shi, za mu fara kallon nasa ma’aunin.

Hakika mafi dacewa abu da ya kamata a duba ga namiji don tantance ko nagari ne, shi ne, rikon addini da kuma kyan dabi’arsa. Bisa la’akari da fadin Annabi SAW: “Idan wanda kuka yarda da addininsa da dabi’arsa ya zo muku (neman aure) to ku aure shi” ko “ko aurar masa”

Yana da kyau matuka. mata da iyaye su lura da maganar dabi’ar nan sosai. Domin sau da dama akan sami mutumin da ya suffantu da addini amma ba shi da  dabi’u masu kyau. Wannan kuma yana daya daga cikin mafiya wahalar da matan da ke karkashinsu!

Mutum mai kyakkyawar dabi’a duk inda yake za ka taras karbabbe ne a wurin al’umar da yake ciki. Kuma dabi’arsa karbabbiya ce. Ba lallai ne ya kasance mai abokai da yawa ba. Amma za ka taras tun abokansa na shekaru aru-aru har yanzu suna tare. Ba kuma wai don ba sa cutar da shi ko bata masa rai ba. Kawai saboda kasancewarsa mai yawan yi wa mutane uzuri.

Kuma za ka same shi mai kallon kyakkyawan ayyuka da daraja, mai kau da kai ga kusakurai da ayyukan tir din mutanen da ya tsinci kansa a ciki. Wannan dabi’a tana taimaka mar kwarai wurin tattalin zamantakewarsa. Domin duk lokacin da aka yi mar wani abu na zalumci ko rashin kirki, idanuwansa ba sa saurin rufewa. Suna iya ba shi damar tuno wasu ayyuka na kyautata da aka yi mar, sai ya gamsu cewa lallai wannan kuskure ne da ya kamata a yi wa mutum uzuri a cikin sa.

Mai kyakkyawar dabi’a zai iya kasancewa mai yawan hakuri da kau da kai da kuma yafiya.  Za ka taras shi ba mai rama mugunta da mugunta ba ne. Yana da kyau mu sani cewa rama mugunta da mugunta, ko rama mummuna da mummuna yana daya daga cikin manyan abubuwan da suke haddasa “mautul hub” wato macewar soyayya tsakanin ma’aurata. Domin yayin da mace ta yi zargin cewa mijinta ya daina yi mata wani abu da ya saba yi mata na kyautatawa, ita ma ta janye abin da take yi mar na kyautatawa, to wannan soyayyar a saurari ranar macewarta! Amma idan kuwa aka yi katari da miji nagari, sai akasin hakan ya faru. Domin shi ba ya rama mummuna da mummuna. Yayin da kuwa ki ka yi wa mutum wani abu mai muni, ya kau da kai, ko ma ya rama miki da mai kyau, to lokaci guda za ki tsinci kanki cikin wani yanayi na jin kunya da nadama. Don haka duk wani yunkuri na maimaita wannan abin sai ya rasa gurbi a ranki.

Miji Nagari A Al’adance.

A al’adance, tun asali Bahaushe yana da sigogi da yawa na auna hankali da tunani ko mu’amular wanda ko wadda zai aura. Daga ciki akwai wannan. Daya daga manyan matakan da ake bi wurin auna miji nagari shi ne, duba yadda yake mu’amulantar mahaifiyarsa. Wato idan aka tarar mutum yana da kyakkyawar mu’amula da mahaifiyarsa. Yakan zauna su yi hira ya ma taya ta wasu ayyuka da sauran abubuwa dake kyautata dangantaka, sai a ce, lallai wannan zai kyautatawa matarsa yayin kuruciyarta. Kuma in ta tsufa zai tausaya mata. Amma wanda aka ga ba ya  kyautata mu’amula ta mahaifiyarsa, ba ya yin wani abu na nuna mata tausayawa. Ba ya sauraro da girmama maganarta. To wannan sai a ce, ba zai tausaya wa matarsa yayin da ta tsufa ba. Kawai dai zai iya son ta da doki da zumudin ta ne a lokutan da take kan ganiyar kuruciyarta.

Domin shi so da sha’awar mace dole ne, kamar yadda son mazan ya zame wa matan. Saboda dabi’a ce da Ubangiji subhanahu wa ta’ala Ya gina kowa a kai. Don haka, kowa ma zai iya son mace. Amma girmama ta da ganin kima da tausaya mata kuma dabi’a ce da ba kowa ne ke da ita ba.

Miji Nagari A Kimiyyance

Masana suna ganin duk yaron da ya taso a hannun mace mai kokari ta fannin tarbiyya da kamanta gaskiya a cikin maganganunta da sa ido sosai wurin tabbatar da cewa ta dora shi a tafarki madaidaici. Wadda kuma take nuna masa so, da jan sa a jiki. Tare kuma da kiyaye duk wani abu da bai kamata ya ji ko ya gani daga wurinta ba. To wannan yaron zai iya kasancewa mutum mai ganin kima da darajar mata, kuma zai girmama su. Don haka zai iya kasancewa miji nagari.

Amma yayin da yaro ya taso a hannun ballagazar mace, wadda za ta iya sakin jiki ta shirga karyarta a gabansa. Ta yi zage-zage da sauran maganganu na wauta da sakin layi yana ji. Kuma ta rika aibata mahaifinsa ko nuna bai isa ba a kan idonsa. Kuma ba ta ja shi a jiki ta nuna mar so ba. To hakika wannan yaron zai iya samun matsala a tunaninsa. Ta inda zai kasance yana kallon mata a matsayin marasa daraja da kima kuma masu tsananin butulci da rashin kamun-kai. Don haka kuma wannan yaron mawuyacin abu ne ya iya zama miji nagari ga iyalinsa.

Miji Nagari, Bayan An Yi Aure.

Kadan daga suffofin miji nagari bayan aure su ne:

Ba ya zagi ko gori wa matarsa.

Ba ya dukan fuskarta.

Idan ya ci sai ya ciyar da ita. Haka in ya sha.

Idan ya yi tufa, sai ya yi mata.

Ba ya bayyana sirrinta ga kowa.

Ba ya wofuntar da shawara ko tunanin ta.

Yana ganin kimarta da kuma girmama manyanta.

Kuma yana kallonta a matsayin ‘ya mai cikakken ‘yanci ba baiwa ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here