Sirrin Iyayen Giji… Nau’ikan Fata Da Yadda Za Ki Kula Da Fatarki

190

Tare da  Umma Sulaiman Shu’aibu ‘Yan Awaki (Aunty Baby)

Anty Baby matar aure ce. Don haka mata zalla (banda maza) za ku iya tura ma ta da tambayoyi ta hanyar imel ko lamba wayar kamar haka:

[email protected]

08028586967

Assalamu Alaikum, ’yan uwana mata, barkanmu da wannan lokaci a cikin wannan shafi mai farin jinni. Saboda shigowar sanyi, na kawo mu ku wannan tsaraba ta musamman, domin yawancin mata mu na samun matsala da sanyi wajen gyaran jikinmu baran ma fatar jikinmu. To, duba da yawancinmu ba su san ma wacce irin fata ce da su ba shi ne ya sa na dauko abin daga tushe. Ku biyo ni.

Idan a ka ce gyaran jiki ko fata ya na da kyau a ce kowacce mace ta san yanayin jikinta, domin sanin shi zai sa ki yi amfani da mai ko sabulun da zai yi daidai da yanayin jikinki. Idan a ka sami akasin haka, sai mutum ya bata maimakon gyara…

Ita fata jiki ta kasu kashi biyar:

1) Gama-garin fata (Normal skin)

2) Fata mai rikida (Combination skin)

3) Busashshiyar fata (Dry skin)

4) Fata mai maiko (Oily skin)

5) Fata mai santsi ko gautsi (Sensitibe skin)

 

  • Gama-garin Fata:

–  Ba ta da maiko sosai, sannan ba a bushe ta ke ba.

–  Ba ta yawan rike tabo ko wani rami da kwari. Ba za ki ga ramin gashi ya na nunawa sosai ba.

–  Yanayinta ya kan zama kamar ba na fata mai rikida ba.

 

  • Fata Mai Kala biyu:

–   Shi wannan yanayin jiki ya kan canza daga lokaci zuwa lokaci ya yi maiko ko ya bushe, musamman a wajen hanci, goshi da haba.

–   Ramin gashi ya na nunawa.

–   Irin bakaken hudojin nan masu tutso da wani baki a fuska su kan fito; wani lokacin ma har jiki,

sannan yawancinsu fatarsu ta na sheki.

 

  • Busasshiyar Fata:

–   Ba a ganin ramin gashi sosai.

–   Launin fatar ya kan zama kyamas, musamman lokacin hunturu.

–   Fatar ta kan zama mai gautsi.

–   Idan mutum fari ne sosai sai ka ga duk ta tattare.

–   Fatar ba ta jawuwa sosai.

–   Jiki ya kan yi zafi da radadi wani lokaci, musamman idan ta bushe da yawa.

–   A wasu lokutan har a kan sami tsagewar fata, musamman a bayan hannu, fuska da kafa

Yawancin abubuwan da ke saka fata bushewa sun hada da girman shekaru, rashin iya kula da kai wajen sanin man da ya kamata a yi amfani da shi da kuma rashin tsaftace jiki yaddah ya kamata da canjin yanayi kamar lokacin iska, rana ko sanyi, idan ba a kula da kai. Yawan yin wanka ko amfani da ruwan zafi da dadewa a cikinsa ma ya na janyo bushewar fata, sannan yin amfani da sabulai masu karfi, ‘cleansers’ da man shafawa wadanda su ka yi wa fatar jiki karfi.

 

  • Fata Mai Maiko:

–   Wannan fata ita ce fatar da ta ke yawan fidda maiko, wasu fuskarsu ce kawai ke zama haka, wasun su kuma har jiki.

–   Fata na zama baka, mai kyallin maiko

–   Fatar ta kan yi kauri

–   Irin wannan fatar ta na kawo yawan yin kurajen fuska da yawan yin bakin tsuro mai kama da tusar jaki a fuska, sannan ta na saka gishirin hanci.

Yawancin abinda ke Janyo ko tsananta shi Maikon wannan fata ya hada da balaga, rashin hutu, dauwama a rana, zama guri mai zafi da rashin yin amfani da hankicin goge gumi lokacin zufa.

 

  • Fata Mai Santsi:

–   Masu irin wannan fatar su na yawan samun matsalolin fata.

–   Idan ki kasance ki na da irin wannan fatar, sai ki lura da abubuwan da jikinka ba ya so ki kiyaye mu’amala da su, don yawanci daga sabulai, mayuka ko dai wani abu a al’ummar da ki ke ya na janyowa

–   Mai irin wannan fata ta kan kasance mai yawan daukar kwayar cuta (infection), kaikayi, jin zafi, da bushewa.

–   Kuma su na saurin jin ciwo. Don haka masu irin fatar nan sai su dinga kula da kansu sosai.

Idan kin gane kalar yanayin fatar jikinka, sai ki san irin mai da sabulun da zai gyara mi ki jiki, sannan ki lura da kayan hadin jikinsu, don gudun matsala.

Akwai launikan mayuka na asali ko na ce wadanda a ka hada su a gargajiyance, sai ki nemi, wadanda sun yi daidai da naki. Kada ki bi yayi ko tsadar mai ko sabulu.

Bari na baku wannan misalan mayukan, amman ku yi hakuri, domin yawancinsu idan za a siya sunayensu a hakan ya ke. Yawancin mai ko sabulu irin wadannan oil su na gyara kusan kowace irin fata:

 

  • Na Kowacce Fata:

–  Grapeseed oil

–  Rice bran oil

–  Olibe

–  Jojoba

–  Peanut

 

  • Na Bushewar Fata:

–   Castor

–   Cocoa butter

–  Grape seed

–  Olibe

–   Rice bran

–   Wheat germ oil

–   Lanolin

 

  • Na Gama-garin Fata

–   Corn

–   Grape seed

–   Sesame

–   Rice bran

–   Sunflower

–   Safflower

 

  • Na Fata Mai Maiko:

–   Olibe

–   Sweet almond oil

–   Abocado oil

–   Coconut oil

–   Apricot and peanut

 

  • Amfaninsu A Jikin Fata

–   Abocado: Ya na da maikon gyara jiki sosai da hana jiki yakushewa.

–   Almond: Wannan ya na da ‘protein’. Saboda haka ya na sa maiko a jiki kuma ya kan taimakawa jiki mai yawan bushewa.

–   Apricot Kernel: Idan za ki sayi man baki (lip balm) ki tabbbata akwai ‘apricot’ a ciki.

–   Cocoa Butter: Ya na kare jiki daga cututtuka kuma ya na taimakawa jiki mai bushewa.

–   Grapeseed Oil: Wannan na masu fata mai maiko ne.

Lanolin: An samar da shi ne daga man tumaki kuma a na samun shi a guraren sayar da magani. Ya na gyara wa masu busasshiyar fata jikinsu

– Peanut: Saboda yawanci ba ya bushewa a jiki, sannan ya na amfani a kowace fata, don haka ya na kare fata daga matsaloli/cutattuka, musamman masu ‘sensitibe skin’

Man Zaitun: Kun san ya na maganin kowacce irin cuta banda mutuwa, to ya na gyara kowace irin fata ta daina tattarewa da yamutsewa, ya na kashe cututtukan cikin fata, ya na saka taushi da santsin fata komai taurinta, sannan ya na gyara fatar jarirai ya yi mu su magani.

Man kadanya yawanci a na hada mayukan fata na kanti da shi saboda kyawunsa, ya na da matukar amfani da inganta fata, yana maganin yamushewar fata ya na maganin tattarewa da da komadewar fata.

A fitowar mu ta gaba za mu zo da babbar tsaraba ta abubuwan da mace za ta sha ko ta ci, ko’ina a jikinta ya ciko ta mirje ta yi kyau; uwa uba ni’ima ta wadace ta ta yi kaura daga mowar tsakar gida zuwa mowar daki.

 

Domin turo tambayoyi a kan wani abu da ya sha muku gaba ta bangaren rayuwarku ko neman karin haske game da wani abu na neman shawara game da zamantakewarku da mazajenku, za mu iya buga tambayarku a nan kuma mu ba ku ansa a shafin nan, domin karuwar sauran dan uwa mata ba tare da mun buga lambarku ko imel dinku ba, idan ba ku bukata.

Sai ku aikowa Anty Baby ta: [email protected]com ko 08028586967.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here