Annobar Zazzabi A Tiyin Ta Dau Sabon Salo

67
  • Babu Wani Abu Makamancin Haka A Tiyin, Inji Pharm. Gamawa
  • Al’ummar Garin Sun Yi Zanga-zanga, Sun Ce ’Ya’yansu Na Mutuwa

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Biyo bayan rahotonnin da jaridu da kuma gidajen rediyo suka bayar ciki har da na kasashen waje kan cewar a kauyen Tiyin da ke karamar hukumar Warji al’umman kauyen suna fama da wata mummunar zazzabi da kuma tari wanda ya ta kashe musu yara sama da 50 a Tiyin, Shitako kuma sama da yara 30 a cikin kasa da kwanaki 30.

Wannan jaridar ita ma ta dauko rahoton, har ma tabi sahun wasu ‘yan jaridu domin yin tattaki zuwa cikin kauyen domin ganowa da ido kan halin da suke ciki, har muka sake kawo muku rahoton a kari na biyu, da cewa shugaban hukumar lafiya daga matakin farko Pharmacy Adamu Ibrahim Gamawa ya kafa kwamitin da zai je kauyen domin yin nasu binciken don kawo musu rahoton abun da ke akwai. Duk da, Ibrahim Gamawa ya ce babu wata annobar da ta konno kai a kauyen amma dai ba su ce babu mace-mace ba.

A ranar juma’a 1 ga watan 12, 2017 ne shugaban hukumar lafiyar daga matakin farko a jihar Bauchi Adamu Ibrahim Gamawa ya kira taron manema labaru inda ya shaida musu cewar kwamitinsa da ya kafa don su je kauyen nan ba su kuma samu kunnowar kai na wata annoba a wannan kauyen ba. wakilinmu yana wajen hirar ya kuma nakalto mana cewar Gamawa ya ke cewa “yau mun kiraku ne kan cewar akwai wasu labarai da suke ta yaduwa ciki har da kafafen sadarwa na kasashen waje wanda suka dauki labari a kauyen Tiyin da ke karamar hukumar Warji wanda rahoton ke cewa akwai wata annobar da ta taso wacce ba a san kanta ba ake ta rasa yara a dalilinta”.

Ya ci gaba da cewa “saboda wannan abun ya dame mu, muka shiga bincike, mun tura kwamiti domin binciko mana. abun da muka samu babu wani abu kamar haka a Tiyin. Sai dai, akwai kes-kes kamar na maleriya wanda a kowani waje ma a samunsa a kodayaushe”. In ji sa

Gamawa ya kuma ci gaba da jawabinsa “Abun da muka samu a Tiyin, an samu yara, domin abun da muka yi shi ne mun je cikin al’umma muka ce duk yaron da bai da lafiya a kawo mana shi, kuma an fito da su abun da muka samu shi ne maleriya ne ke akwai. Sannan mun samu wasu yaran da suke tari, tarin kuma tari ne na yau da kullum, sannan an basu magani, babu wani abun da zai kawo tashin hankali a ciki”. ta bakinsa

Gamawa ya ce mutane biyu ne kawai suka samu sun rasu a bincikensu “mun je asibitin Gwaram asibitin da suka ce suna kai yaransu, mun samu an kawo yara 9 ne daga Warji, 3 daga Tiyin biyu ne a cikinsu suka mutu, abun da ya yi sanadiyyar rasuwarsu maleriya ne amma babu wani ciwon da ba a san kanshi ba”. in ji sa

Sai dai kuma, Ibrahim Gamawa ya ce wai Sarkin garin na Tiyin ya tara yara don su jifi dukkanin wanda zai shigo cikin kauyen domin yin bincike “a jiya mun samu rahoton da ke cewa shi wannan shugaban wannan al’umman ya samu yara ‘yan daba ya basu izini cewar duk wanda ya shigo cikin al’allumsa su jefesa”. In ji Gamawa

Tambayar wakilinmu a wajen ganawar. Yallabai, al’umman kauyen da daman, da kuma iyayen da suka rasa ‘ya’yansu a cikin wannan kankanin lokacin, shin dukkaninsu karya suka fada ke nan? Sai shugaban hukumar lafiyar ya amsa da cewa “ba mu ce ba a mutu ba; bamu ce yaro bai mutu ba, amma annoba ce ta kashe yara ko kuma mene ne, idan annoba ne ba ka dauki mataki ba zai ci gaba da yaduwa ne, babu annoba a garin”. In ji sa

Ke nan kana nufin Sarkin garin ya hada baki da jama’arsa su fadi haka? Sai ya amsa da cewa “wannan ai sai ka je ka tambayeshi”. Ta bakin shi Gamawan fa.

Jin hakan ke da wuya, bayan kammala ganawarsa da manema labaru, washe gari ranar Asabar 2/12/2017 tawagar ‘yan jarida suka sake komawa wannan kauyen domin sake binciko nasu binciken na ‘yan jarida, wakilinmu ya kasance a cikin tawagar domin tsago gaskiyar abun da ke akwai a tsakanin shugaban hukumar lafiya na jihar Bauchi da kuma su iyayen da suka rasa ‘ya’yansu, sarkin garin, limamai da kuma masu unguwanni.

Isar tawagar manema labarun ne dai, a karin farko babu wani wanda ya jefi ko mutum daya a cikinku ba kamar yadda shi Ibrahim Gamawa ya shaida wa ‘yan jaridan ba. inda muka riske su suna kan jerin gwano suna yin tir da kalaman shugaban hukumar lafiya daga matakin farkon ya fadi kan cewar ‘ya’yansu ba su mutuwa, kuma sun yi tir da dukkanin lamansa da rashin tauyasa musu da ya yi. A yayin da suke tsaka da zanga-zangar lumana ne kuma manema labaru suka samu jin ta bakunan wasu daga cikin, ga abun da kadan daga cikinsu su ke cewa “Sunana Abdullahi Alhaji Rinkicikin daga cikin unguwar Kankare a Tiyin. Mun fito wannan zanga-zangar lumanar ne domin mu nuna bacin ranmu a bisa kalaman da shugaban hukumar lafiya daga matakin farko ya yi a kan halin da muke ciki. dukkanin mutumin da ya ce yaranmu basu mutu ba, na farko muna kiransa da ya zo mu tabbatar masa, na biyu kuma muna cewa karya ne, na uku kuma muna kai kararsa wajen Allah da cewar Allah ya isa, kuma ya zalumce mu ko a hakan. Idan muka je lahira sai Allah ya yi mana hisabi da su. Wallahi mutuwa an yi, kuma yaranmu mun rasa su, kuma muna shelanta wa duniya duk mai son gaskiya ya zo don Allah ya gane wa idonsa”. In ji sa

Abdullahi Alhaji ya daura da cewa “Yau sati uku ke nan muna fama da wata cutar da mu bamu santa ba, mun gagara sanin kanta, asibibitin garinmu da magani ne babu magani amma mu bamu sani ba, don sun gagara yi mana komai a kai, hakan ya sa muke diban ‘ya’yanmu mu kaisu wasu asibitocin don samar musu da magani”. In ji sa

Da yake bayanin adadin yaran da suka mutu a kasa wata dayan kuwa ya ce “a wannan unguwar kawai tsakiyar garin Tiyin yaranmu 22 suka mutu a hanumu kuma muka sallacesu, yankunan da suke jikin garin Tiyin in haka hada adadinsu za su haura yara 50 da muka rasa, a Shitake yara 30, unguwar Biza suna da yara biyar da suka rasu, unguwar Allah ya yi yara 5, unguwar duba gari 3, bujala 10, kashafa 3, Aru suma suna da yara da dama da suka yara ransu.   Dukkanin mutumin da ya ce karya ne, muna kiransa da ya zo ya nuna mana wajen da ba a yi mutuwar ba, da iyayensu da hujjoji ga kuma marasa lafiya jangwa mana tare da su ”. in ji sa

Abdullahi ya yi kira ga gwamnan jihar Bauchi da cewar don Allah ya turo da kwamiti da kansa domin binciken halin da suke ciki, da kuma kawo musu daukin gaggawa, a cewarsa matukar ba a yi hakan ba suna fuskantar ‘ya’yansu za su yi ta mutuwa kila ma su kai ga karewa domin ci gaba da mutuwar suke yi, hukumar lafiyan kuma bata da niyyar daukan mataki, bihasalima ba su yi abun da dace don shawo kan matsalar ba.

Shi kuma Muhmmadu Hambali Shagon Kangare wanda ya yi magana a madadin matasan kauyen Tiyin cewa yake “wannan mace-macen da ake yi gaskiya ne, wanda wannan rashin da ake yin ya damemu wallahi, iyayenmu, ‘ya’yanmu, abokanmu babu wanda wannan matsalar ba ta shafa ba; babu kuma wanda wannan matsalar bata dama ba, amma abun takaici wani a can yana kwance da ‘ya’yansa lafiya, mu kuma ya ce wai ‘ya’yanmu basu mutu na, muna kira ga mutanen gwamnati da su zo su duba don fitar da mu daga cikin halin da muke ciki”. in ji sa

Ya kuma kara da cewa “yanzu haka yarana biyu suna kwance babu lafiya, amma kuma an ce wai babu ma matsalar, wannan na nufin ba a ma da shirin kawo mana dauki don ceto rayukan ‘ya’yanmu, idan an maishemu saniyar ware ne to a sanar mana domin mu gane cewar mu bamu da ‘yanci, amma dai muna yin zabe ai ko”. Ta bakinsa.

Shi kuma Sani Gambo cewa ya yi sun fara shin kishin-kishin wai za a cire musu hakimin garin don ya fadi gaskiyar halin da jama’ansa suke ciki, sai ya ce kafin a kai ga hakan ya kamata a duba da kyau “muna bayan Sarkinmu, bamu taba sonsa kamar yadda muke sonsa a yanzu ba, domin kuwa ya bayyana halin da muke ciki wa karamar hukuma ba sau daya ba, ba sau biyu ba, ya zo ya dauki mataki sanar da duniya halin da muke ciki, duk wanda ya shiga gidan rediyo ya karyata shi wallahi bai neman rahama a wajen Allah, mu da muke cikin halin damuwa an zo an ce mana wai yaranmu suna mutuwa a ce karya ne, mu duk halin da ake ciki za mu fadi gaskiya, ko ni ‘ya’yan yayana biyu sun mutu, ‘ya’yana biyu yanzu haka basu da lafiya”. In ji sa

Lokacin da jami’an lafiyar suka zo ba ku shaida musu halin da kuke ciki bane? Sai ya amsa da cewa “sun zo mun sanar musu, har makabarta sai da muka kaisu, akwai wani jami’in lafiya a karamar hukuma mai suna Habila har hotuna ya dauka, amma tsabaragen rashin tsohon Allah da yake ba tsoron Allah suke ji ba, ba kuma ‘ya’yansu ne ke mutuwa ba, sai suka zo suka munafurci mutune suka ce suna cewa wai mutane biyu ne suka mutu. Wallahi tallahi muna kira ga gwamnan jihar Bauchi Muhammadu Abdullahi Abubakar mun sani da adalci ya ce zai yi aiki mun amince ya sanya kwamiti su zo su duba idan bamu cikin halin da muka shaida duk hukuncin da ya dace a dauka a kanmu, bamu da inda za mu yi mu bayyana kukanmu da halin da muke ciki sai ta wajen ku ‘yan jarida ku taimaka mana ku bayyana wa duniya muna cikin halin ni-yasu wadanda ya kamata su kare lafiyarmu sun je suna cewa babu wannan matsalar, dauka yanzu damar da muke da ita muna jiran mu ga wani mataki ne gwamna zai dauka, zai turo wakilai su bincika ne ko yaya”. In ji sa

Daga bisani kuma ya yi kira ga gwamnan da ya dauki mataki a kan shi shugaban hukumar lafiya daga matakin farko domin zai jawo wa gwamnan jihar bakin jini “gwamna ya tashi tsaye ya sanya ido, ya turo masu dubawa daga garesa in ba haka muna ganin alamar ‘yanmu dukka za su kare. Don Allah gwamna ya taimakemu ya taimaki jama’anmu da yaranmu”. In ji sa

Shi kuma, wani dattijo cewa ya yi “makabarta a kowace unguwa mun bisne yara, muna son duk mai son neman gaskiya za mu iya kai mutum, mu kuma nuna masa, inda muka bisne yaran, kuma muna da jerin ‘ya’yanmu da suka mutu, don haka muke neman tallafi, iyayen yaran nan suna nan, komai ake so na tabbatarwa a zo ko kuma a kiramu mu za mu je domin mu bayyana gaskiyarmu”. In ji wani tsoho a garin.

Shi kuma Sarkin Fawan Tiyin mai suna Adamu cewa ya yi “ni ma a cikin rashe-rashen da ake yin nan ta shafe ni, duk kokarin da na yi wajen kai yarinya ta asibiti amma ta rasu, yau kwanaki 12 da suka gabata na rasa daya daga cikin yarinya na a sakamakon wannan zazzabin da ya addabemu”. In ji Sarkin Fawan.

Ita kuma wata uwa da muka zanta da ita mai suna Harira Munkaila Tiyin ta shaida tsananin da suke ciki inda ta nemi daukin daga gwamnatin jihar “bayan ‘ya’yan kanne da na yayuna sun mutu a sanadiyyar wannan cutar, akwai jikanni na biyu sun rasu. Zahiri wannan matsalar ta addabenmu, domin muna cikin wani yanayi, ba a daukan kwanaki sai jarirai sun rasu a wannan kauyen. Hatta shekaran jiya wani jinjirin yaro ya rasu, wallahi ni din nan ni ce na amshi haihuwarsa a nan masallacin aka yi masa jana’iza (ta sa kuka) dukkaninsu tari ne suke damunsu. Yanzu haka ga wannan yarin da take baya na tana da wannan cuta ga shi ku ji tarin da take yi (ta nuna mana, jaririyar yarin tana ta yin tarin) a shekaran jiya aka yi mata karin jini”. In ji ta

Ta nuna mana yadda yarinyar ke tari, sosai, mun kuma shaida, yarin duk ta galabaita.

Bayan kammala ganawarmu da jama’an wannan kauyen mun yanki jiki muka sake ziyararta makabartar Kankare da ke tiyin inda muka sake samun yara biyar kari a kan wadanda muka taba zuwa a ranar juma’ar makon jiya da muka gani.

Bincikenmu ya iya gano mana cewar su ma’aikatan lafiya suna dogaro da abun da ke faruwa ne kawai idan sun ga rahoto a cikin asibitinsu, wato idan sun duba janibin shigar da sunaye suka tarar an sanya sunan mutum da jan bairo hakan ke nuna ya mutu, wato suna nufin duk wanda bai mutu a asibiti ba, basu da masaniya. Ko su jama’an garin sun bayyana cewar suna kai yaransu ne asibitoci daban-daban ciki kuwa har da masu zaman kansu domin nema ya yaransu lafiya. Sannan, shugaban lafiyar ya ce sun je asibitin Gwaram ne kadai, su kuma mutanen gauyen sun bayyana asibitocinsu da suke kai ‘ya’yansu ciki har da asibitocin kudi masu zaman kansu kamar yadda muka labarto a kwanaki.

Dangane da batun nan da ‘yan jarida suka yi na cewar sun je asibitin kankare da ke Tiyin a ranar juma’ar wancan makon ba su gamu da ma’aikacin lafiya ko daya ba, tattare da a lokacin jama’an kauyen na neman agajin gaggawa, shugaban hukumar lafiya daga matakin farko Adamu Gamawa ya bayyana cewar kwamitin da suka turo don yin bincike bai kawo musu rahoton hakan ba “mu bamu samu wani ma’aikacinmu da bai zuwa aiki ba’. in ji sa

Ya zuwa yanzu dai jama’an garin sun bayyana cewar matsalar da suke ciki dai tana nan tana kuma damunsu, don haka suke matukar neman agajin gaggawa daga gwamnatin jihar da kuma hukumomin da abun ya shafa domin a ceto musu rayukan ‘ya’yansu da kuma nasu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here