Lalacewar Tarbiyar Yara: Iyayen Yara Sun Gudanar Da Taro A Yola

16

Daga Muhammad Shafi’u Saleh, Yola

Kungiyar iyayen yara P.T.A da hukumar makarantar sakandiren jeka ka dawo ta gwamnatin jihar Adamawa, Double Secondary School, da ke karamar hukumar Yola ta arewa sun gudanar da taron lalubo hanyoyin magance matsalolin da suka yiwa makarantar tarnaki.

Taron wanda ya samu halartan bangarorin iyaye da malamai da hukumar gudanarwar makarantar, babban jami’in ‘yan sanda da ke kula da karamar hukumar DSP Ola Ajisebatu, ya halarta da sauran masu ruwa da tsaki a yankin.

Tun da farko da take jawabin maraba da baki shugabar makarantar Hajiya Hauwa Bello, ta zayyana matsalar tsaro, rashin tarbiya, rashin da’ar yaran da kuma matsalar shi kansa karatun yaran a makarantar, da cewa sune abinda ke damunsu.

Tace wani abin mamaki wasu yara ‘yan marantan sun koma sace-sacen kayayyaki dama kofofi da tagogin makarantar, tace hatta dakin shan maganin makarantar bai tsira daga sace-sacen yara ‘yan makarantar ba.

“Yara sun matsa mana da sace-sace komai na makaranta sacewa sukayi hatta dakin shan maganin da muke amfani dashi, bai tsira daga sace-sacen yarannan ba, da yi mana barazanar kisa.

“Mun dauko hayan jami’an tsaron ‘yan sanda da Cibil Defense, Peace Corps amma sai yaran suna haurawa ta saman takangar makaranta su tsere, indan kuma police sun kame yaran iyaye su ce bamu kyauta ba, shi yasa muka shirya taron domin sanin abinyi” Inji Hauwa.

Shugabar makarantar ta kuma koka da halayyar wasu yara a makarantar da cewa batagari ne kawai amma ba karatu ke kawosu ba, tace “idan mun ajiye domin su gano masu wannan aikin sai su kama yaro da karfi su bugar dashi da kayan maye, su aikata abinda sukeso su gudu.

“Mu ma malamai bamu tsira ba, idan mun dauki mataki akan yaro, sai su taremu a kofar fita makaranta, suna barazanar zasu kashemu, gara mu dauki mataki saboda yaron da ya kashe malaminshi ba zai bar ubanshi ba”.

Tace kamata yayi iyaye su rika ziyaratar makaranta suna gani da sanin halin da yaransu suke ciki, tace hakan zai taimaka wajan rage aikata miyagun ayyukan da yaran ke yi, “mu hadu mu warware wannan matsalar, muyi kokarin gyarawa” inji Hauwa.

Shima a jawabinsa shugaban kungiyar iyayen yara (PTA) na makarantar Alhaji Hussaini Gambo, ya koka da irin lalacewar da tarbiyan yara ya’yi a makarantar, yace ya zama musu wajibi su dauki mataki domin gyara tarbiyar da makarantar baki daya.

Yace “biyayya ga tsare tsaren da makaranta za ta fitar domin kyautata karatu da magance matsalar kangararron yara a makaranta dole ne, duk uban da ba zaiyi biyayya ba, a kori yaronshi yaje ya karantar dashi.

Hussaini Gambo ya kuma roke gwamnatin jihar Adamawa da ta yiwa Allah ta biyawa iyayen yara kudin kudin rubuta jarabawar WEAC da NECO, yace yara da dama basa samun daman rubuta jarabawar sakamakon kasa biyan kudin.

“ mafi yawa iyayen yarannan talakawa ne, muna rokon mai girma gwamna Bindow da ya yiwa Allah ya taimaka ya biyawa yaranmu kudaden zana jarabawar WEAC da NECO, domin yaranmu suma su samu su rubuta jarabawar” inji Hussaini.

Shima a jawabinsa babban jami’in dan sanda DPO da ke kula da karamar hukuma DSP Ola Ajisebatu, ya bada shawarwari da dama dama hanyoyin da hukumar makarantar ya kamata ta bi domin shawokan matsalar rashin tarbiyan yara.

Yace makarantu da dama na fuskantar irin wadannan matsalolin a yankin, yace duk wani mataki da rundunar zata dauka ya ta’allaka da matakan da hukumar makarantar ta dauka akan lamarin, yace akwai hanyoyin da sukebi amma rundunar bata da wani tanadin akan yara ‘yan makaranta.

“duk abun da zamuyi ya dogara ga irin matakin da hukumar makaranta ta dauka ne, amma daga yanzu ba zamu yarda yara su shiga makarant da ashana da wiwi ko kwkyoyi, kuma ba zamu bar yaron da ke yiwa malamai barazana ba” inji DPO.

Jami’in dan sandan ya nuna damuwa game da yadda wasu iyayen ke watsi da yayansu haka, yace “bai kamata mu iyaye mu rika watsi da ya’yanmu ba, mu rika sa’ido game da zargazirgan yaranmu, zai taimaka wajan rage yawan yawan matsalolin da muke ciki.

“mu rinka karfafa yaran mu nuna musu suma zasu iya zama wani abu anan gaba, mu rika ziyartar makarantun ya’yanmu mu san halin da suke ciki, ni yara suna karatu a Lagos amma ina da lambar malaminsu ina magana dashi ko yaushe” inji DPO Ola.

Suma dai iyayen yaran sun bayyana abubuwan da suke ganin ya kamata hukumar makarantar ta yi domin shawokan matsaloli dama rashin da’ar yara a makarantar.

Taron dai ya amince da cimma matsaya uku, a matsayin dokar da makarantar zata bi tace shigo da Kwaya makaranta da rashin da’a, da barazana ga malami, “idan yaro ya’yi laifi zamubi dindigi idan mun tabbatar da laifin koransa zamuyi kuma mu hadashi da jami’an tsaro, ko dan waye kuwa” inji sakamakon taron.

Mamba da ke wakiltar kananan hukumomin Yola ta kudu Yola ta arewa da Girei a majalisar wakilai ta kasa Lawan Garba, ya tallafawa makarantar da kwamfitoci 40, domin koyawa yara na’ora mai kwakwalwa a makarantar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here