Babu Batun Karin Kudin Man Fetur –NNPC

190

Daga Sulaiman Bala Idris

Kamfanin NNPC ya kara fito wa fili wurin bayyana matsayarsa na rashin shirin yin karin kudin man fetur a yayin bukukuwan sabuwar shekarar da ke karato wa.

A jiya ne Kamfanin na NNPC ya fid da sanarwar da ke cewa kudin litar man fetur ta na nan kuma za ta ci gaba da kasancewa akan kudin sari daga depo lita guda akan Naira 133.38, sannan a kasuwanni kuma Naira 142 ko 145 duk lita guda. Babu wani abu da zai sa wannan farashi ya canza, saboda a cewar Kamfanin na NNPC, tuni sun tanadi wadataccen man fetur din da zai ishi ‘yan kasa a lokutan wannan bukukuwa na karshen shekara.

Sannan kuma Kamfanin na NNPC ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da masu ababen hawa da su yi watsi da duk wata jita-jita da ke yawa a kafafen sadarwa na jabu, wanda ke cewa za a yi karin farashin man fetur. Kamfanin ya ce, wannan aiki ne na wasu baragurbi kuma zance ne da ba shi da madafa balle tushe.

Kamfanin ya roki al’umma da su guji halayyar siyan man fetur suna boye wa a gidajensu, saboda hadarin da ke tattare da aikata hakan na da yawan gaske.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here