Dole A Biya Ni Diyyar Dala Miliyan 800 –Kanu

630

Daga Umar A Hunkuyi

Shugaban sokakkiyar kungiyar nan mai rajin kare ‘yan asalin Biyafara, Nnamdi Kanu, ya ce, duk da cewa yana kan beli ne da Kotun daukaka kara ta Tarayya da ke Abuja, ta ba shi, inda ake tuhumarsa tare da wasu da laifin cin amanar Kasa, wannan bai hana masa a biya shi diyyar Dalar Amurka Milyan 800 ba, saboda kamu da kuma tsare shin da aka yi a shekarar 2015.

Kanu ya fadi hakan ne, a martanin da ya mayarwa kudurin da Gwamnatin Tarayya ta mayar, a inda take neman da Kotun Kasa-da-kasa ta Yammacin Afrika, da ke zamanta a Abuja ta yi watsi da wannan karar ta neman diyyar keta hakkin [an Adam da Kanu din ya shigar.

A watan Maris ne na shekarar 2016, Kanu ya shigar da kara, a inda yake neman diyyar Dalar Amurka milyan 800, daga Gwamnatin Tarayya, saboda kamu da kuma tsare shin da ya ce anyi ba bisa ka’ida ba a shekarar 2015.

Sai dai kuma Gwamnatin Tarayya ta shigar da kudurinta a ranar 13 ga watan Nuwamba, ta hannun Lauyarta, Uwargida Maimuna Shiru, tana neman Kotun kasa-da-kasa din da ta yi watsi da shari’ar, a bisa abin da ta kira da cewa, a yanzun shari’ar ba ta da wata ma’ana, kasantuwar Kanu din ya tsere daga belin da babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta ba shi a ranar 25 ga watan Afrilu na shekarar 2017.

Da yake mayar da martani kan bukatar Gwamnatin Tarayyar, ta bakin Lauyansa, . Ifeanyi Ejiofor, Kanu ya nemi Kotun da ta yi watsi da wannan bukata ta Gwamnatin Tarayya, yana mai cewa, ai belin da waccan Kotun ta ba shi, wani bangare ne kawai na abin da ya nema daga Kotun.

Ya ce kuma yana nan akan bukatarsa ta neman Kotun ta kasa-da kasa da ta tilastawa Gwamnatin Tarayya da ta biya shi wannan diyya ta Dala Milyan 800 da ya nema, saboda keta hurumin ‘yancinsa.

Lauyan na shi ya bayyana wa Kotun a rubuce, “Mun yarda da cewa, wannan Kotun tana da karfin da za ta tilasta a biya mu diyya saboda barnar da aka yi mana.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here