Gazawar Gwamnati Ne Silar Zub Da Jini A Nijeriya –Sarkin Musulmi

529

Daga Sulaiman Bala Idris

Sarkin Musulmi, Mai Girma Alhaji Abubakar Sa’ad III, ya alakanta yawaitar zub da jinin da ake samu a Nijeriya, musamman ma a yankin Arewa maso gabas da sakaci daga bangaren gwamnatin Nijeriya, ta fuskancin gaza daukar matakan da suka dace a lokacin da ya dace.

Sarkin Musulmin, wanda shi ne ya zamto Shugaban taron Majalisar Sarakunan Jihohin Arewa 19, taron da ya samu wakilci daga shugabanin sarakunan gargajiya daga Kudu maso kudu, da Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabashin Nijeriya. Wanda kuma ya gudana jiya a garin Kaduna.

A ta bakin Sarkin Musulmin, ya ce taron nasu zai yi nazarin wasu lamurra da suke damun al’umma, ciki har da yanayin tafiyar da gwamnati, da adalci ga dukkan ‘yan kasa.

Sultan din ya ce; “A matsayina na shugaban Fulani, ni ne shugabansu a wannan kasar, a ma gaba daya yankin Afirka ta Yamma, na rayu da mutane da dama, kuma na san matsalolinsu, don haka babu yadda za a yi na tunzura Fulani kan su dau makamai don su kashe mutane.

“Na sha fadin cewa, mutanen da suke daukar makamai suna aiwatar da kashe-kashe ‘yan ta’adda ne, mabarnata ne, ko da kuwa sun kasance Ibo, Hausawa, Yarbawa. Babu wani da ked a lasisin daukar makami.”in ji Sultan

Ya kara da cewa; “Idan aka ga irin wannan yawaitar kashe-kashe na afkuwa, akwai gazawa daga bangaren gwamnati, domin matukar gwamnati ta zage damtse ta tashi tsaye wurin yin abin da ya dace, makamancin wadannan abubuwan ba zai taba afkuwa ba.

“Kamar yadda muka saba, a taruka makamantan wannan, za mu tattauna wasu muhimman batutuwa da ke damun al’umma a kasar nan, wanda kuma za mu cimma matsaya tare da fitar da shawarwarin da za mu aika zuwa ga gwamnati da masu ruwa da tsakin da abin ya shafa, domin ganin ko za su aiwatar da shawarwarin namu.

“Ba mu da iko ko karfin aiwatar da doka ko zartaswa, saboda mu iyayen al’umma ne kawai, kamar dai yadda malaman addini suke, sai dai mu bayar da shawarwari a wuraren da suka dace, saboda shugabanci ba abu ne da za a sakarwa mutum guda ko wasu gungun mutane ba, abu ne da ke bukatar a hada karfi da karfe. Dole ne kuma mutane su saurarawa wadanda ke shugabanci don a iya fahimtar juna.” In ji Sarkin Musulmin.

Duk dai a jawaban nasa, Sarkin Musulmin ya bukaci wakilan al’ummar kudu da su bayyanawa majalisar sarakunan irin abubuwan da mutanensu ke ganin ana yi musu ba daidai ba a Arewa, domin a samu fahimtar juna. A cewarsa, “Dukkanku nan wakilan al’ummarku ne, wadanda ke rayuwa a tare da mu a arewa da wadanda ke rayuwa a kudu.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here