Jonathan Ya Ki Rike Girmansa –Oyegun

277

Daga Bello Hamza

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Cif John Oyegun, ya kalubalanci tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan bisa ikirarin da yake na cewa, ba wani ci gaba da aka samu a kasar nan, tun bayan da ya bar mulki na tsawon shekara biyu da suka wuce. Oyegun ya ce, irin wadannan maganganun da tsohon shugaban kasar ke yi za su jawo masa zabar da mtuncin kansa da na matsayin da ya rike.

Haka kuma,Cif John Odigie-Oyegun, ya nuna matukar mamakinsa bisa yadda tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya fita daga jam’iyyar APC ya koma jam’iyyar PDP, domin bayyana aniyarsa ta takararshugaban kasa a shekara ta 2019, saboda haka yace wannan alama ce ta lalace wa domin kuwa a karshe ba zai samu nasara ba.

Oyegun din ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zanta wa ta musamman da ‘yan jarida kan al’amuran da suka shafi kasa a Abuja.

Shi kuwa tsohon shugaban kasa Jonathan ya mayar da martini ne kan jawabin da Gwamna Kassim Shettima ya yi a wajen bikin kaddamar da wani littafi a Abuja, inda yace gwamnatin Jonathan ba ta yi wani abin a zo a gani ba, kuma duk da haka yake kururuwar cewa, wai wannan gwamnatin ba ta kama kafar gwamnatinsa ba. A martaninsa Oyegun, ya nuna rashin dadinsa a kan yadda Tsohon shugaban kasar ya kasa rike girmansa ta inda yake gaggawar mayar da martani a kan kowanne magana komai kankantar ta.

Tsananin lalacewar hanyoyin Gabas maso Yamma da lalacewar filin jirgin saman Fatakwal da rikicin Boko Haram manyan alamu ne na rashin nasarar mulkin Jonathan.

Ya kara da cewa, Jonathan ya amfana da tsarin karba-karba na shiyya wajen zama shugaban kasa amma bai yi cikakken amfani da daman da ya samu wajen taimakon mutanen yankinsa ba ta yadda za su yi alhafari da shi.

Nasarar Goodluck Jonathan da ta bayyana kwara daya ce kawai, ita ce yarda da kayan da ya sha a zaben shugaban kasa na 2015 da kuma mika wa Shugaba Buhari mulki, duk da bayanan sirri ya nuna cewa yayi kokarin kin bada mulkin daga baya.

‘’Ina tunanin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan bashi da masu bashi shawara na gari, ganin yadda Allah Ya daukaka shi ba tare da ya wahala ba, ya kamata a ce ya rike mutuncinsa” ‘’Nasara da rashin nasarorinsa a bayyane suke, ya kasa maganin rikicin Boko Haram, duk da yayi shugabancin kasar nan na tsawon shekara 6 hanyoyi a Gabas maso Yamma na nan cikin halin ni ‘yasu bai iya gyara filin jirgin sama na Fatakwal ba duk da kusan duk mako sai yayi amfani ita, an bayyana filin jirgin a matsayin mafi muni a duniya, wadanna sun isa su nuna maka irin rashin tabuka komai da Jonathan yayi a shekara 6 da yayi yana mulki.

“duk da sashin Kudu maso Kudu sun dade suna fafutukan ganin dansu ya zama shugaban kasa, sai gashi Allah ya kadarta ya basu Shugabanci ta hannun Jonathan a cikin ruwan sanyi ba tare da wani wahala ba, “maimakon ya yi aiyukan da mutanensa za su yi alfahari da shi sai ya barar da daman da ya samu”

‘’a halin yanzu ba mu san lokacin da yankin Kudu maso Kudu za su sake samun daman shugabancin kasar nan ba duk da yankin ya na taka rawa mai mahimmancin gaske wajen kasancewar kasar a dunkule”

‘’Daga karshe, lallai an samu babban dama amma an yi asarar ta, ana ganin girman sa da mutuntashi ne kawai domin ya yarda da shankaye a zaben da aka yi, daga baya kuma ta bayyana cewa ya yi kokarin kin bada mulkin daga baya”

‘’Shawara ta gare shi, shi ne ya daure  kada yace zai rinka mayar da amsa akan kowanne magana da ya taso, abubuwan da yayi a lokacin mulkinsa suna nan a bayyane gaskiya bata boyewa.

“saboda karbar kaye da yayi ta ceci kasar nan da rayukan jama’a da dama domin a lokacin hankali ya tashi, ba a san abin da zai iya faruwa ba in da an samu akasin haka, “ya kamata ka rike wannan girman da kasar nan da kasashen waje suke baka, har yanzu kana da sauran gudumawar da zaka iya bayar wa, wata rana sai labara”.

‘’Amma I dan ya ci gaba da abin yake yi yanzu, to tabbas zai rasa komai na daga mutuncinsa”

Da aka nemi Oyegun ya kara haske a kan batun cewa, Jonathan ya nemi ya janye mika mulkin da yayi sai yay i kokarin kaucewa. “wannan wani tarihi ne da zamu bar shi a tsakaninmu, muna dai fatan zai dauki shawarar da mu ke ba shin a kama girmansa”

Ya kuma ce, basu yi mamakin ficewar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yayi daga jam’iya mai mulki ba, ya na mai bayyana cewa, ya nuna alamun ficewa tun fiye da watanni 18 da suka wuce, sai dai bai yarda da cewar Atiku ya fice ne saboda tsananin rikicin da ta dabaibaye jam’iyar. “fitan Atiku abu ne da bai yi mana dadi ba, bama son rasa kowa a jam’iyar mu musammam mutum mai matsayi irin na Atiku, amma fitarsa baabin mamaki bane domin tun watanni 12 zuwa 18 alamomi ke nuna cewar zai fice sai dai ba a san yaushe ko kuma wani lokaci bane”

“A shekarun da Atiku ya yi a duniya, maganan shugabancin kasar nan fa abu ne da dole ya fuskance ta yanzu, na farko in Shugaba Buhari ya yanke shawarar takara a zabe mai zuwa kaga bashi da cikakkiyar dama kenan a APC sai ya yi jiran wasu shekaru 4 kenan bayan nan kuma ana iya mayar da takarar shugabancin kasar a jami’yar zuwa Kudu kaga wasu shekaru 8 kenan wanda shekarunsa ba za su iya jiran wancan lokacin ba, kaga in har yana son takarar shugabancin kasar nan dole ya nemi inda zai gwada sa’ar sa”

“Atiku yace zai kayar da Buhari a zabe cikin sauki, wannan magana ce da ba zata taba yi wu ba, fatan mu kawai shi ne Buhari ya kabi shawarar takara a kakan zabe mai zuwa tun da doka ta ba shi damar sake neman takarar in ya samu nasara kuma yayi mulki har tsawon shekara 4, lallai a ra’ayi na babu yanda Atiku zai kayar da Buhari a fagen zabe a kowanne lokaci.

A wata sabuwa, kungiyar (Northern Emancipation Network) ta gargadi tsohon mai ba tsohon shugana kasa Jonathan shawara a fannin yada labarai Reno Omokri da ya daina munanan kalamai a kan gwamnan jihar Barno Kashim Shettima, kungiyar ta yi wannan bayanin ne a sanarwar da shugaban ta Abdul’Azeez Suleiman ya sanya wa hannu, sun kara da cewa mutanen Arewa na matukar girmama matsayin Shettima na shugaban gwamnonin yanki Arewa saboda haka ba zasu zura ido ana ci masa mutunci ba, “burin mu shi ne samar da kasa da za a mutunta shugabanni ba tare da la’akari da wani bangare suka fito ba”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here