Matashi Ya Sare Kan Mahaifiyarsa A Osun

338

Daga Umar A Hunkuyi

Rudunar ‘Yan Sanda ta Jihar Osun ta sami nasarar damke matashin nan da ya datse kan Mahaifiyarsa a ranar Litinin din nan. Matashin mai suna, Joseph Mark dan shekara 25, wanda yake karatun Digirinsa a Jami’ar Adekunle Ajasin, da ke Jihar Ondo, a ranar Lahadin da ta gabata ne ya aikata wancan danyen aikin.

Mai magana da yawun rundunar ‘Yan Sandan ta Jihar Ondo, , DSP Folashade Odoro, ta bayyanawa manema labarai a Osogbo cewa, wannan abin asshan da matashin ya aikata ya faru ne da misalin karfe, 6:30 na safe, a gida mai lamba 25, a rukuni na 5, kan titin A jemobi, Layin Eko-Ende, Ekirun, Osun.

Odoro, ta shaidawa manema labaran cewa, mahaifin matashin ne, Mista Adewale Mark, ya kai rahoton faruwar lamarin a ofishin ‘Yan Sanda da ke Ikirun.

Ta bayyana cewa, mahaifin matashin ya bayyana masu cewa, shi ya bar gida ne a ranar da lamarin ya faru da misalin karfe 5:30 na safe, da nufin ya ziyarci wani abokinsa da ke layin gaba da na su, ko da dawowarsa gida ne da misalin karfe 6:30 na safiyar, sai ya taras da [an nashi ya datse kan matarsa da Adda.

Odoro ta kara da cewa, wanda ya aikata laifin da ake kyautata zaton kanshi ba daya ne ba, ‘Yan Sanda sun sami nasarar damke shi ne a lokacin da suka isa wajen da ya aikata aika-aikar.

Tana mai cewa, dukkanin wasu shaidu da suka hada da, sakamakon binciken lafiyar mai laifin daga Likita, makamin da ya yi amfani da shi wajen aikata laifin, hotunan wajen da abin ya faru da kuma ita wacce wannan hatsarin ya rufta da ita, duk suna wajen ‘Yan Sanda.

Ta kuma karkare da cewa, sun ajiye gawar mamaciyar ne mai suna, Uwargida Christianah Mark, ‘Yar shekaru 62, a dakin ajiyar gawarwaki, sannan kuma suna nan suna ci gaba da zurfafa bincike kan lamarin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here