Jarumi Buhari Ya Kubuta Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane

591

Daga Muhammad Inuwa, Abuja

Rahotanni daga Jos babban birnin jihar Filato na bayyana cewa, fitaccen jarumin nan dan wasan Hausa, Al’amin Buhari, ya samu kubuta daga hannun wasu masu garkuwa da mutane, wadanda su ka yi awon gaba da shi na tsawon wani lokaci.

Rahotannin sun nuna cewa, ya samu kubuta ne bayan an biya wata diyya wacce ba a gama tabbatar wa da wakilinmu ba, amma dai wata majiya ta ce, an biya diyyar zunzurutun kudi Naira 500,000 ne.

Bayanan sun nuna cewa, da fari ba shi kadai a ka kama ba, amma dayan ya samu kubuta kafin a yi awon gaban da su. Sai dai shi ma Jarumi Buhari ya sami kansa bayan dan wani lokaci, inda rahotanni ke nuna cewa, ya koma cikin iyalinsa a birnin na Jos.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here