Kotu Ta Yi Watsi Da Shari’ar Sanata Yarima A Zamfara

485

Daga Hussaini Baba, Gusau

Babbar kotu ta hudu da ke Gusau, Baban Birinin Jihar Zamfara, karkashin jagorancin Mai Shari’a Bello Muhammad Tukur ta yi watsi da tuhumar da hukumar yakar cin hanci da rashawa ta Kasa watau ‘ICPC’ ta ke yi wa Sanata Yarima, dangane da zargin karkatar da naira biliyan daya na aikin Madatsar ruwa ta Gusau.a lokacin da yana Gwamnan Jihar.

Mai Shari’a Bello Muhammad Tukur ya bayyana cewa a bisa gamsuwa da hujjojin da masu kare wanda ake tuhuma suka bayyana wa kotu, akan haka ne kotu ta gamsu da su. don haka ta yi watsi da Shari’ar.

Lauyan Hukumar ICPC Ya bayyana cewa su basu da hurumin magana da ‘yan Jarida don suna wakiltar gwamnatin tarayya ne. Amma ya bayyana cewa za su daukaka kara zuwa kotu ta gaba.

Lauyan Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura ,Barista Ifeanye Augustter Azuamashi, ya bayyana cewa gaskiya ce ta yi halinta. Kuma kotu ta tabbatar da haka. “Tuni muka ce a yi watsi da shari’a, amma yanzu da ta gama bincikenta gashi ai an yi watsi da ita.muna godiya ga Allah da ya bamu wannan nasara.”in ji Lauyan

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Sanata Yarima, ya yi godiya ga Allah bisa wannan mataki da kotu ta dauka.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here