Nijeriya Na Dab Da Amso Dukiyar Da Abacha Ya Sace – Minista

217

Daga Umar A Hunkuyi

Babban Lauyan Kasarnan kuma Ministan Shari’a, Mista Abubakar Malami, ya ce, Gwamnatin Kasar Switzerland ta shirya tsaf domin maidowa da Kasarnan wasu dunkulallun kudade da aka sace da yawansu ya kai Dalar Amurka Milyan 321, suka kuma makale a wasu Kasashen waje, da ake zargin tsohon Shugaban Kasarnan ne Janar Sani Abacha da iyalansa ne suka sace daga asusun wannan Kasar ta mu.

Wannan bayanin ya fito ne daga Ofishin Babban Mai Shari’a na Kasarnan, ta bakin mai ba shi shawara na musamman a kan harkokin yada labarai, Mista Salihu Isa, a ranar Talatan nan, yana mai cewa, hakan ya samu ne a sakamakon wata yarjejeniyar fahimtar juna da aka sanyawa hannu a tsakanin Kas ashen Biyu da kuma Babban Bankin Duniya a can Kasar Amurka ranar Litinin.

Kamar yadda Mai taimakawa Ministan ya fada, Minista Malami ne ya sanya hannu a madadin Gwamnatin Tarayya, tare da wakilan Gwamnatin ta Kasar Switzerland da kuma Jami’ai daga Babban Bankin na Duniya. Ya kuma kara da cewa, Jagoran Jami’an Gwamnatin Ta Kasar Switzerland wanda kuma zai sanya hannu a madadin Gwamnatin ta Kasar Switzerland shi ne, Roberto Balzaretti, a sa’ailin da Babban Daraktan yanki na Babban Bankin Duniya da ke Abuja, Mista Rachid Benmessaoud, ne zai sanya hannu a madadin Babban Bankin na Duniya.

Ya kuma bayyana cewa, yarjejeniyar ta fayyace hanyoyin da Kasar ta Switzerland za ta bi wajen maido wa da Nijeriya da Kudaden da yawan su ya kai Dala Milyan 321.

Ya ce, za a maido wa da Nijeriya Kudaden ne kashi-kashi, a karkashin wani shirin kyautatawa al’ummar Kasa da samar masu da tsaro, mai suna, “the National Social Inbestment Program” a Turance.

“Wannan yarjejeniyar kuma ita za ta sanya ido wajen ganin an yi amfani da Kudaden a bisa yanda aka tsara, da kuma daukar kwakwaran mataki a kan duk inda aka nemi a yi wasan wa-ka-ci-ka-tashi da kudaden.

“Yarjejeniyar kuma har’ila yau ta yarda da sanya idon kungiyoyin fararen Hula a kan yadda ake kashe kudaden. Dawowa dai da wadannan Kudaden ya karfafa samun nasarar shirin nan na samar da dawwamammen ci gaba a Duniya na nan da shekarar 2030.

Ya kuma bayyana cewa, da farko dai su wadannan Kudaden da aka sata an jibge su ne a Ludembourg, kafin daga bisani Gwamnatin Kasar ta Switzerland ta kwace su a watan Disamba na shekarar 2014, a karkashin tuhumar nan ta almundahana, da Gwamnatin Kasar ke wa daya daga cikin ‘Ya’yan Marigayi Abachan mai suna Abba Abacha.

Bayanin ya ci gaba da nu na cewa, “Wannan yarjejeniyar da aka sanyawa hannu ta baiwa Nijeriya damar sanin dukkanin abubuwan da suka faru a wancan lokacin, da kuma karin hanyoyin da Kasar za ta bi wajen ganowa da kuma maido da kudaden na ta da mahandaman Shugabanni suka sata.

“Sannan kuma Nijeriya za ta yi amfani da wannan daman a wajen taron da za a yi a Washington, domin tattaunawa yanda za a bi a dawo da sauran kadarori da Kudaden kasar da aka sata, kamar yanda hakan zai ba ta daman tattaunawa da sauran kasashe wajen sanin hakikanin Kudadenta da aka sata aka kuma jibge su a kasashen na su.”

Wakilan  Nijeriya da za su jagoranci zaman a can Washington suna karkashin jagorancin Ministan Shari’a ne Malami. Sauran wakilan sun hada da, mai taimakawa Shugaban Kasa a kan harkokin Shari’a, Uwargida . Juliet Ibekaku-Nwagwu; da Mataimakin Darakta a Ma’aikatar Shari’a Uwargida Ladidi Abdulkadir, Wakili daga Kungiyoyin fararen hula, Rabaran Dabid Ugolor.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here