RAHOTON MUSAMMAN: Mata Biyar Da Ke Da Matukar Hadari A Duniya

759

Daga Idris Sulaiman Bala

A lokuta da dama ayyukan barna na da alaka ne da kungiyoyi ko gamayyar ‘yan daba. Idan a na batun mutane masu hadarin gaske, abin farko da zai fara zuwa kwakwale shi ne mafiya hadari su ne maza. Wannan rahoton zai karawa mai karatu sabon ilimi na labarin mata da ke da hadarin gaske, wadanda ke da ruwa da tsaki a cikin harkokin dabanci da ta’asa.

A shekarun baya, da zaran an ji labarin cewa an maka wata Mace a kotu domin yin shari’a, mutane su kan cika da tausayinta. Amma a yanzu dole ta sa wannan tausayi ya fara kaura daga zukatan jama’a, saboda kamarin da mata su ka yi a aikata barna.

Jaridar LEADERSHIP A YAU ta yi nazarin wasu mata guda biyar wadanda ke da hadarin gaske a duniya, kuma su ka tara dukiya mai tarin yawa ta hanyoyin dabanci da sauransu. Wadannan mata su ne wadanda ke sa maza tsima da karkarwa. Za mu ga yadda wadannan mata ‘yan daba su ka fuskanci hukunci kotu da irin harkallar da su ka shuka.

Haka kuma labarin wadannan mata masu hadari zai sa mutane su daina yiwa mata kallon biyuu – ahu. Mata sun san dadin kudi, don haka su ma su na iya aikata komi don su same su. A wurin samun kudin su kan yi kisa, da sauran abubuwan saba doka.

  1. MARIA LEON

Ba abu ba ne mai sauki ga mace ta iya kula da ‘ya ‘yanta guda 13 alhali ta na jagorancin wata tafiya, musamman kungiyar ‘yan daba ta duniya. Wannan shi ne babban abin da ke tsorata mutane dangane da Maria. Ta kasance shugabar wata kungiyar masu safarar miyagun kwayoyi da ‘yan mata a sassa daban daban na duniya. Ta na samun goyon bayan kungiyoyin ‘yan daba da ke kasar Medico, wanda wannan ya ci gaba da jefa tsoronta a zukatan ‘yan daban da ke Los Angeles.

Rahoton ‘yan sanda ya bayyana cewa kungiyar da Maria ke jagoranta ta gawurta ta yadda duk yanki da su ka shiga sai an yi zaman makoki.   A shekarar 2008, danta Danny wanda a ka fi sani da ‘Cleber’ yam utu a musayar wuta da ya yi da ‘yan sanda. A wannan lokacin da danta din yam utu Maria ta shiga buya a kasar Medico, amma saboda mutuwar sai ta bayyana domin halartar jana’iza a kasar Amurka.

Kasar Amurka ta ki ta lamuncewa Maria tikitin shiga, saboda haka ne ta yi amfani da wasu ‘yan ta’adda cikin yaranta, domin su shigar da ita kasar ta Amurka ta barauniyar hanya. Maria ba ta san ashe jami’an tsaron Amurka na bibiyansu ba, wanda sai da su ka durfafi marabar kasar Amurka da Medico sai a ka yi ram da su. A kotu an yanke ma Maria hukuncin daurin shekaru 8 a gidan kurkuku, sauran kuma wa’adinsu bai kai nata ba.

  1. JEMEKER THOMPSON

A duniyar mabarnata an fi sanin Jemeker da suna ‘Kueen Pin’ iyayenta sun kasance talakawan gaske, wanda hakan ya sa ta kuduri aniyar sai ta yi kudi ko ta wanne hali. Ta auri mijinta mai sunaAnthony Mosley, wanda su ka haifi da a tare. Wannan aure da su ka yi ne ya jefa su  gadan – gadan a cikin sana’ar siyar da diddigar hodar iblis.   A tsakankanin 1980s gamayyarsu ce kungiyar da ta fi karfi a harkar hodar Iblis a Los angeles.

An kashe mijinta Anthony ne wata rana yayin da ya ke goge motarshi. Wannan mutuwar ta mijinta ta tsima Jemeker amma bai zamar mata izna ga dillancin hodar iblis ba, sai dai ma ta kara habbaka sana’ar, wanda ta yi ta hada makudan daloli duk wata. Daga bisani ta hada gwiwa da wani dilan hodar iblis, wanda a ‘yan sanda su ka cafke , da ya ji yaji sai ya bayyana sunan Jemeker a matsayin abokiyar huldarsa.

Tsoron fadawa komar ‘yan sanda ta sa Jemeker ta shiga buya har na tsawon shekaru biyar, ba a sake jin duriyarta a Los angeles ba, har sai ranar da danta ya ke bukin kammala karatunsa. A wurin wannan bukin ne ‘yan sanda su ka yi mata kofar rago, su ka cafke ta. An yanke mata hukuncin shekaru 15 a gidan yari.

  1. JUDY MORAN

An haifi Judy a ranar 18 ga watan Disambar 1944, ta kasance shugabar kungiyar ‘yan daba ta ‘Moran Family’, wadanda a baya ba wani kaurin sunan da duniya za ta mayar da hankali a kansu su ka yi ba. sun kasance su na gudanar da ta’asarsu ne a Melbourne ta kasar Australiya. Kungiyar ‘Moran Family’ ta kasance kungiyar da a ke shakka ne sakamakon safarar miyagun kwayoyi da su ka shiga. Mijin Judy na fari, Leslie Cole, ya mutu a wata musayar wuta da kungiyarsu su ka yi da wata kungiya a shekarar 1982. Danta Mark Cole, shi ma an bude mishi wuta har lahira a shekarar 2000.

Ta sake auren wani mutum mai suna Lewis Moran wanda su ka haihu tare, sunan dan na su Jason Moran wanda shi ma a ka bude mishi wuta har lahira a shekarar 20003. Kanin mijinta, Des Moran shi ma ya sha harsasan ‘yan adawa har lahira a shekarar 2009. Amma bisa kisan kanin mijinta, jami’an tsaro sun cafke Judy tare da wasu mutum uku bisa zargin kisan kanin mijinta din.

A lokacin da jami’an tsaro su ka bukaci iznin kotu domin bincikar gidan Judy, kafin su kai ga yin binciken, sai wasu ‘ya ‘yan kungiyarta su ka bankawa gidan wuta komi ya kone, wannan ya sa a ka yanke mata hukuncin daurin shekaru 26.

  1. CLAUDIA OCHO

Claudia Ochoa Felid ta shahara ne da sunan ‘Kim Kardashian din mabarnata’, hotunanta sun yi ta yawo a yanar gizo, musamman kafar sadarwa ta hanyar hotuna ‘Instagram’. A shekarar2014, wata jarida mallakin gwamnatin Birtaniya ta wallafa cewa Claudia ta cimma matsayin shugabar kungiyar ‘yan daban kasar ‘Medico’ mai suna ‘Los Antrad’, kungiyar da ta shahara wurin aikata manyan kashe – kashe.

Jami’an tsaron farin kaya na kasar Amurka sun fid da rahoton cewa kungiyar daban da Claudia ke jagoranta, ita ce kungiya mafi hadari a harkar safarar ‘yan mata a duniya, sannan kungiyar cike ta ke da makasan da ba su da imani ko miskala. Claudia ta zamto shugabar kungiyar ne bayan da a jami’an tsaro su ka yi ram da tsohon shugaban kungiyar mai suna Jose Rodrigo Arechiga ‘Elchino’, kuma tsohon saurayinta. An kama Elchino ne a shekarar 2010 bisa zargin kisan wasu manyan mutane da a ka samu a sargafe a wata gadar sama da ke babban birni kasar Medico.

Duk da cewa ita Claudia ta na samun lokacin kulawa da ‘ya ‘yanta guda uku, amma wannan bai kange ta daga ci gaba da jagorantar kungiyar ‘yan daba ta ‘Los Antrad’ ba.

 

  1. SANDRA ÁBILA BELTRÁN

An haifi Sandra a ranar 11 ga watan Oktoban shekarar 1960. A lokacin da ta jagoranci wata kungiyar masu safarar hodar iblis a kasar Medico ta shahara da sunan ‘The Kueen of the Pacific’.  Ta yi aure har sau biyu, dukkanin mazajen biyu sun kasance tsofaffin ‘yan sanda ne wadanda su ka watsar da aikin su ka shiga sana’ar safarar hodar Iblis. Kuma dukkan mazajen nata an yi amfani da kwararrun maharba daga nesa ne wurin halaka su.

Sandra ta na da wayo fiye da tsammanin mutane, ba ta yarda ta bar wata shaida bayan ta aikata barna, balle ‘yan sanda su samu su yi amfani da ita. Sai a shekarar 2002 ne alkadarinta ya fara karyewa, bayan da a ka sace Yaronta sannan a ka bukaci ta biya Dalar Amurka Biliyan 5 fansa ga dan nata. Bayan ta amso Yaron na ta ne, ‘yan sanda su ka kaddamar da bincike na musamman a kanta.

A shekarar 2007, an gurfanar da ita a gaban kotu da laifin yin hadaka da mabarnata wurin aikata manyan laifuka ciki har da safarar miyagun kwayoyi. Duk da ya ke bayan sauraron shari’ah an yi watsi da wasu tuhume tuhumen da a ke yi mata. Duk da haka an kama ta da laifin mallakar makamai ba tare da izni ba, da kuma kudin ruwa. Har zuwa hada wannan rahoto Sandra ta na garkame a gidan yari.

 

 

 

 

 

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here