Wani Mutum Ya Kashe Kansa Saboda Bashi

329

Daga Mustapha Hamid

Wani Mutum mai shekarun haihuwa 57 mai suna Olajire Otunla ya kashe kansa ta hanyar rataya, saboda bashin kudi da ake bin sa da ya kai Naira 300,000.

Lamarin wanda ya faru a adireshi mai lamba sw8/634 da ke kan Titin Ososami/Oke-Ado da misalin karfe 1:30 na rana ya yi matukar girgiza al’umomin da ke zaune a yankin, da yawan su da suka zanta da Jaridar ‘Nigerian Tribune’ bisa sharadin za a boye sunayen su sun bayyana cewa, marigayin Mutum ne mai matukar saukin kai.

Yayin zantawar ta da Jaridar ta Nigerian Tribune, Matar marigayIn, Mrs. Monisola Otunla wacce ta ke sana’ar sayar da Abinci, cikin kuka ta bayyana cewa, “Mijina dan kasuwa ne, mai sana’ar sayar da kananan Kayan ciki na Maza, Mutum ne mai matukar kwazo, yau bai fita ya tafi wurin sana’ar sa ba, dan haka yana zaune a cikin Gida”.

“Da misalin karfe 1:30 na rana, na hau saman Benen Gidanmu domin in ajiye wasu Kayayyakin Kicin da na yi anfani da su dan shirin sana’a ta na Abincin gobe, saboda Shagona yana kasan Benen Gidan namu ne, na yi ta kwankwasa Kofar Dakinmu, amma na ji shiru ba a amsa ba, daga nan ne na sanar da makwabtan mu, inda su ka zo su ka taya ni balle kofar Dakin, ballewar mu ke da wuya, sai mu ka tarar da gawar sa tana reto, ga Igiyar nan daure a Wuyarsa wacce ya dauro a jikin Karafunan Tagar Dakin namu”.

Yayin da aka tanbaye ta ko tana da masaniya a kan abinda take gani ya janyo Mijin nata ya kashe kan nasa, sai ta bayyana cewa, “duk da cewa bai fiye bani labaran matsalolin da ke damun sa ba, amma dai na san da cewa ana bin sa bashin kudi Naira 300,000, wata kila dalilin da ya sanya ya kashe kan nasa kenan, amma bai bar wata Takarda mai dauke da wsiccin dalilin da ya sanya ya kashe kan nasa ba”.

Daya daga cikin ‘ya’yansa Bolade Otunla ya bayyana wa Jaridar ta Nigerian Tribune cewa, “wani ne ya bugo mini Waya, ya shaida mini cewa lallai-lallai ko me na ke yi in komo Gida a take, saboda Mahaifina ya kashe kan sa, lamarin yana da matukar girgizawa, har yanzu na gagara gane dalilin da ya sa ya aiwatar da wannan danyen hukunci”.

Jaridar ta Nigerian Tibune ta tattara bayanan da ke nuna cewa, Otunla ya mutu ya bar ‘ya’ya 4, Maza biyu da Mata biyu, biyu daga ciki sun kammala karatun su na Jami’a, 1 daga cikin su makonni biyu da suka gabata aka yi bikin kammala karatun nasu, wanda har marigayin mahaifin nata ya samu daman halarta, yayin da daya dan nasa ana shirye-shiryen gudanar da bikin kammala karatun Jami’ar nasa ne nan da makonni biyu.

Jami’an tsaron ‘yansanda daga Ofishin yanki na Orita Challange sun halarci Gidan Mamacin da misalin karfe 3:00nr, bayan da suka gama nazarce-nazarcen aikin su, sai aka wuce da gawar mamacin zuwa dakin ajiye gawarwaki na Adeoyo.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here