Zuwan Buhari Kano Yau: An Tsaurara Tsaro

733

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

A ziyarar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai kai Kano a yau, an tsaurara matakan tsaro.

Wakilinmu a Kano ya ruwaito cewa an kawata muhimman titunan Jihar Kano da jami’an tsaro, wadanda ga dukkan alamu cikin shirin ko-ta kwana suke don tarbar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Daga rahotannin da wakilinmu ya harhado mana, akwai iyayen da suka yi ta tunanin yiwuwar hana ‘ya’yansu fita ko dakile zirga-zirgar ‘ya’yan nasu a yau da gobe, ganin yadda jami’an tsaron suka cika gari.

Sai dai a bangaren gwamnati, wannan tsaro da aka tsaurara ba komi bane face, irin tsaro na kiyaye ka’ida. Babban Mai Magana da yawun shugaban Kasa, Garba Shehu, ya bayyana cewa, babban kudurin gwamnatin Buhari na farko shi ne tsaro. Domin ko ba komi, gwamnatin ta iya samar da tsaro a Kano, domin gari ne wanda a baya aka yi ta samun tashe-tashen bama-bamai da kashe-kashe. Tun bayan hawan Buhari mulki, ba a taba samun makamancin wannan ba.

Shugaban Kasa Buhari dai ya shafe shekaru biyu har da doriya a ofis, amma bai samu damar ziyarar Kano ba, wanda hakan ke alamta wasu tambayoyin da kila har yanzu aka gaza samun gamsasshiyar amsarsu. Shugaban fara nuna sha’awar takarar shugabancin kasa tun dawowar dimokradiyya a shekara ta 1999, wanda sai da ya tsaya takarar har karo uku kafin daga bisani ya samu nasarar dafe madafun ikon mulkin Nijeriya.

Jihar Kano ce Jihar da ta samar wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari kuri’ar da wani dan takara bai taba samunta ba a Nijeriya, inda Jihar Kano ta kada masa kuri’a sama da Miliyan biyu a kakar zaben shekarar 2015, Sannan kuma ita ce Jihar da ko Jihar Shugaban kasar ta haihuwa Jihar Katsina basu nunawa shugaban kasar kaunar da ya samu a Kano ba. Amma akwai wasu abubuwa da masu harsashe suka kasa gane musabbabinsu abubuwan da ake yiwa Kanawa ba.

Daga cikin korafin wasu jama’ar Kano akwai, cewa ita ce cibiyar ciniki a kasashen arewacin Sahara wadda ta gamu da annobar gobara kusan kashi biyar, daya daga cikin wadannan gobara itace wadda kasuwar Sabon Gari ta fuskanta, gorar da aka shafe kwanaki bakwai ta na ci, amma shugaban kasa Muhammadu Buhari bai iya sarayar da minti 15 ba domin zuwa Kano don Jajanta wa ‘yan Kasuwa bisa wannan bala’i da ya afka musu da sauran al’ummar Kano. Haka aka yi ta rajin rarrashin Kanawa kan rashin zuwansa jihar don jajanta wa kan wannan matsala da aka fuskanta.

An samu rasuwar manyan mutane a Jihar Kano irinsu Magaji Danbatta OFR, Dan Masanin Kano, ABM Muktar Muhammad da sauransu, amma wannan ma bai sa shugaban Kasa zuwa Kano domin yi wa Kano da Kanawa ta’aziyya ba. Har wasu ke kallon lamarin a matsayin tsananin tsana da kuma rashin gamsuwa da dangantakar da ake zato akwai tsakanin Shugaban Muhammadu Buhari da Kanawa. Lamarin da yasa har wasu suka fara yanke zaton akwai wani abu na amintaka da ya rage tsakanin al’ummar da suka yi uwa kuma suka yi makarbiya wajen jajircewar ganin burin jama’a ya cika na zabarsa amatsayin shugaban kasa.

Cikin abubuwan da jama’ar Kano ke fatan samun amsarsu su ne shin a fadin jihohin Nijeriya 36 har da Abuja wace Jiha ce Shugaban kasa ya samu kuri’a sama da miliyon biyu? Wacce Jiha ce suka kirkiri shirin akasa, a tsare, a jira sanann kuma a raka idan ka cire Jihar Kano? wacce jihar ce da ta taka waccen rawa kuma har yanzu wasu daga cikin talakawan jihar ke kyautatawa shugaban kasar zato, amma kuma ya shafe shekara biyu da doriya bai taka kafarsa jihar ba? Shin wanann ziyara ta wuni biyu itace sakayyar kauracewa Jihar Kano da shugaban Kasa Muhammadu ya yiwa Jihar na tsawon shekaru biyu da doriya?

Wani abin kuma da aka kasa  samun fahimta a kansa shi ne a lokacin da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ziyarci Kano an rufe hanyoyi a Jihar Kano, wai bisa zargin akwai tsana tsakanin shugaban kasar da al’ummar Kano, to shi kuma shugaban Kasa Muhammadu Buhari wanda Kanawa suka bashi kuri’a sama da miliyon biyu, wanda aka kwana aka wuni ana jiran sakamakon zabensa, akwai mutanen da aka tabbatar da yin bakancen a zumin Kwanaki arba’in da daya domin fatan samun dorewar lafiyar shugaba Muhammadu Buhari alokacin da yake fama da rashin lafiya, a Jihar Kano ne aka gudanar da saukar alkur’ani sama da dubu daya da dari daya da goma sha daya domin samun saukin shugaban, amma duk da haka wanann bai sa shugaban yin abinda Kanawa ke kyautata masa zato ba.

Yanzu dai shugaban kasar da Kanawa suka nunawa waccan kauna sai gashi a ziyarar wuni biyu da zai kai jihar Kano an rufe manyan hanyoyin da suka zarta sauran tururuwar jama’a ko dai wajen shigowa harkokin kasuwanci ko kan hanyarsu ta zuwa wuraren ayyukansu, wadannan hanyoyin sun hadar da hanyar titin zuwa Gidan adana namun daji (Zoo Road) titin zuwa unguwar Giginyu, Panshekar/Madobi, Kofar ruwa/Katsina Road, Maiduguri Road da sauransu.

Haka kuma akwai wata sarkakkiyar dake zaman kanta tsakanin gwamna mai ci yanzu a Kano da kuma Sanatan Kano ta tsakiya Sanata Rabiu  Musa Kwankwaso, wanda yanzu haka sanarwa ke gudana a Kano cewar ba’a yarda aga kowa da jar hula a wuraren da shugaban kasa zai ziyarta ba, wannan matsala na cikin irin matsalolin da aka kasa mantawa dasu a zukatan Kanawa, musamman ganin yadda jama’ar Kano ke ganin girman shugaban kasar, wanda akayi zaton zai kira Gwamna Ganduje da Sanata Kwankwaso ya nunawa kowa kuskurensa tare da dinke wannan baraka.

Amma kuma hakan ba sabon al’amari ba ne idan aka tuna lokacin Muhammdu Buhari na takarar a Jam’iyyar CPC kafin ficewarsa daga Jam’iyyar, anga yadda a jihar Kano Jam’iyyar CPC ta shiga takarar kujerar Gwamna da ‘yan takara biyu, Muhammadu Abacha da Lawal Jafaru Isa, hakan ce ta faru a Katsina da Bauchi, Shugaban bai iya sasanta rikicin ba har sai da aka kai keyar Jam’iyar CPC Kasa duk irin farin jinin ta. Wanann ma na cikin abubuwa da Jihar, Kano ke dandana dangane da fata da kyakkyawan zaton da Kanawa suka yiwa Buhari

Alhaji Rarabi Dahiru guda ne cikin masu adawa da salon mulkin Jam’iyyar APC ya bayyana cewa mu bamu yi mamakin hakan ba domin juma’ar da za tayi kyau tun daga Laraba ake gane ta, kuma sanin kowa ne Buhari ba ya fiya, jihar Kano ko al’ummar Kano na da wani tabo da kila Buharin ke kallo, da farko an samu babbar matsala tsakninsa da tsohon Gwamna Malam Ibrahim Shekarau lokacin da yake gwamna, sannan kuma da lokacin da aka kafa Jam’iyyar hadaka ta APC wanda akarshe Shekarau ya fice daga cikinta. Sai kuma tsakaninsa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda suka shiga zaben fidda gwani tare shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin kuwa alokacin Kwankwaso ya samu kuri’a sama da dai takwas ya yin Buhariya samu kuri’a dubu daya da doriya. Wasu na ganin cewa ko wadannan da wasu dalilan da shi kadai ya barwa kansa sani ne kila suka jawa Kano da Kanawa shiga irin wannan takun sakar da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here