Al-Makura Ya Hana Kiwon Dare A Nasarawa

119

Daga  Umar A Hunkuyi

Gwamnan Jihar Nasarawa, Umaru Tanko Al-Makura, ya hana dukkanin makiyaya dabbobi yin kiwon dare a fadin Jiharsa.

Gwamnan wanda ya sha alwashin ganin bayan dukkanin wadansu rigingimu da tashe-tashen hankula, musamman a tsakanin Manoma da Makiyaya, da ke ci wa Jihar tuwo a kwarya, gami da sauran manya laifuka daga Jihar.

Gwamna Al-Makura, ya fadi hakan ne Jiya a garin Keffi wajen wani taro na masu ruwa da tsaki, da ya gudana a garin na Keffi, ya bayyana cewa, hanin, ya biyo bayan yawaitar koke-koken da Manoman Jihar ke yi ne, wanda suke kokawa da yawaitar barnar da makiyayan ke yi masu cikin gonakinsu a cikin dare.

Al-Makura, wanda mai ba shi shawara na musamman a kan harkar tsaro, Janar Mohammed Adeka, mai ritaya, ya wakilta,yace, Mun hana yin kiwo ne ga makiyaya a cikin dare, musamman a daidai wannan lokacin na Kaka, domin mu gujewa dukkanin wata tarzoma da ka iya tasowa.

Hakanan Gwamnan, ya yi jimamin yawaitar ayyukan ta’addanci na fashi da makami, da kuma yin garkuwa da mutane a Jihar, wadanda a cewarsa, suna matukar yin barazana ga matafiya da suke bi ta cikin Jihar, da kuma masu kasuwancin amfanin gona da Jihar ke tinkaho da su. “Muna gargadi da kakkausar murya ga Makiyaya da su nisanci tabawa ko lalatawa Manoma kayan amfanin gonarsu, sannan kuma muna yin kira ga Manoma da su hanzarta kawar da amfanin gonar na su da zaran lokaci ya yi, in ji Gwamnan.

Gwamnan kuma ya gargadi Manoman Jihar da su nisanci toshewa Makiyaya burtalolinsu, yana mai shawartar Makiyayan da su hanzarta kaiwa Hukumomin da suka dace rahoton hakan idan ya faru, domin daukar matakan da suka dace.

Daga nan, sai Gwamnan ya kirayi dukkanin Dagatai da Shuwagabannin al’ummomin Jihar da su hada kai da Jami’an tsaro wajen bayar da rahoton dukkanin wani abin da ba su ganewa take-takensa ba.

A lokacin da yake mayar da martani a madadin sauran Sarakunan yankin, Ohimega Opanda, Usman Abdullahi, ya yi kira ne da a baiwa Sarakunan kasarnan Kudade na musamman da za su taimaka masu wajen aiwatar da ayyukansu, musamman ta fuskacin tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here