Kasar Wales Ba Za Ta Dauki Mai Koyarwa Dan Ingila Ba

29

Daga Abba Ibrahim Wada

Hukumar kwallon kafa ta kasar Wales ta kawar da yuwuwar daukar dan kasar Ingila a matsayin kocin tawagar yan wasan kasar saboda wasu dalilai.

Hukumar na fatan ganin ta samu wanda zai gaji tsohon mai koyar da ‘yan wasan kasar Chris Coleman a kan lokaci domin tunkarar gasar kasashen Turai ta Natios League ranar 24 ga watan Janairu.

Shugaban hukumar kwallon ta Wales Jonathan Ford ya ce a ko da yaushe sukan dauki ‘yan Wales a wannan aiki, saboda suna da sha’awar aikin, to amma a wannan karon dan waje za su dauka amma kuma ba dan kasar Ingila ba.

Kociyoyin Wales shida na baya bayan nan ciki har da na rikon kwarya dukkaninsu ‘yan yankin ne, in banda Bobby Gould, dan Ingila wanda ya rike tawagar daga shekarar 1995 zuwa 1999.

Mai koyarwar yan wasan kasar na baya bayan nan Chris Coleman ya raba gari da Wales din saboda kasa samun gurbin gasar cin kofin duniya da za a yi a shekara mai kamawa ta 2018 a Rasha, a lokacin bazara mai zuwa.

Yayin da yankin ke ci gaba da neman kociya, Wales din ba ta da wani wasa a nan gaba, sai a gasar China Cup a shekara ta 2018 mai kamawa.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here