Kwastam Ta Tara Sama Da Naira Miliyan 145 Cikin Shekara Guda A Adamawa

48

Daga Muhammad Shafi’u Saleh, Yola

Hukumar hana fasa kwaurin kayayyaki ta kasa (Nigeria Costoms Serbice) shiyar Yola, ta bayyana kimanin naira miliyan dari da arba’in da biyar da dubu talatin da daya da dari tara da tamanin da takwas da kwabo saba’in da takwas, cikin shekara guda.

Shugaban hukumar shiyar jihohin Adamawa da Taraba Adetoye Frances, ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Yola, ya ce hukumar ta kuma kame kayayyakin da aka shigo dasu jihar ta barauniyar hanya na sama da naira miliyan dari da goma sha tara.

Shugaban hukumar ya ci gaba da cewa “wannan lokaci na karshen shekara wasu gurbatattun mutane kan shigo da kayayyakin da wa’adin aikinsu ya kare, musamman tayoyin mota domin kawai su kashe mutane.

“saboda haka jami’an mu suna nan mun sa’ido domin tabbatar da hana shigar da irin wadannan kayayyakin kasuwa, matattun tayoyi su ke haddasa hadara da kashe mutane duk shekarar” inji Frances.

Shugaban hukumar ya kuma yaba da irin hadinkai da goyon bayan da yake samu daga gwamnati da jama’ar Adamawa, yace musamman goyon bayan da hukumar ke samu daga sarakunan gargajiya.

Yace “sarakunan gargajiya musamman masarautar Mubi tana bamu kyakkyawar hadinkai da goyon baya, kuma da ke ta hada iyaka da Jamhoriyar Kamaru, aikinmu na gudana yadda ya kamata” inji shi.

Haka shima shugaban yanki na hukumar kwaston da ke Bauchi Fatade Ali Ola Kunle, yace dama aikin hukumar aiki ne na jama’a da ke bukatar samun hadinkai da goyon baya, domin cimma nasara.

Yace “mu aikinmu na jama’a ne, abune mai kyau a ci gaba da aiki tare da hadinkai domin mu cimma nasaran shawokan matsalar shigo da gurbatattun kaya cikin kasar mu” inji Ali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here