Muna Bukatar Gyara!

111

Shugabannin Nijeriya a matakai daban-daban za ka ji a na yaba wa wasu bisa wasu abubuwa wadanda hakkinsu ne su sauke shi ko kuma bisa samun wani mukami da su ka yi.

Hakika yaba kyauta tukuici ce, kamar yadda ’yan Magana su ke fada kuma a dabi’a ta dan adam zai so ya a yaba ma sa a lokacin da ya yi abin yabo, to amma a zahirin gaskiya mu ba yabo mu ka saba yiwa shugabanninmu, a’a, bambadanci ne, la’alla ko dai don haka su ke so a yi mu su ko kuma don bambadancin ya zama jinin jikinmu.

Ba za mu ce kada a rika yaba wa shugabanni a lokacin da su ka yi abinda ya dace ba, amma a hakikanin gaskiya yawancin abubuwan da shugabannin kasar a matakai daban-daban su ke yi ba su cancanci yabo ba, idan a ka yi la’akari da yanayin dukiyar da su ke mallaka bayan sun rike mukamai daban-daban.

Ko da za ka ga shugaba ya yi wani aiki na abin a zo a gani, to amma babban abin lura shi ne, a yau za ka iya samun gwamnan da idan ka je jiharsa za a iya ce ma ka ya yi aiki sosai, to amma da za ka bincika ka ji yadda a ke tsula kudi a cikin kwangilar da ya ke bayarwa, kai ka san cewa, don ba dukiyarsa ba ce. Idan dukiyarsa ce, babu yadda za a yi abinda za a iya kashe Naira biyu a ce ma sa za a yi ma sa kwangilar a kan Naira 10 ya yarda. Ko kusa!

Haka nan kuma da za ka bincika ka ji irin dukiyar da wannan mai mukamin ya mallaka a dalilin hawansa mulki, kai ka san cewa, babu yadda za a yi ya mallake tat a hanyar albashinsa ko alawus-alawus dinshi.

Abin misali shi ne, akwai wani gwamna wanda bai jima da barin mulkin jiharsa ba a arewacin Nijeriya, ya mallaki rukunin gidaje da dama a babban birnin tarayya Abuja bayan hawansa mulki. Shin ina ya samu wannan kudin? Babban abin takaici shi ne, ya na cikin irin gwamnonin da a ke kallo a matsayin sun tabuka wani abin arziki a lokacin da su ke mulkin jihohinsu.

Tabbas irin wannan babu inda zai kai mu, domin an wuce irin wannan wajen a kasashen da su ke kokarin cigaba ko su ke tasowa.

Komai sai ka yi daidaito a cikinsa. Ita barna daga karama ta ke zama babba. Ba a raina ta kwata-kwata! A inda a ka cigaba, ’yar kankanuwar ayar tambaya a kan shugaba ta na iya sanyawa ya rasa mukaminsa ko dai shi da kansa ya sauka ko kuma a tilasta shi ta hanyar tsigewa.

Wani zai iya cewa, ai har yanzu ba mu cigaba irinsu ba. To, su ma sun saka wannan akidar a ransu ne tun kafin su samu cigaban. Don haka ne ma su ka cigaban. Idan mu ka cigaba da nanata cewa, har yanzu rainon dimukradiyya mu ke yi, to ba za mu taba wuce irin wadannan guraren ba, alhali an riga an yi ma na nisa.

Akwai kasashen da ba su wuce tsaranmu ba, amma su ma sun riga sun yi ma na nisa kamar irin su Indunisiya, Malesiya da sauransu. Dole ne sai mun tsefe idanunmu mun gaya wa junanmu gaskiya mun ja hankalin shugabanmu a kan su rika yin abinda ya dace, sannan za mu mike mu samu cigaba. Bai dace a ce har yanzu mu cigaba da bari a na yi ma na nisa ba. Tilas mu sa idanu kan shugabannin kananan hukumomionmu, gwamnoninmu, shugaban kasa da sauran duk masu rike da mukamai, wadanda ba zababbu ba, kamar ministoci, kwamishinoni da makamantansu, domin AN YI MA NA MA NA NISA!!!

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here