Mutum Da Sana’arsa: Hira Da Malam Musa Mai Kayan Miya

25

Hausawa na cewa, a san mutum, a san sana’arsa. Wannan wata tattaunawa ce da MALAM MUSA ABDULLAHI mai kayan miya ya yi da MUHAMMAD USMAN SHABA, a cikin hirar, ya bayyana irin sirrukan da ke cikin sana’arsa ta kayan miya. Ga yadda hirar ta kasance:

Baba ko za ka sanar da masu karatu sunan ka?

Alhamdulillahi suna na Mallam Musa Abdullahi ni dai mutumin jihar jigawa ne ni birnin kudu a Yelwa gwamnatin gida chibi na yake.

 

Shekarun ka nawa?

To fa! maganan Shekarun ne dai sai a hankali na manta gaskiya, ba zan iya tuna wa ba amma na san lokacin na shiga kaduna, na shiga kaduna ne bayan murtala ya rasu da shekaru biyu, kuma har yanzu da nake magana da kai iyalai na suna kaduna a Rigasa kusa da sabon titin jirgin kasa dake Rigasa Kaduna, ana nan dai na shigo Abuja a 1999.

 

Lokacin da ka ke Kaduna wace sana’ar ka ke yi?

Sana’ar saida jaridu. Nakan kai wa kamfanoni ne kullum aikin kenan, daga wannan kamfanin zuwa wani kamfanin kuma kar kace jaridar ta kamfani daya kawai, ba na kamfani daya ba ne, duk jaridun da ka sani nake saidawa.

 

To Mallam Musa ya maganan makaranta?

Alhamdulillahi ni dai na sauke Kur’ani tun ina dan karamina, amma ban je boko ba, gaskiya na boko kuma a kan titi na tsintsince su har ma nakan dan karanta jaridu da kuma rubuta wa, ba wai dai sosai ba, gaskiya ina da-na-sanin rashin yin karatun bokon, saboda ina ganin lokaci ya wuce ni yanzu gaskiya.

 

A wancan  lokacin mene ne ya hana ka yin karatun bokon?

Gaskiya bamu dauke shi da muhimmanci ba, iyayenmu ma gudu wa damu suke ta yi don su boye mu, idan ana jin kunyan iyayenka kuma to sai a barka ba sai ka gudu ba, ko an buye ka ba. Ka ga dai jan mu ake a wannan lokacin, amma mu ki yi. Karatun kyauta fa, ba yanzu da karatu ya zama na kudi ba, iyayen mu na tunanin cewa yahudanci ne, su kawai basu yadda da shi ba.

 

Ka ce ka shigo Abuja a shekara ta 1999, da ka shigo Abuja ka ci gaba da saida jaridu ne?

Da na shigo Abuja gaskiya ban sa saida jaridu a zuciya na ba, ba da niryar saida jaridu na zo ba, saboda ka ga ba zan iya yawo kamar da ba, abin da nasa a rai na shi ne saida kayan miya kuma ka gansu tun daga wannan lokacin har zuwa yau su na dogara, da shi na dogara da Allah na dogara.

 

Nan ne farkon wurin da ka fara wannan kasuwanci?

A’a, ba nan ba ne waje na farko da na fara zaunawa. Na fara ne a kasuwar Wuse, aka zo aka tashe mu a ‘yan tumatur dake Kasuwar Wusen, sannan muka koma sabuwar kasuwar wuse, wato ‘New market’ can ma aka rusa, sai na bar nan na koma barikin ‘yan sanda na dan kai wani lokaci sai Allah ya kawo ni nan wurin, shi ne kenan na ke zaune har zuwa yau.

 

Shekarunka nawa kenan da zama a nan?

Shekaruna 10 zuwa 11, ka ga daga Wuse zuwa sabuwar kasuwar wuse dake Abuja har zuwa barikin ‘yan sandan na yi Shekaru bakwai da watanni, ban dai karasa Takwas ba, duka kuma sayar da kayan miya nake ta yi. Ka san komai na da sanadi ko? Kamar zuwa na Kaduna sanadiyyar wani aboki na ne yasa na zauna a Kaduna a takaice  dai iyali na ma su na Kaduna har yanzu da nake magana da kai. Na fara zau nawa a Tudun Nufawa layin ‘yan kwakwa, shi abokina dan Kano ne a Rano, kuma ta nan mahaifiya ta tafito daga nan na koma abakwa da zama da yara na guda hudu biyu maza biyu mata sai dai Allah ya yi wa daya daga cikinsu rasuwa magon da ya gabata, har ta gama sakandare. Babban yarsu kuma ta yi aure, yanzu amma ita a gidan mijinta ta gama sakandare.

Amma yanzu a Rigasa nake zaune shekara bakwai a nan Rigasa sai dai fatana shi ne na gina nawa gidan amma ba a Rigasa ba, ka ga dai ina da fili anan rigasan amma zaman gurin bai yi min ba.

Mene ne ya sa ka ce Rigasa bata yi maka ba?

Kawai dai bata kwanta min ba ne kawai, gidan da nake ciki ma ba wai biya nake yi ba, amma Unguwan ne bana so, kuma ka ga yau da kullun sai Allah ko ba haka ba? Shi ya sa ni dai fatana nima na samu nawa, kuma Insha Allah nan ba da dade wa ba, da ikon Allah zan mallaki nawa.

 

To wane shawara zaka ba wa gwamnati kan matasa?

Shawara ta Ga gwamnatin kasar nan shine su ji tsoron Allah cewa wataran zasu mutu saboda haka su tsaya suyi hadalci susan da cewa duk abubuwan da sukayi sai Allah ya tanbaye su daya bayan daya susan cewa kowa na da hakki akan su ata dabban da ke cikin daji ya na hakki a kan su bale dan adam, susani shugabanci ba wasa bane ko gwamnatin gida ne ba karamin abu ba ne saboda an bashi aiki ne ba kadan ba balantana shugabancin kasa gabaki daya. Ni dai su duba suyi hadalci bawai sai wani da wani ba. Su kuma matasa shawaran da zan ba su shine da farko dai duk inda mutun ya tsinci kan shi yayi kokari ya nami illimi da boko da kuma islamiya dan Allah su sa ido su karatu iyaa karfin sa sannan ya nemi sana’ar da za dogara da kan sa ba sai ya jira gwamnati ba domin shi aikin gwamnati ba wai lalle kowa sai ya samu ba babu inda haka ce wai dole idan kagama karatu gwamnati za ta baka aiki babu saboda haka mu kama sana’ar hannu mu kuma rike shi da mahim manci. Lallai matasa su tashi suje su nemi illimi islamiya da na bokon. Idan aikin gwamnati tasamu to falillahil hamdu, idan ma batasamu ba kasan dai inda ka dogara ba wai da gwamnati ba, ka tashi ku naimi naku kawai.

 

Yanzu nawa ne kwandon tumatur na roban nan?

Kwandon roba ina saida wa Naira 1,000 kashi kuma akoi na Naira 200 Naira 100 har na Naira 50  wani lokacin ma ko nawa ka zo dashi zan baka saboda ban san halin da ka ke ciki ba.

 

Wanne kalubale ka ke fuskanta a nan?

Alhamdulillahi ba a nan kawai ba duk inda na zauna babu wanke zuwa ya da me ni gaskiya idan ba dai wurin sana’a ta na wuse wda aka rusa a wannan lokacin ba na gode Allah.

 

Ya zancen riba a sana’ar Kayan Miya?

Akwai riba mana, tunda har ina ciyar da iyalina a wannan sana’ar, sai dai godiyan Allah.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here