Nijeriya Za Ta Fafata Da Kasar Ingila A Wasan Sada Zumunci

192
during the 2019 Africa Cup of Nations Qualifying match between Nigeria and South Africa at Godswill Akpabio International Stadium on June 10, 2017 in Uyo State, Nigeria. Photo by Kabiru Abubakar

Daga Abba Ibrahim Wada

Babban sakataren hukumar kwallon kafa ta kasa Alhaji Muhammad Sunusi ya tabbatar da cewa Nijeriya da kasar ingila sun amince da buga wani wasan sada zumunta a watan Yuni na shekara mai zuwa domin shirye shiryen fara gasar cin kofin duniya da za’ayi a kasar Rasha a shekara mai zuwa.

Alhaji Muhammad Sunisi yace tuni hukumomin kwallon kafa ta kasashen biyu suka gama shiryawa donmin tabbatar da anyi wannan wasa abinda yarage kawai shine filin wasan da za’a fafata wasan da kuma rana da lokaci.

Yaci gaba da cewa dalilin hada wasan shine domin yan wasan na super eagles su buga wasanni da kwararrun kasashe domin gwada kwarewar yan wasan kasar da kuma shiryawa sosai a gasar.

Nijeriya dai da kasar Ingila sun taba buga wasan sada zumunta a shekarar 1995 a filin wasa na Wembley wasan da akaci Nijeriya daci 1-0 ta hannun dan wasa Dabid Platt.

Sannan kasashen sun sake haduwa a gasar cin kofin duniya a shekara ta 2002 a kasashen Korea da Japan wasanda akatashi kowacce kungiya tana nema.

A karshe Muhammad Sunusi yace super eagles din kuma za ta buga wani wasan na sada zumunci a nan gida Najeria Abuja da wata kasar domin yiwa gwamnati da magoya bayan kasar godiya bisa irin goyon bayan da tawagar super eagles din take samu kafin su tafi kasar Rasha.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here