RAHOTON MUSAMMAN: Abubuwan Da Na Gani A Hedikwatar Tsohuwar Kasar Biyafara

496

Daga Alhaji Hassan Dandy

Da ya ke na sha zuwa yankin Inyamurai, musamman hedikwatar tsohuwar kasar Biyafara,  wato Umuahia, amma dai garin ya fi ban sha’awa ne da adon kyale – kyale, da annashuwar bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekarar Miladiyya. Daga ‘City Center’ ka na iya ganin al’ummar cikin annashuwa, kaman ba a daidai wannan dandali ba ne shekaru 47 da su ka wuce, a can kusa da karshen layi ‘Junction’ da ya hade da titin ‘Aba’ wani matashin sojan Nijeriya mai suna Manjo Ibrahim Babangida, sanye da kayan yakin Nijeriya cikin Motar yaki mai sulke da a ke kira ‘Anti-tank Bazooka’  bisa kariyar  hafsoshin atilare fululu, su ka rutsa da birnin Umuahia da Arochukwu, wanda ya yi sanadiyyar faduwar sabuwar gwamnatin Biafrah, ta Odumegwu Ojukwu.

Takanas na niki gari a ziyarar da na kai kasar Ghana, har birnin Aburi, na je hedikwatar Soji inda a ka yi zaman karshe wanda ya tashi baran – baran tsakanin Shugaban kasa Matashi Janaral Yakubu Gowon, da tsohon Gwamnan Kudu maso gabas Birigediya Odumegwu Ojukwu, wanda ya ayyana warewar ilahirin yankin daga Nijeriya, matakin da ya sabbaba kazamin yakin wata 30 cur, asarar rayuka sama da dubu 150, da kuma bacewar mutane  bat har gobe sama da mutum miliyan 2, ‘yan gudun hijira sakamakon yakin sama da mutum miliyan biyar, ba a batun wadanda yunwa, namun daji, cututtukan sakamakon yaki ya yi sanadiyyar halakarsu.

Ko da ya ke na sha zuwa Umuahia, amma dai lallai ba na gajiya da ziyartar  ‘War Museum’ da ‘Ojukwu Bunker’ wato fadar Ojukwu wacce ta ke gidan kasa, a garin na Umuahia. A ranakun bukukuwa irin wadannan lallai duk wuraren cike su ke da maziyarta, wadanda ‘Curators’ ke ta faman yi ma bayanin irin abubuwan da su ka faru a lokacin yakin, da irin kayan fadan da a ka yi amfani da su lokacin yakin.

Za ka sha mamaki matuka idan ka shiga fadar Ojukwu ta gidan kasan nan, ka ga yadda a kayi hikima wurin tsara gidan da dakunan kwana; dakunan cin abinci, gidan rediyon (da ya ke watsa shirye – shiryen farfaganda na yaki duk ilahirin yankin na Biyafaran), dakunan fursunoni, dakunan girke – girken abinci, dakunan ajiyar kaya da sif – sif na ajiyar kudi da sauransu duk a karkashin kasa, wato idan a ce mutum shi kadai ne, zai yi wuya ko da masu kula da wannan waje, ya yadda ya iya shigar maka wannan waje shi kadai, amma a haka Ojukwu ya zauna a wannan waje, ya dinga jagorantar yakin wata da watanni, ya yi ta tarurruka da manyan kwamandojinsa, da kulle kullen yaki kala – kala.

A wannan wuri irin wannan rana tilas mutum bahaushe irina ya yi badda bami, domin gane kai bahaushe ne a irin wannan wuri, musamman cikin ‘Museum’ da ya ke cike da Inyamurai maziyarta, lallai ka iya jawowa mutum matsala. Za ka ga a na bayanin yakin, da ya ke wasu a na maganar sanannun iyayensu da kakanni da a ka kashe, manya da yara na ta sharar hawaye, a na la’antar Hausawan Arewa, da Yarbawa (munafukai a wajensu).

A Umuahia ‘City centre’, za ka iya ganin inda shekaru 49 da su ka wuce (June 1967) samari majiya karfi ‘yan kabilar Igbo su ka dinga cudadowa su na ba da sunansu a sabuwar hedikwatar kasar Biyafara don ‘yanto kansu daga Hausawa ( ci – ma banza).

A cikin littafin “The Cyclist” a wannan wurin ne kyakkyawar amarya ‘Celina’ ta yi bankwana da angonta, ta karfafeshi da tafiya yaki “Ka tafi ka yi yaki da sunan Koko Obiama. Ina nan zan jira ka ko yaushe, zaman mu cikin ‘yanci ya fiye mana mu da ‘ya’yayen da zamu haifa, fiye da zaman kangin bauta”.

Iyaye na kuka ‘ya ‘ya na kuka a wannan dandali za a yi rabuwar karshe, a kai sababbin sojoji sansanonin horon gaggawa, na ‘yan kwanaki kafin a kwashe su zuwa fagen fama, wasu kuma daga nan sai a Darussalamu.

A ‘Situation room’ din nan da na shiga ne, Ojukwu ya fara bawa Njoku da Laftanar Kanar Chukwuma Nzeogwu (wanda ya jagoranci kashe Sardauna) umarnin kare yankin arewacin Biyafara, don an samu rahoton sirri ‘Intelligence report’ cewa sojan Nijeriya ta nan za su fara kai hari. Haka kuwa a ka yi, a watan Yulin 1967 gwamnatin Nijeriya karkashin Shugabancin Janar Gowon ta tura kwamandan Hafsoshin farko na Nijeriya (NA 1 Dibision) Kanar Muhammadu Shuwa, ya fara kaddamar da hari ta Nsukka da nufin kama Enugu. Shuwa, da Timothy Shelfidi da Kanar Obasanjo sun yi nasarar shiga har Enugu, amma Njoku da Nzeogwu su ka fatattako su.

Daga nan ne fa Nijeriya ta nada wasu kwamandojin Murtala Muhammad da Shehu ‘Yar’aduwa daga bangaren Asaba da nufin tunkarar Onitsha, Nnewi da Aba. Sai Benjamin Adekunle da nufin kama yankin Delta tun daga Fatakwal, Warri, Sapele da Ughelli. Sai Alani Akinrinade daga bangaren  Opobo, wanda zai yi fafutukar kama Obudu, Kalaba da Uyo

Hakikanin gaskiya duk a wadannan kwamandoji babu wanda a ka hadawa tarban musifa tsagwaronta irin Murtala da Yar’aduwa, domin su ne a ka bawa aikin tunkarar ainihin Inyamuran ta tsakiyarsu, wato idan su ka yi nasarar kama Anambra, daga nan sai su yi kokarin kama Owerrin Imo, sai su shimfida hedikwata ‘Umuahia’ daga bangaren Ojukwu kuma ya na da Kanar Joseph Achuzia (Murtalan Inyamurai) ya tunkare su.

Sannan tunda gumurzu ya yi gumurzu sai Ojukwu ya ce ba zai yiwu mu zauna kawai da aikin kare kai ba, muma dole ne mu kaiwa makiya hari har gidansu da nufin kame nasu garuruwan su ma.

Amurka, Rasha, Misrah da Ingila na taimakon Nijeriya. Su kuma Faransa, Spain da Afrika ta kudu, da Gabon na taimakon Biyafara, haka a ka ci gaba ta gwabza yaki, a wancan lokaci dai Ojukwu ya tura kwararren masanin yaki Kanar Banjo ya kai hari ta bangaren ‘Midwest’ tun daga Benin a kan ya yi iya iyawarsa ya fada kasar Yarbawa ya kama Legas.

Lokacin da Banjo ya isa garin Agbor da tawagar mayaka dubu 7,000 sai ya tura Laftanar Alakhija zuwa Benin, Manjo Humphrey zuwa Warri, sai Laftanar Kanarl Mike Inbenso zuwa Auchi. Inbenso, yayi nasarar kama Auchi har ya shiga Okene, ya yayyanka hausawan Garin, kuma umarnin da a ka ba shi idan ya gama da Auchi ya bi ta Idah ya nufi Nsukka ya bullowa tawagar Mamman Shuwa ta baya.

Shi kuma Manjo Humphrey ya shiga Warri, ya yi nasarar kama ta, (duk da dai gwamnan Nijeriya na lokacin Dabid Ejoor ya gudu) amma dai shi ma haka ya zauna ya jira umarnin gaba na dumfarar Fatakwal. Shi ma dai Alakhija ya shiga Benin, ya kama Benin, har ya sanar da Banjo. Banjo din ya baro Agbor ya samu tawagar Alakhija, ya ce da su su shirya dumfarar Legas hedikwatar Nijeriya, to sai Ojukwu ya aiko ka da su tafi, a ka rinka samun cece ku-cen umarni tsakanin Bonjo da Ojukwu a kan su sai sun wuce, har tsawon sati uku, ba su yi komi ba, karshe dai Banjo ya yi kunnen uwar shegu da Ojukwu ya nausa Ikko da tawagarsa.

Wannan tsaikon da a ka samu ya taimaki Sojojin Nijeriya sun kara shiri da kara karfi a yankunan da aka sassamu matsala. Banjo ya yi tawo mu gama da tawagar Murtala wanda ya dumfaro

masu ta Arewa daga Ore ya yi biji biji da su, a ka kashe da dama, tilas su ka yo baya, su ka yi ta gudu su na farfasa gadojin hanya, har Garin Asaba.

A Asaba ne a ka umarci Murtala ya dakata a kara karfi sosai kafin ya tsallaka gada ya shiga Onitsha. Har yau ina iya tunawa a darussan mu (dayake Malamin mu Inyamuri ne, ya na bamu darasi ya na kuka), cewa a Asaba a lokacin Murtala ya kashe musu matasa sama da 800, kaman ramuwar gayyar abin da a ka yi a Okene.

Sau biyu Murtala shi ma ya na kin bin umarnin Shugaba Gowon ya na tsallakawa Onitsha, su na koro shi, har dai a zuwa na uku ya yi nasarar kama Onitsha. Yawwa na manta, a dawowar su Banjo shigowarsu Benin sojojinsa cikin yunwa su ka aukawa farar hulan Benin da kwace har da yi wa mata fyade Gida Gida, lokacin da labari ya watsu, Masarautar Benin ta bada sanarwar duk ilahirin Benin Emphire babu ruwansu da Biyafara, su na tare da Nijeriya.

Wannan ya saukakawa lokacin da Adekunle da tawagarsa su ka biyo ta ruwa, su ka shigo su ka kame Warri, Saphele da Ughelli cikin sauki, can kuma an yi sa’a Akinrinade ya kama Kalabar da Uyo, kenan an mayar da Biafra sai su isu zallah Inyamurai.

Bayan Murtala ya yi nasarar kama Onitsha, sai Joseph Achuzia, ya ja da baya zuwa Nnewi (Garin su Ojukwu), su kuma su Murtala su ka yi nasarar samun tulin makaman da Sojojin Biyafaran su ka gudu su ka bari, to ashe komawar su Nnewi karfi su ka kara hadawa.

Haka a ka yi kuwa cikin dare su ka aukowa su Murtala a Garin Abagana, su ka kone motocin yaki 19, su ka kashe sojoji sama da 150 rana daya, duk sojojin Nijeriya su ka yi ta gudu. Inyamuran, su ka yi sauri su ka fasa gadar Niger (wacce a ke cewa gadar Murtala ta wajen Garin Onitsha) da nufin sai sun kama Murtala hannu da hannu. Har hazar yau a na mamakin yadda Murtala ya tsira daga harin Abagana da ransa, a na cewa ruwan Onitsha ya fada ya yini iyo ya tsallake gaba, Allahu aalam.

Gwamnatin Nijeriya ta fusata da rashin aiki da umarni na Murtala duk da dimbin nasarar da ya samu, sai ta tura shi Ingila, a wani matakin soji da a ke kira Awol, kafin daga bisani su ka dawo da shi. Jarumtar da Achuzia ya nuna ta sanya Ojukwu ya tura shi Warri inda a ke kazamin fada da Sojojin Nijeriya karkashin Adekunle Benjamin, nan ma dai da tawagar su ta kare dole ya dawo Owerri su ka kara karfi da nufin hana sojojin Nijeriya tsallakawa Umuahia, hedikwatarsu.

A wannan lokacin ne Gwamnatin Nijeriya ta nada Olusegun Obasanjo babban kwamandan yakinta. A hannunsa Enugu ta fadi, Onitsha ta fadi, Nnewi ta fadi. Saura Owerri, Aba, Abakaliki da Umuahia. An gwabza kazamin yaki da mutanen Joseph Achuzia a Owerri, tare da gamayyar sauran kwamandojin Nijeriya da su ka kakkama wurare, ganin su na hada karfi ne Achuzia ya fasa gadojin hanyar Owerri – Fatakwal da hanyar Aba – Umuahia.

A watan Mayun 1969, tawagar Murtala ta kama Oguta, Ojukwu ya umarci Omerua da Achuzia lallai su fita su kwato garin ganin muhimmancinsa wajen shigo da kayan yaki da abinci, duk dai Murtalan ya kora su tilas su ka koma Owerri.

Da dare babban kwamanda Obasanjo ya bada umarnin sojoji dubu 15,000 su ka zagaye Owerri, a ka gwabza kazamin fada, sama da kashi 30 na garin su ka gurgudu har da sojojin Biyafaran, Jarumin soja Laftanar Kanar Joseph Achuzia ya ce babu inda zai gudu, wannan ta sa Olusegun Obasanjo ya kama shi hannu da hannu.

Jin labarin kama Achuzia ya karya sauran sojojin da su ke yaki a bangaren Biyafara. Ojukwu ya samu labari, ya wuce Uli Airstrip, ya mikawa  Phillip Effiong ragamar mulkin Biyafarah shi kuma ya arce zuwa Kwatdibuwa. Kashegarin guduwarsa ne Matashin Soja Major Babangida, ya shiga Umuahia ta Aba ya kama garin, ya wuce ya kama filin Jirgin saman Uli (kenan kadan ya kuskure, da shi ne zai kama Ojukwu).

A ranar ne kuma Philliph Effiong ya fito daga gidan Gwamnati ya bada sanarwar janyewar Biyafara daga yakin, da hadewar yankin cikin Nijeriya.

Umuahia zuciyar Igbo zamu tafi sai watarana…

Hassan Dandy manazarci ne na musamman.

A na iya tuntubarsa a wannan lambar, 08032809899

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here