Shelar Kano: Ko Yau Aka Yi Zabe, Sai Na Lashe –Buhari

746

Daga Sulaiman Bala Idris

Jiya a yayin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ga ayarin jama’ar da suka tarbe shi a Birnin Kano, Shugaban ya ce lamarin ya tsima shi, ‘Daga wannan abin da na gani yau, ko a yau aka shirya zabe sai na lashe.’

Miliyoyin al’ummar Kano da magoya bayan jam’iyyar APC ne suka yi dango a titunan jihar don tarbar ziyarar yini biyu da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fara gudanarwa.

Tawagar Shugaban Buhari ta sauka a Birnin Kano ne da misalign karfe 10:27 na safiyar Talata a Tashar Jirgin Sama na Malam Aminu Kano.

Shugaban wanda ya samu tarba ta musamman daga Kanawan, sun yi ta rera taken ‘Sai Baba’ a duk wuraren da tawagar tasa ta bi. Shugaban ya yi ado da fararen kaya, wanda kuma tawagar tasa ta bi ta unguwar Asthon, zuwa Sani Marshal inda suka ci karo da dandazon al’umma a titin Murtala Muhammad.

dandazon al’ummar sun fito ne rike da kwalaye wadanda aka rubutu sakonnin maraba da zuwan Buhari Kano. Wasu kuma daga cikinsu na rera wakokin yabo da irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu a tsawon shekarun da ta kwashe a ofis.

Daga cikin jawaban da ya gabatar, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa kafin zuwan gwamnatinsa, al’amuran kasuwanci sun tsaya cak a Kano, an samu salwantar rayuka da dukiya marasa adadi saboda hare-haren ‘yan ta’adda. Ya ce; “Amma a yau, komi na tafiya lafiya, babu wata fargaba ballantana tashin hankali. Sakamakon karya lagon ayyukan ‘yan ta’adda da gwamnatinsa ta yi.” In ji shi

Haka nan kuma Buhari ya ce, daga cikin alkawurran da jam’iyyarsu ta APC ta yi akwai samar da ingantaccen yanayi na kiwon lafiya, inda ya ce tuni sun cika wannan alkawari da suka dauka.

Duk dai a jiya, Shugaban ya ziyarci fadar Mai Martaba Sarkin Kano, wanda kuma a yayin a ziyarar ya ce sun biyo ta fada ne domin mika gaisuwar ban girma ga masarautar Kano, domin irin kima da darajar da masarautu suke da shi. Ya yi godiya ga Sarki Sanusi II dangane da irin tarbar da aka yi musu.

Daga fada ne kuma Shugaban ya nufi Gidan Yarin Kurmawa, inda a can ya ‘yanta fursuna har mutum 500.

A na sa ran a wannan ziyarar ta yini biyu, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da jerin ayyuka Kaman haka; Asibitin Kwararru na Muhammadu Buhari, Asibitin Yara Na Unguwar Zoo, Gadar Kasa Ta Panshekara zuwa Madobi, Hanyar Jerin Gidajen CBN, sannan kuma zai duba wani aikin a Gadar Kasa ta Barikin Bukabu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here