Shugaban NNPC Zai Dawo Don Kawo Karshen Matsalar Mai

195

Daga Bello Hamza

Shugaban kamfani samar da Mai na kasa,( NNPC), Maikanti Kacalla Baru,  zai yanke tafyar da ya yi zuwa Landan, ya dawo kasar nan domin ganin yadda za a shawo kan matsalar karancin man ta ake neman haddasa a wannan kasa

Mista Baru, wanda ya tafi bias gayyatar da aka yi masa ta karramawar da  za a yi masa ta Forbes Oil & Gas Man na shekarao 2017a kasar Turai ya dawo gida don ya fuskanci wannan kalubale na karacin Mai

Da yajke jawabi kafin tasowarsa  Mista Baru ya shwarci ‘yan nijeriya da su guji mummunan halin son yin arzikin dare daya ta hanyar amfani da wani lokaci domin takura wa jama’a. saboda sai ya tabbatarwa da ‘yan nijeriya cewa, zai dawo kasar nan daga tafiyar da yay i ba don y agama ba, sai dai saboda ya dawo a samu hanyar warware wannan matsala da muka afkar da ita da gangan.

Haka kuma ya ce, kamfanin main a NNPC ya yi tanajin wadataccen man da za a dade ana amfani da shi, ko da kuwa an dakatar da hakar man na wani lokaci,

Kafin tafiyarsa shugaban kamfanin na NNPC ya bayar da umarnin a wadata ko’ina da mai yadda ba za a samu matsala ba musamman lokacin bukukuwan kirsimeti, wanda alokutan baya aka saba samun matsala.

Tun farko a nasa jawabin shugaban kamfanin na NNPC ya bayyana cewa babu wani shiri na kara farashin man. Saboda haka ya ce, farashin nanan dai da aka sani tun farko shi ne zai ci gaba da aiki.

Saboda haka ya ce, domin ganin ba a samu matsala ba kamfanin na NNPC ya samar da wadataccen mai ga ‘yan kasuwa, watau kamfanin sayar da mai na PPMC, da  NNPC masu sayar da mai  duk dai domin a tabbatar da cewa, ba a ci karo da matsala ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here