Watakila Chelsea Ta Hadu Da Barcelona Ko PSG

70
LONDON, ENGLAND - SEPTEMBER 12: Players of Chelsea celebrate after scoring during the UEFA Champions League Group C match between Chelsea FC and Qarabag FK at Stamford Bridge on September 12, 2017 in London, United Kingdom. (Photo by DeFodi/Anadolu Agency/Getty Images)

Daga Abba Ibrahim Wada

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea na fuskantar yuwuwar haduwa da kungiyar Barcelona ko Paris St-Germain a wasansu na gaba na kungiyoyi 16 na gasar zakarun Turai bayan da suka tashi 1-1 da Atletico Madrid, wanda hakan yasa Chelsea ta rasa damar zama na daya a rukunin nasu da Roma tayi na daya.

A yanayin yadda sauran wasannin suka kasance kungiyar Besiktas ta Turkiyya ita kadai ce bayan bayan Barcelona da Atletico Madrid, za a hada Chelsean da ita a matakin na gaba na kwab daya.

Chelsea ce ta mamaye wasan har zuwa lokacin da Saul Niguez ya faki dan bayanta Tiemoue Bakayoko, ya zura musu kwallo da ka, bayan da Fernando Torres ya cillo masa ita a minti na 56.

Chelsea ta kara matsa lamba ba kakkautawa yayin da lokaci ke kurewa, har ta yi sa’a Stefan Sabic ya ci kansu da kwallon da Eden Hazard ya dauko.

To sai dai Roma a gidanta ta doke Karabag, kuma Chelsean ta kasa kara cin ta biyu, ta samu nasarar da za ta sa ta sake zama ta daya a rukuninsu na uku.

Spartak Moscow ko Sebilla wata daga cikinsu ma za ta iya zama wadda za a hada su da Chelsean idan wasan ranar Laraba ya sauya matsayin kungiyoyin rukuni na biyar inda Liberpool take ta daya.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here