Westham Da Sporting Lisbon Sun Sasanta A Tsakaninsu

30

Daga Abba Ibrahim Wada

Kungiyar kwallon kafa ta West Ham ta ce rikicin da aka samu tsakaninta da kungiyar Sporting Lisbon ta kasar Portugal akan dan wasan da suke son zawarci a lokacin kasuwar saye da sayar da ‘yan wasan data gabata wato William Carbalho na Portugal ya faru ne saboda matsalar sadarwa kuma an sansanta ta matsalar.

A kwanakin baya dai kungiyar ta Sporting ta ce za ta kai karar kungiyar West Ham gaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, saboda zawarcin dan wasan nata na tsakiya mai shekara 25, ba bisa ka’ida ba.

A wata sanarwa da kungiyar ta West Ham ta fitar a shafinta na twitter ta ce kungiyoyin biyu za su dawo su ci gaba da dangantakarsu kamar yadda sukeyi a baya.

A watan Satumba West Ham ta ce ta nemi sayen dan wasan na Portugal har ma ta fitar da wasu wasiku na e-mail da take ikirarin cewa ta yi zawarcin dan wasan bisa ka’ida.

Amma kuma darektan sadarwa na Sporting Lisbon din Nuno Saraiba ya kalubalanci ingancin wasikun da e-mail da aka yi satar fitarwa, wadanda suka nuna tayin euro miliyan 25 da aka yi a kan dan wasan.

Darektan ya kuma nuna bayyana Sulliban a matsayin makaryaci kuma cimazaune a wani sako da ya sanya a shafinsa na Facebook.

A lokacin West Ham ta karyata maganganun har ma tana barazanar daukar matakin shari’a akan lamarin wanda ta bayyana abin takaici da rainin hankali.

Sai dai duka bayan wannan musayar kalamai a ranar Talatar nan kungiyar ta firimiya ta fitar da wata sanarwa, wadda a ciki take cewa, an samu wannan rashin fahimta ne saboda matsalar sadarwa tsakanin wakilan kungiyoyin biyu, a kan batun zawarcin dan wasan na Sporting, William Carbalho.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here