Ziyarar Jaje Adamawa: Osinbajo Ya Taras Al’ummar Kauyen Kiyan Sun Yi Hijira

211

Daga Umar A Hunkuyi

A ranar Talatan nan ne Mataimakin Shugaban kasa,Yemi Osinbajo, ya kai ziyara ga kauyakun da rikicin kabilanci ya rutsa da su a Jihar Adamawa, wanda ya yi sanadiyyar kashe mutane da yawa da kuma lalata dukiyoyi.

Daga cikin kauyakun da Mataimakin Shugaban kasar ya ziyarta, sun hada da Numan da kuma Dong, lamarin da ya fi baiwa Mataimakin Shugaban kasar da tawagarsa mamaki shi ne, yaddasuka taras da garin Kikan ya zama Kufai, wayam ba bu kowa a cikinsa.

Kasantuwar manufar ziyarar shi ne, yin ta’aziyya ga wadanda lamarin ya shafa, da kuma ba su tabbacin aniyar Gwamnati na samar masu da tsaron da ya kamata domin hana aukuwar hakan a nan gaba, sai tawagar Mataimakin Shugaban kasar ta nemi da Shuwagabannin al’ummomin yankin su hanzarta zuwa a tattauna da su a dan wani gajeren lokaci nan gaba.

A duk inda Mataimakin Shugaban kasar ya ziyarta, yakan nanata kira ne ga Shugabannin al’ummomin wajen, da su kirayi Jama’arsu a kan zaman lafiya da gudun tashin-tashina, da kuma mayar da hankali a kan dukkanin abin da zai iya kawo masu bunkasa da ci gaba mai ma’ana.

Rigingimun dai, sun lakume rayuka da yawa, tare da raunata mutane da dama, baya ga dimbin gidaje da dukiyoyin da aka lalata a dukkanin kauyakun.

Mataimakin Shugaban kasar da ya kai ziyara a madadin Shugaba Buhari, ya kirayi al’ummomin yankunan kamar haka, “A daidai wannan lokacin, babban abin da ya fi mahimmanci a gare mu shi ne, mu hadahannu wajen ganin mun wadata kanmu da abin da za mu ci, wurin zaman da ya dace da kuma samarwa al’ummomin mu hanyoyin more rayuwa, wannan shi ne abu na farko da ya kamata ya kasance a gabanmu.

Wannan lokaci ne da ya kamata mu hada kai, domin mu sami ci gaba. Ba bu wani dalilin da zai sanya mu yi ta kashe kawukanmu, muna lalata dukiyoyinmu ta hanyar yakan junanmu. Ya kamata ne mu kasance masu baiwa junanmu tsaro, mu kuma bi duk hanyoyin da suka dace wajen samarwa da al’ummominmu ababen more rayuwa, ta yanda kowa zai ji dadin rayuwarsa a wannan kasa ta mu.

“Ba bu fa wanda zai ci wata riba da kashe-kashen nan a tsakaninmu, duk wani da zai iya yin kisa, ko ya sanya a yi kisan, to ba Shugaba ne ba. Shugaba shi ne wanda zai jagoranci al’ummarsa ta hanyar hadin kai da kuma ci gaba. A matsayinmu na Shugabanni, tilas ne mu lalubo duk hanyar da za ta kawo ci gaba wa al’ummominmu, irin kuma wannan ci gaban ne muke bukata a daidai wannan lokacin a wannan kasa ta mu.”

Daga nan sai Mataimakin Shugaban kasan, ya yi wa wadanda lamarin ya shafa ta’aziyya amadadin Shugaba Buhari, ya kuma tabbatar masu da cewa, Gwamnatin Tarayya za ta yi duk abin da ya dace, domin warware wannan rigimar, sannan kuma Gwamnati za ta tabbatar da an cafko wadanda suka aikata wannan aika-aikar domin tabbatar da an hukunta su kamar yadda doka ta tanada.

“Wannan mummunan abin bakin ciki ne, na kuma zo nan ne a madadin Shugaba Buhari, domin na jajanta maku, tare da al’ummar Jihar Adamawa baki daya. Ina jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu, da wadanda suka rasa muhallansu da dukiyoyinsu da ma wadanda suka rasa wasu hanyoyi na neman abincinsu. Mun zo nan ne domin lalubo hanyar da za ta warware wannan rikici baki daya,” in ji Osinbajo.

Mataimakin Shugaban kasar, ya sami tarba daga Gwamnan Jihar ta Adamawa, Jubrilla Bindawo. A kuma lokacin ziyarar, Mataimakin Shugaban kasar ya sami damar ganawa da Lamidon Adamawa, Dakta Barkindo Aliyu Mustafa, da saura Sarakunan Jihar da suka hada da, Hamma Bachama,Mai Girma Irmiya Stephen, da Hamma Bata, Alhamdu Teneke, dukkansu daga karamar Hukumar ta Numan. Sannan kuma Mataimakin Shugaban kasar ya sami rakiyar Ministan Babban Birnin Tarayya, Muhammadu Bello, da Sanata mai wakiltar Adamawa ta Kudu, Sanata Ahmad Abubakar, gami da babban mai baiwa Shugaban kasa shawara a kan harkokin siyasa, Sanata Babafemi Ojudu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here