LABARI: Tsallaka Katangar Majalisa: Kwamishinan Shari’a Ya Nemi Afuwa

A ranar Talatar makon jiya ne wani abu mai kamar almara ya auku a zauren Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, inda Kwamishinan Shari’a na Jihar Nasarawa, Hon. Innocent Lagi ya tsallaka katangar Majalisar Dokokin Jihar.

Hakan ya faru ne a yunkurinsa na mika takardan dakatar da ‘yan majalisar, game da tuhumar da suke yi wa Shugaban hukumar zabe na jihar, Dakta Abdullahi Salluh Modibbo game da rashin bayyana sakamakon zaben kananan hukumomi guda biyu akan lokaci, duk da cewa  a kananan hukumomin an bayyana wadanda suka lashes zaben.

Kwamishinan shari’an ya yi amfani da dokar da kotu ta ba shi da nufin ya mika takarda da za ta dakatar da ‘yan majalisar daga wannan tuhumar  da suke yi wa Shugaban hukumar zaben. Amma ko da ya taho an garkame kofar shiga harabar majalisar.

Ganin haka ya bukaci a bude masa ya shiga, amma masu tsaron suka ce ba a ba su izinin kowa ya shiga ba, tunda ana zama.

Duk da cewa shi ma tsohon dan majalisa ne a shekarar 2007 zuwa 2011, sai kawai ya ajiye motarsa  a gefe ya kama katangar majalisa ya fada ciki, inda ya isa zauren da majalisar take zama, amma sai ya yi rashin sa’a ko kafin ya je an kammala batun cewa Kwamishinan Shari’a  ya haura Katanga  ya shigo, nan take hatsaniya ta kaure da shi da wasu ‘yan majalisar, inda nan take  jami’an  tsaro suka kama shi suka jefa cikin mota suka yi awon gaba da shi daga bisani aka sallamo shi.

Shi ma da ya tashi maida martini, Kwamishinan Shari’ar, Hon. Innocent Lagi ya yi karar dan majalisa mai wakiltar mazabar Keana, Hon. Orogoh ko da aka shiga Kotun tuni kotu ta tasa kyeyar dan Majalisar zuwa gidan maza dake garin Lafiya,  inda ya shafe awannia tsare daga bisani aka bada belinsa. da yake zantawa da wakilin LEADERSHIP HAUSA dangane da abin da ya faru, Kwamishinan Shari’ar ya ce, “Na samu labarin gayyatar da Majalisa ta yi wa  Shugaban hukumar zabe tare da jama’arsa, dangane da kananan hukumomi da ba a bayyana sakamakon su ba, alhali akwai kotun koken zabe, sai na kira Kakakin Majalisa na yi masa magana ya ce sam dole sai ya zo. Na kira Shugaban hukumar zaben na ce ya rubuta masu takarda cewa doka ba ta yarda da haka ba, ya ce a’a, shi zai je.

 Ranar Talata na tafi kotu na shigar da karar a dakatar da su, Alkali ya rubuta takarda cewa a je a dakatar da wannan maganar koda na isa gurin na tarar an rufe kofa sai na gabatar da kaina ga ‘Yan sanda suka ce a’a sai na tsallaka katangar na wuce.” In ji kwamishinan.

Kwamishinan ya ce hakan da ya yi bai keta doka ba, saboda babu dokar da ta ce wani dan Majalisa ya rufe kofar shiga majalisa.

Da ya ke amsa tambaya dangane da Dan majalisar da yake tsare ya ce, “Lokacin da muka je kai takarda majalisa sai da ‘yan sanda suka kwace ni a hannun shi har ya yaga min riga. Kuma dayansu ya fasawa ma’aikacin kotu hanci da kai! Ka ga ba siyasa ya kaimu gurinba, kuma ba ta da hargitsi ya kaimu gurinba, ka ga wannan laifi ne.” Daga bisani  Kwamishinan ya roki bangarorin dukansu da su yi hakuri tunda wurare ne na yin doka da kuma gurin duba doka.

Daga Zubairu T.M Lawal Lafiya.

 

Add new comment

Plain text

  • No HTML tags allowed.
  • Web page addresses and e-mail addresses turn into links automatically.
  • Lines and paragraphs break automatically.
 
 

Monthly archive