LABARI: Na Yafe Duk Wulakancin Da ‘Yan Siyasa Suka Yi Min A Baya —Gwamna

Gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Muktar Ramalan Yaro ya bayyana cewa ya yafe wa duk wadanda suka kuntatta masa lokacin da yake kujerar mataimakin gwamna.   Gwamnan ya bayyana haka ne a sa’ilin da yake kaddamar da shugabannin jam’iyar PDP na kananan hukumomi 23 na Jihar Kaduna, wanda ya gudana a dakin taro na Kasuwar Duniya dake hanyar Rigachikun.  

Gwamanan ya yi kira ga wadanda suka sauya sheka daga jam’iyyar  a dalilinasa su dawo domin hada karfi da karfe a samu nasara “Ina roko ga duk wadanda suka fice daga PDP saboda Muktar ya zama Gwamnan Jihar Kaduna, da su dawo a tafi tare,  saboda Muktar ba shi da matsala da kowa. 

A da can baya, Muktar ba komai ba ne,  sai a yanzu cikin ikon Allah Muktar ya zama Gwamnan Jihar Kaduna.  Ina  mai tabbatar ma ku  da cewa duk irin cin mutunci da wulakancin da wasu su ka yi min a lokacin ina mataimakin gwamnan,  da kuma a yanzu da na zama gwamnan, har ma da wanda watakila za a yi min bayan na sauka daga gwamna, wallahi ina mai kara tabbatar maku da cewa ni na yafe har ga Allah”. 

Gwamnan ya jawo hankalin ‘yan siyasa su game da fara kamfen alhali lokaci bai yi ba sannan ya ce akwai abin ya fi cancanta a mayar da hankali a kai  “Har yanzu akwai ayyuka da wannan gwamnati mai ci a yanzu ta sanya a gaba wanda muke sa ran cikin ikon Allah za mu kammala nan da wasu ‘yan lokuta”.  Kana ya bukaci sababbin shugabannin Jam’iyar PDP na kananan hukomomin su ji tsoron Allah, su tsaya su yi wa jam’iyyar da  jama’ar da suka zabe su aiki.

Daga Ibrahim Ibrahim,  Kaduna.

 

Add new comment

Plain text

  • No HTML tags allowed.
  • Web page addresses and e-mail addresses turn into links automatically.
  • Lines and paragraphs break automatically.
 
 

Monthly archive