Ƙalubalen Da Gidajen Yari Ke Fuskanta A Jihar Yobe

Gidan yari mahalli ne wanda ake tsare masu laifuka daban-daban; hakan yana zuwa ne bayan ƙuliya manta-sabo ya tabbatar da laifin mai laifi. Gidan-jarun waje ne da aka tanade shi domin je ka gyara halin ka. Daɗin daɗwa kuma, a kan yi amfani da kurkuku wajen adana waɗanda ake tuhuma ko aikata wasu manyan laifuka masu nauyi kafin alƙali ya kammala tattance matsayin shari’a a kan mutanen.

Akwai ƙarancin gidajen yari a jihar Yobe, yayin kuma da hakan ke jawo cunkoson fursunoni a ciki. Jihar Yobe tana da gidajen yari guda takwas a yankuna daban-daban da suka haɗa da Damaturu, Potiskum, Gashuwa, Fika, Gaidam, Nguru da kuma a Damagun. Haka zalika, tun kafin zuwan matsalar tsaro wasu daga ciki suna fuskantar ƙarancin samun cikakkiyar kulawar da ta dace.

Dangance da wannan, a halin da ake ciki yanzu gidajen yari a jihar cike suke da ƙorafe-ƙorafen manazarta bisa ga yadda Gwamnatin Tarayya ta kasa taɓuka wani abin a zo a gani a sha’anin. Yanayin wuraren da yadda ake tsare da mutane ya jawo cece-ku-ce a matsayin tauye haƙƙoƙinsu. Babu isassun ɗakunan kwana waɗanda ya kamata mutum ya zauna a ciki, babu magunguna da sauran ababen more rayuwa, sannan da ƙarancin yadda ake kula da fursunonin bisa tsari da mutuntawa.

Manya a tsakanin waɗannan gidajen yari dake jihar Yobe sune na Damaturu, Gashuwa sai na Potiskum. An gina waɗannan gidajen yari ne tun kimanin shekaru 100 (lokacin Turawan mulkin mallaka) in banda kwaskwarima da aka yi wa wasu daga cikin su. Yayin da zancen da ake ciki yanzu, ƙalilan ne daga cikin waɗannan gidajen yari suke aiki kamar yadda ya kamata. Wannan yanayin ya ƙara sanya fargaba a zukatan ‘yan rajin kare haƙƙoƙin bil’adama bisa yuwuwar samun ƙarin cinkoso da tafiyar hawainiya a ɓangaren yanke hukunci.

Manazarta sun sha yin kira na bai-ɗaya tare da bawa hukumomin da haƙƙin kula da gidajen yari a ƙasar nan ya rataya a wuyansa cewa su ɗauki matakin kawo ɗauki a cikin waɗannan gidajen na jarun. Bugu da ƙari sun sha buga misali da yadda wasu ƙasashe ke amfani da gidajen mazan wajen gyara gurɓatattun tunani ko tarbiyya da miyagun halaye.

Haka zalika kuma, ta fuskara shari’a suna kallon cewa cunkoso ko ƙazanta suna jawo cikas a gidajen yari da ake da su a ƙasar nan. A hannu guda kuma yana kawo tsaiko a ɓangaren shari’a. Haka kuma, matsalolin sun jawo da dama daga cikin mazauna gidan yarin faɗawa cikin mawuyacin hali na yunwa tare da nau’ukan cutuka maras adadi, inda wani sa’in matsalar ke kaiwa ga rasa rayuka.

Marigayi Mista Gani Fawehinmi, ɗan rajin kare haƙƙin bil’adama ne a Nijeriya, wanda yake ɗaya daga cikin fitattun mutane waɗanda suka yi zaman kaso a kurkukun Gashuwa a jihar Yobe a shekarar 1989. Har wala yau, mutumin da ake alaƙanta rashin lafiyar da tayi ajalin sa; a yayin zamansa na jarun a kurkukun Gashuwa.

Gani Fawehinmi wanda ya ɗauki tsawon kwanaki 121 a tsare, ya bayyana yadda taswirar ɗaya daga cikin waɗannan gidajen yari a jihar Yobe dake Gashuwa.

Ya fara da bayyana cewa, “a cikin ɗakin da aka saka ni, waje ne maras daɗi ko kaɗan. Na san abinda nake faɗa dangane da gidan kurkukun, tsawon sa bai wuce takon ƙafa 18 ba, faɗin sa kuma tako 10 ne. Har wala yau, an zagaye shi da wata makekiyar katanga wadda ta kai ƙafa 22 wadda na yadda za a yi ta bar iska ya shiga cikin ɗakin.

“Tagogin ɗakin da ake tsare da ni ‘yan ƙanana ne ainun, sannan shi ma ɗakin matsattse ne da har ba kada sukunin miƙe sawu domin walawa. Wai a haka ɗakin da aka tsare ni yana da ɗan dama-dama idan an kwatamta shi da sauran, amma dai babu silin a ɗakin; a fafarke yake, yanayin da zai ba zafin rana damar kutsawa kai tsaye ta ko’ina a ɗakin. Haka kuma, babu daɓen siminti a ɗakin, babu tabarma, balle kuma katifa; a haka aka bani tabarma na shimfiɗa”. In ji shi.

Ya ci gaba cewa, “A wannan fafutikar, kowanne lokaci idan na tuna wahalhalun da na sha a gidajen jarun yayin da nake tsare. A ɗakin da nake, ina tuna wasu yan ƙananan bokitai biyu; ɗaya a kan kwana wanda nake yin bawuli, ɗayan kuma a cikin sa nake yi bahaya”.

“Duk mutumin da ya zauna gidan yarin Gashuwa, tabbas zai bayyana maka cewa ya ɗanɗani kuɗar wahala. Abu na farko da za ka ci karo da shi su ne ƙadangarru; gada-gada, saboda a ɗakina kaɗai a cikin kowacce safiya ina ƙirga ƙadangaru sama da 100, sannan kuma ɗakunan maƙil suke da ƙyanƙyaso da sauran ƙwari”.

“Sannan akwai ƙuda masu yawa fiye da Maiduguri, kuma ga tsananin sauron masifa (gidan yarin yana manne kusa da kogin Yobe), yamma tana yi za ka rinƙa jin rugugin rurin ƙarajin sauro kamar kana maƙwabtaka da filin jirgi, a haka muke rayuwa ta zarar almuru ta yi kusa”. Ya ce.

A wani batu na daban kuma, ta dalilin yadda matsalar tsaro ta yi ƙamari a jihar Yobe, wanda mayaƙan ƙungiyar Boko Haram suka yi ta auna gidajen yari a jihar da zargin cewa ana tsare da mutanen su. Bisa ga wannan ne, da dama daga cikin gidajen jarun ɗin sun fuskanci hare-haren mayaƙan wanda hakan yayi sanadiyyar lalata gidajen yari baya ga asarar rayukan fursoni, yayin da wasu suka samu munanan raunuka. Halin da ya jawo a baya mayaƙan fasa gidan yarin Damaturu. Yayin da wannan harin da aka kai a wannan gidan yarin da makamantan sa suka maida hannun agogo baya a wannan haujin.

A cikin wata tattaunawa da kwamishinan shari’a na jihar Yobe; Barista Ahmed Goneri, dangane da ƙoƙarin gwamnatin jihar Yobe wajen rage matsalolin da ke kawo cunkoso a gidajen yarin jihar. Ya ce cewa cunkoson gidajen yari a ƙasar nan ya zama ruwan dare, duk da ya danganta daga wannan jihar zuwa waccan, musamman yadda yanayin su ya bambanta. Duk da yake a babu wadataccen gidan yari a Damaturu.

Ya ce, “Muna amfani da ƙaramin gidan jarun ne a Damaturu sannan kuma tuni mayaƙan Boko Haram suka ƙona ta. Kuma sabili da wannan matsala ta tsaron ne ma ya jawo mu kan yi amfani da gidajen yari daban daban, kawai muna amfani da gidajen yari guda biyun da muke da su a halin yanzu, kuma waɗanda muke da tabbacin tsaro da kayan aiki a cikinsu da ke a Gashuwa da Potiskum.

“Ba zan yi mamakin a samu cunkoso a gidajen yarin ba, amma da a ce muna da babban gidan yari a nan Damaturu, to zai yi wahala mu sami cunkoson. Ta dalilai guda biyu; ba muda yawan ƙararraki a nan Yobe da har zai jawo cunkoso a gidajen yarin, babban alƙalin jihar Yobe yana ƙoƙari koda yaushe wajen bibiyar lamurran shari’a, lokaci bayan lokaci, kuma muna ganin sakamakon wannan dangane da rahotannin da muke samu daga su gidajen yarin”. In ji shi.

Goneri ya sake bayyana wasu ƙarin matakan da ma’aikatar shari’ar ke ɗauka wajen hana samun cunkoson da suka haɗa da yadda gwamnatin jihar Yobe kan yi amfani da matakan yin afuwa ga wasu yan zaman jarun ɗin ko ta dalilin rashin lafiya. Ya ƙara da cewa, sannan da ziyarar da babban alƙalin jihar ke yi a gidajen kason a lokuta da dama, inda ya ce kuma ba ya ƙyale kowacce irin matsala ce da ta danganci wannan.

A zantawar LEADERSHIP A Yau da wani matashin mai fafutika a jihar Yobe, Malam Nura Ɗalhatu Audu, ya bayyana kaiconsa dangane da halin da gidajen yari suke a jihar inda ya ce wuraren suna cikin mawuyacin hali na nuna rashin ɗaukar ɗan’adam da kima. Ya ce halin ni-’yasu wanda fursunoni ke ciki a waɗannan gidajen yari ba shida kyaun gani.

Nura Ɗalhatu ya bayyana cewa, “kwanakin baya na kai ziyara a gidan yarin Gashuwa, gaskiya ban ji daɗin abinda idona suka gani ba, tattare da halin matsalar ƙarancin wuraren kwana, ruwan sha da magunguna da sauran abubuwan more rayuwa waɗanda ya kamata a ce ɗan Adam ya samu. Yayin da na lura da nau’in abincin da ake ba su, ya sha bamban da yadda yake rubuce a takarda, kuma ya saɓa tunanin cewa wannan shi ne abincin da ya kamata a ce mutum yana ci, wanda ina zargin cewa kamar akwai haɗin baki ne tsakanin hukumar gidan yarin da masu kula da kwangilar ba su abincin.

“Kamata ya yi a ce gwamnatoci da hukumomin da abin ya shafa da su sake duba lamarin gidajen yarin ƙasar nan, a yi amfani da waɗannan wuraren wajen goge matsalolin da suka jawo laifukan da suke jawo ɗaure mutane a jarun. A samar musu da makarantu tare da ƙwararrun malamai da masana a ɓangarorin rayuwa daban daban wajen faɗakar da su halin da rayuwa take; kamar yadda yake a wasu ƙasashen da suka city gaba”. In ji Nura Ɗalhatu.

Exit mobile version