Daga Wakilinmu
Ɗaya daga cikin kwamandojin ƙungiyar Boko Haram da aka kama a Jihar Ondo, Muhammad Bashir, ya tabbatar wa jami’an ‘yan sanda cewar sun shigo jihar ne domin su tarwatsa ta,sai kuma Allah ya fallasa asirinsu har jami’an tsarosuka samu nasarar cafke su.
Bashir ɗan shekaru 20, wanda ya ce shi daga jamhuriyar Nijar yake, an gurfanar da shi tare da wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne su 11, da ‘yan ƙungiyar asiri da masu noman tabar wiwi, ya tabbatar da cewa sun shigo jihar ne domin haifar da yamutsi.
Yace jami’an ‘yan sanda sun kama shi ne a lokacin da ya fito zagayen ganin gari. Rundanar ‘yan sandan Nijeriya ta bayyana cewa jami’anta ne suka ga Bashir yana sallah a gefen babbar hanya, don haka sai suka tafi da shi ofishinsu domin ya amsa tambayoyi.
Daga nan ne jami’an ‘yan sanda suka bi sawun wanda ake zargin, inda suka samo nasarar cafke shi.
Muhammad Bashir da ake zargi, ya bayyana wa manema labarai cewa ‘ya’yan ƙungiyar suna haɗuwa a cikin daji domin tattaunawa kan shirye-shiryen harin. Sannan kuma akwai wani babban kwamandansu da zai kawo musu kayan aiki, a ranar da suka shirya za su ƙaddamar da hare-haren.
Ya ƙara da cewa, suna da yawa sosai da suke halartar ganawar, amma akwai ɗaya da ‘yan sanda suka sake damƙe waa ƙarshen makon da ya gabata, mai suna Idris Babawo, dukkansu kusan wuri ɗaya aka kama su, wato a Isua da ke ƙaramar hukumar Akoko ta jihar Ondo.
Shi ma Babawo da aka kama lambarsaa jadawalin ‘yan ta’addan da sojoji k enema, shi ne na 156. Tuni dai ‘yan sanda suka miƙa shi hannun jami’an soji domin su gudanar da bincike.
Bashir da ake zargi, yace, asalinshi ɗan Jihar Nasarawa ne, kuma mahaifinsa ne ya kore shi daga gida, sannan sunzo nan Jihar Ondo ne da ƙaninshi, ya ce lallai ya taɓa hallaka mutum biyu (Babban Mutum da ƙaramin yaro) yayin da suke aiki a gonarsu a Jihar Nasarawa, watanni takwas bayan ya zama ɗan ƙungiyar Boko Haram.
Bashir ya ce, sam ba ya shakkar kashe mutum, kisa ma ya zame mishi tamkar nishaɗi ne. Sannan da yake magana game da mahaifiyarsa ya ce, ‘yar Maiduguri ce, kuma ta na fama da cutar taɓin hankali.
Da aka tambayeshi ko yaushe ya zama ɗan ƙungiyar ta Boko Haram, sai ya ce, shugabannin ƙungiyar ne suke zaɓe su a jihohin arewa.
Kwamishinan ya ce; “bayan an yi wa wanda ake zargin tambayoyi sai ya amsa cewar shi ɗan ƙungiyar Boko Haram ne, daga jamhuriyar Nijar ya zo, mahaifiyar sa kuwa ‘yar Maiduguri ce, ya gudu daga Maiduguri ne zuwa Jihar Nasarwa inda daga nan ya taho Jihar Ondo, Bashir ya ce, shi mabiyin wani na hannun daman Shekau ne mai suna Daffo.
“Batun shigowar ’ya’yan ƙungiyar Jihar ta Ondo kuwa, za mu tabbatar da mun neme su duk inda suke domin fuskantar shari’a, idan kuwa har yanzu suna cikin jihar nan za mu cim musu. Wannan aikinmu ne don haka mun san yadda za mu kamo su, ina roƙon al’umma su kwantar da hankalinsu sannan su taimaka mana da duk wani bayani da zai kai ga gano ’ya’yan ƙungiyar da ma duk masu aikata laifuka a Jihar.’ Inji Kwamishinan ‘yan sandan Ondo.