ƘUNDIN MASARAUTA

Daga Rabi’u Na’auwa Balarabe +23480 2299 9898 naauwa1@gmail.com

Wannan kundi zai fara ne da jawabi a kan tarihin sunayen sarautu a ƙasar Hausa. Sunayen sarautu a ƙasar Hausa sun samo asali ne daga yarirrika guda uku, waɗanda su ka haɗar da Hausa da Larabci da Kanuri sai kuma Fulatanci.

A wani Bincike da Malam Ibrahim Ado Kurawa ya gudanar a kan Sarautu na ƙasar Kano ya bada haske mai yawa a wannan aiki da na yi baya ga jawabin masana harkokin sarauta wanda wannan shafi ba zai ishe ni in ce sai na jero su da kuma irin gudunmawar da su ka bayar ba.

Kamar yadda jawabi ya gabata wannan harshe namu na Hausa ya yi aron kalmomi da dama daga yaren Kanuri da Larabci kamar yadda masana da yawa su ka kawo kamar su: Neil Skinner (1980), Khalil (2009) sun kawo yanayin yadda a ke yin aron da kuma misalan kalmomin da a ka aro a wasu yaren.

Wanda ya fi zurfin bincike a wannan fannin na aron kalmomin da Hausawa su ka yi shi ne Skinner (1980:169 -202), domin shi ya kawo yarurrika da dama da Hausa ta yi aro a cikinsu kamar Nufanci da Yarbanci da Barbarci da sauransu.

A wannan karon za mu fara ne da sarautun da a ka samar na Hausawa waɗanda tarihi ya nuna sun samo Asalinsu ne daga masarautar Kano a lokacin Sarkin Kano Gajimasu Ɗan Warisi (A.H. 488-528, A.D. 1095 -1134).

Sunayen sarautun da a ka fara samu na Hausa masu “Ɗan” a farkonsu (Palmer, 1908) inda ya yi duba ga muatane da suka taho da Bagauda Ɗan Bawo daga Daura zuwa Kano, guda bakwai, ya naɗa yayyensu sarauta kuma kowanne sarautarsa tamu ne daga suanan mahaifinsa, waɗannan sarautu su ne:

Irin waɗannan sarautu sun cigaba da samuwa har bayan zuwan Sarkin Kano Rumfa, inda lokacin Sarkin Kano Muhammadu Kisoki (A.H. 914-972. A.D. 1509-1565) a ka samar da sarautun Ɗan Maje (ma’ana Ɗan Sarki ) da Ɗan Makwayo (Ɗan Mai Daraja) da kuma Ɗan Iya (Ɗan Mahaifiyar Sarki).

Sannan kuma akwai sunayen sarautun da a ke kagarsu daga sunan aikin da Masarauta ta ba mutum kamar misali; Magajin Gari, daga jiran gari, Madaki daga Doki, sai Makama daga kamu.

Daga zamanin Sarkin Kano Muhaacmmadu Rumfa (1463-1499AD-867-904H) har izuwa lokacin Fulani an samar da sarautu da dama an bayar da su ga bayin Sarki da sauran jami’an fada.

Baya ga aro da a ke yi daga yare izuwa wani kamar yadda Hausa su ka yi daga Kanuri da Barbarci a sunayen sarautu akwai kuma aro da a ke yi tsakanin masarautu shi wannan aron bai takaita ga yaren wasu ba kadai, har masarautun Hausar a na aronsu indai masaratar da za ta yi aron bata da wannan sarautar.

Misalin irin wannan aron a masarautar Kano akwai Waziri da masarautar Kano ta aro daga ƙasar Sokoto a ƙarshen ƙarni na 19, inda Sarkin Kano Alu Mai Sango (1894-1903) ya aro ta ya naɗa wa Kawunsa Ahmadu, sannan Ado Bayero (1963 – 2014) ya aro sarautar Sardauna ya naɗa ta ga Gwamnan Kano na lokacin Malam Ibrahim Shekarau.

Baya ga wannan masarautar Kano ta aro sarautar Kaigama da Kachalla da Bunu da Zanna daga Masarautar Borno sai kuma Ajiya da Talba daga Bauchi, sai Dan Masani, Durɓi da Sa’i daga Masarautar Katsina, sai San Turaki da Katuka da Matawalle daga kasar Zaria.

Haka nan kuma wasu masarautun sun ari sarauta daga masarautar Kano misali Zaria sun ari sarautar Ɗan Isa da Ɗan Amar daga Kano. Haka nan masarautun Gusau, Birnin Gwari da Anka sun ari sarautar Wambai daga Kano. Amma kamar yadda a ka yi bayani a baya yawa-yawan waɗannan sarautu da a ka aro asalinsu daga Larabci ko Kanuri su ke.

Dalilin da ya sa a ke yin aron sarauta shi ne buƙatuwa da naɗa irin wannan sarauta ko don rashin sarautar da za a naɗa mutun, ko domin ma’anar sunan sarautar ga misali ta ɓangaren ilimi ko sadaukantaka kuma wanda za a naɗa ya na da wannan ko domin wani dalilin daban.

 

Exit mobile version