Ƙungiyar Bella Ta Kai Wa Asibitoci Tallafin Magunguna A Bauchi

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Wata gamayyar ƙungiyar matasa masu zaman kansu, masu fafukar tabbatar da daidato a tsakanin musulmai da kirista mai suna a shiyyar Bauchi ta Kudu ‘Bauchi South Youth Coalition’ da haɗin guiwar ‘Bella Foundation’ sun raba kayyakin magungun jinya da kuɗinsu ya haura naira dubu ɗari biyar 500,000 a cibiyoyin jinya na Asibitin Tashan Babiye da ke Bauchi da kuma asibitin jinya da ke Yalwan domin taimaka wa gajiyyu da kuma marasa lafiya.

Da ya ke yi wa LEADERSHIP A Yau, ƙarin bayani kan wannan tallafin nasu da kuma manufar kafa wannan cibiyar tasu, shugaban gamayyar haɗakan ƙungiyar, mai suna Kwamared Daure Daɓid Yankshi ya shaida cewar babbar manufarsu dai ita ce domin daidaita tsakanin matasa musulmai da kirista da kuma tabbatar da fahimtar juna a tsakanin juya.

Ya ce, a bisa haka ne suke gudanar da aiyukan jin ƙai da taimakon jama’a domin rage wa jama’a raɗaɗin talauci, kana da fitar da masu kunci zuwa ga ‘yanci “Mun raba kayyakin jinya a jiya litinin a asibitin Tashan Babiye da kuma asibitin Yalwa-Lemura mun kai tallafin magunguna da sauran kayan jinya da kuɗinsu ya haura dubu ɗari biyar”. A cewar shugaban

Yakshi ya bayyana cewar daga cikin aiyukansu har da kuɓutar da jama’a daga cikin wani yanayin rayuwa a bisa hake ma suka ceto wasu matasa masu laifu daban-daban su 25 a gidan kurkuku domin ‘yantar da su “Mun je gidan yarin Bauchi mun kuɓutar da mutane sama da 25, kuma mun yi feshin magungunan, mun raba musu kayyakin abinci da na amfanin yau da gobe, kana mun tsaftace rijiyar gidan yarin da sauran aiyukan da muka yi”.

Kwamared Daure Daɓid ƙara da cewa “mun kafa wannan ƙungiyoyin ne domin kawar da banbance-banbancen na addini da ke tsakani. Kuma daga cikin ƙungiyoyin nan mun haɗa da musulmai da kuma kirista inda muke faɗi tashin ganin an samu ci gaba mai ma’ana domin shi fitina ko tashin hankali bai da fa’ida. Sannan muna faɗakarwa kowa ya gane cewar dukkanimu ‘yan uwan juna ne don haka faɗa ba namu bane. Muna yin aiyukanmu tare ba tare da nuna banbanci ba” a cewarsa

Shugaban haɗakar ƙungiyar, ya kuma ce aikace-aikacen nasu bai tsaya haka nan ba, sun kuma yi nasarar kai tallafi sansanin ‘yan gudun hijira da kuma ɗaukan nauyin biyan kuɗin makarantar wasu daga cikin ‘yan gudun hiran da suke jihar ta Bauchi. hakazalika sun kuma nausa bibiyar kula da marayu da marasa galihu inda suka tallafa musu da kuma kai musu ɗauki. Kana sun kuma yi feshin maganin sauro a faɗin jihar Bauchi domin rage yawaitar cutar maleriya.

Da ya ke mana ƙarin bayani kan hanyoyin da suke samun kuɗin da suke tafiyar da waɗannan aiyukan a cikin ‘yan kwanakin nan ya bayyana cewar ganin muhimmancin aiyukan nasu ne ya sanya suke fitar da kaso daga aljihunsu domin yin hidima wa jama’a kana da suna kuma samun tallafi daga wajen Alhaji Kabiru Sallau.

Haka kuma Daure ya ce kasantuwarsu matasa masu tunani mai kyau ne ya sanya suka kafa wannan cibiyar da zimmar gudanar da aiyukan taimakon jama’a masu tarin yawa kana da kuma daidaiwa tsakanin musulmai da kirista.

Da ya ke amsar maganin jinya da su kai asibitin jinya na Tashan Babiye, jami’i mai kula da asibitin, Alhaji Ahmad Dauda Jika ya jinjina wa ƙoƙari da kuma sa’ayin waɗannan matasan, inda ya nuna su a matsayin abin koyi. Ya kuma baya sosai da tallafin da su kawo, inda ya sha alwashin tafiyar da mugungunan ta hanyoyin da suka kamata.

Exit mobile version