Ƙungiyar Izala Ta ’Yanta Fursononi 15 A Bauchi

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Ɗaya daga cikin ƙungiyoyin addinin musulunci mai fafatukar yaƙar bidi’a da kuma ɗabba’a sunnah wato ‘Izalatul Bidi’a Wa Iƙamatus Sunnah’ ta ƙasa ta biya tara gami da ‘yanta fursononi 15 masu laifuka daban -daban domin su zama ‘yantattu domin yin rayuwa daidai da kowa a jihar Bauchi a cikin makon nan.

Kwamitin wa’azi da faɗakarwa na ƙungiyar ta Izalar ne suka yi wannan gagarumin aikin na ceto da kuma ‘yanta ɗaurarun domin samar musu da ‘yancin rayuwa daidai da kowa.

Shugaban kwamitin wa’azi ta ƙasa Malam Muhammad Malwan ya tabbatar da fitar da fursinonin a wajen wa’azin da suka gudanar wa fursinonin da suke garkame a cikin gidan yarin Bauchi.

Malam Malwa ya ce wannan yunƙurin sun yi shi ne da nuhin samar wa fursinonin ‘yancin dawowa cikin ‘yan uwa da abokan arziki gami da dawowa cikin al’ummominsu domin ci gaba da rayuwa don ba da gudunmawa wajen ci gaba da gina ƙasa. A ta bakinsa “Domi shiga gidajen yari ya ƙara mana ilimi, ya ƙara mana basira ya kuma ƙara mana hangen nesa. A da wanda ba ya shigowa cikin gidan yari ya kan ɗauka duk wanda ya samu kansa a gidan yari to mutumin banza ne. alhali kuma abun ba haka ya ke ba, domin wani laifinshi ne wani kuma jarabawace ta kawoshi ga shiga gidan yari, jarabawace da aka rubuta masa tun yana cikin mahaifiyarsa sai ya shiga gidan yari koda bai yi laifin komai ba”. ta bakin shugaban kwamitin wa’azin na Izala

Sai kuma ya shawarci waɗanda suka ‘yantar da ɗin da ji tsoron kada su koma aikata aiyukan da ya kawosu ga shiga wannan gidan tun a fari, ya shawarce su da su kauce wa aiyukansu muna na baya. Sai kuma ya buƙaci jami’an gidan yarin da a kodayaushe suke kyautata wa fursinonin da suke hanunsu tare kuma da basu horo na musamman kan sana’o’in dogaro da kai domin bayan cinye wa’adinsu su samu abun yi.

A nasa jawabin mataimakin shugaban gidan yarin DC Sulaiman Inuwa ya nuna matuƙar farin cikinsa a bisa karamcin da ƙungiyar Izala ta yi wa fursinoni, yana mai cewa Allah ya biya su da sakamako mai kyau “ina nuna cikakken farin cikina a bisa wannan gunmawar da ƙungiyar Izala take mana saboda me ita tarbiyya mutum ɗaya baya yinta, tarbiyya ya hau kan iyaye, jama’an gari, da suransu”. A ta bakinsa

A cewarsa DC Sulaiman Inuwa tun usuli an gina wannan gidan yarin na Bauchi ne da nufin ya ɗauki mutane ɗari biyar kacal amma ya yanzu haka mutane sama da dubu ɗaya ne suke shake a garƙame a cikin wannan gidan yarin, a bisa haka ne ma ya ke kira ga masu hanu da shuni da kawo ɗauki ta fuskokin da suka dace kama biyan tara domin ‘yanta wasu da kuma kawo tallafi kamar yanda ya dace domin inganta aiyukan gidan yarin da kuma jin daɗin fursinonin.

Wasu daga cikin fursinonin da aka ‘yantar sun nuna maƙutar jin daɗinsu a bisa wannan karamci inda suka sha alwashin cewar ba za su koma aikata aiyukansu na baya ba, sun kuma yi fatan Allah ya yafe musu laifukansu.

 

 

Exit mobile version