Ƙungiyar Malaman Makaranta Ta Umarci Mambobinta Su Je Aiki Da Bindiga A Taraba

Daga Sulaiman Ibrahim

Shugaban kungiyar malamai ta kasa (NUT) reshen jihar Taraba, Kwamared Peter Jurius Vow, ya shawarci dukkanin malaman jihar da su dauki bindiga a yayin da suke zuwa makarantun su domin kare kan su da daliban su.

Jurius ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga sace dalibai a wasu jihohin Nijeriya.

Ya daura maganarsa ne kan maganar da ministan tsaron kasa, Bashir Magashi ya yi kwanan nan, cewa ‘yan Nijeriya su kasance a shirye don kare kansu daga ‘yan bindiga.

Ya kara da cewa makomar Nijeriya tana hadari, ganin yadda sace dalibai ke yawaita a kasar nan.

“Wadannan yaran da ‘yan bindiga ke garkuwa da su, cikin su wasu likitoci ne, ‘yan jarida, farfesoshi, gwamnoni ko shugabannin duniya na gobe.

“Game da abin da ke faruwa, muna fuskantar barazana ga makomarmu, ya kamata gwamnati ta kara himma kan matakan tsaro, ya kamata mu ma mu yi taka-tsan-tsan a muhallinmu, mu bayar da rahoton fuskokin da ba a saba ganin su ba ga jami’an tsaro da kuma lura da yankunanmu don magance matsalolin rashin tsaro.” Inji shi.

Exit mobile version