Daga Lawal Umar Tilde, Jos
‘Ya’yan ƙungiyar, “The Transform Nigeria Group [TNG]’, ƙarƙashin jam’iyyar PDP ta kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da taron shiyyar Arewa ta tsakiya, a watan nan mai kamawa na Nuwamban 2017.
Bayanin haka na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar wanda ke ɗauke da sa hannun Ko’odinetan ƙungiyar na ƙasa, Kwamared Idris Zahiri, wacce kuma aka raba wa manema labarai a garin Jos a ƙarshen makon da ya gabata.
Ƙungiyar ta ce, taron wanda ake sa ran halartar ‘ya’yan ƙungiyar daga kowanne lungu na ƙasar nan, sun shirya ayyana kiransu ga tsohon ministan ayyuka na musamman, Barista Kabiru Tanimu Turaki, da ya fito ya nemi takarar shugabancin ƙasar nan a zaɓen shekarar 2019.
Ya ce, a baya sun sha yin kiraye-kiraye ga shi Kabiru Tanimu Turaki ɗin da ya fito ya nuna wa ‘yan Nijeriya zai tsaya takaran amma a yanzu ya zama wajibi ne a gare su da su tilasta shi ya fito ya faɗa wa mutanen ƙasar nan ya amsa gayyatarsu.