Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RAHOTANNI

Ƙyautar Mota Ta Tarwatsa Jam’iyyar APC A Taraba

by Tayo Adelaja
October 23, 2017
in RAHOTANNI
2 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Aliyu Idris daudawa

Akwai alamun da ke nuna cewar wata matsala ta taso a reshen jam’iyyar APC Ta jihar Taraba, saboda kuwa wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar, waɗanda suke nuna goyon bayansu ga Ministar Harkokin Mata, Aisha Alhassan, sun buƙaci tsohon shugaban jam’iyyar na jihar, Hassan Arɗo da ya dawo da motar da tsohon shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya bashi kyauta.

Bincike ya nuna shi Arɗo, wanda shi babban mai goyon bayan Hajiya Aisha ne, yanzu ya samu matsala ne da ita Ministar Harkokin Matan, sai hakan ya sa suka kafa wata ƙungiya wadda suka sa ma suna ‘Integrity Group’, wannan ƙungiya dai kwanan ne suka nisanta kansu da kalaman da Ministar ta yi, wanda hakan ya sa jam’iyyar a jihar a na yi mata wani gani-gani. Amma har ila yau waɗansu da har yanzu suna ba Ministar goyon baya, sun kafa kwamiti wanda zai kawo ƙarshen rikita-rikitar, a dalilin bada kyautar motar.

Arɗo wanda ba da daɗewa bane aka bashi muƙamin  Jakada, zuwa ƙasar Trinidad da Tobago. A tattaunawarsa da majiyarmu, ya ce;  “an aiko mani da wasiƙa inda aka buƙace ni da cewar tsohon shugaban ƙasa Atiku Abubakar yana son in maido da motar  da ya bani kyauta.

Sauran mambobin kwamitin kamar yadda shi Arɗon ya bayyana, sun haɗa da Haladu Yakubu wani lauya, Sani Mamman Posa, Aliyu Umar Bali, da kuma Godin Ɓillana.

Takarda ta biyu kamar yadda a cewarsa; “An ce ta fito ne daga Atiku Abubakar, Abdullahi Nyako ne ya sa hannu a kanta, an kawo mani ita, na lura an rubuta ta ne a ranar 27 ga Satumbar 2017’’.

Ya ƙara jaddada cewar “Ni na san kawai domin ina goyon bayan Buhari, shi yasa duk suke mani haka. Wannan ne ma dalilinmu na kafa ƙungiyar Integrity group’’.

Shi ma da yake tofa albarkacin bakin sa, Abdullahi Ade wanda shi ne shugaban matasa na jam’iyyar, ya ce, su kawai suna buƙatar ya dawo da motar ne, saboda ba shi aka ba, ta jam’iyya ce.

Ɗaya daga cikin jiga-jigan ‘Integrity Group’, Iliyasu Mu’azu ya bayyana cewa ɓangaren Ministar Matan na son kawo saɓani da ɓata jam’iyyar ne a jihar, saboda kuwa ɓangaren sun yi niyyar barin APC.

Ya ce, “mu muna goyon bayan Buhari, ita kuma tana nuna sai mai gidanta na siyasa Atiku, ƙiri ƙiri muka faɗa mata mu bamu yin Atiku, ko da Atiku ya amshi motarshi wannan ina shakkun haka, mu ‘yan ƙungiyar integrity, a shirye muke mu sawo ma Ambasada Arɗo wata mota’’.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Diezani Da ‘Yan Tawagarta: Tsarinsu Da Yadda Suka Damfari Nijeriya

Next Post

Masu Ruwa Da Tsaki Sun Kaɗa Ƙuri’ar Amince Wa Shugabancin Buhari A Adamawa

RelatedPosts

ACF

Kungiyar ACF Da Badakalar Jagoranci A Yankin Arewa

by Muhammad
2 days ago
0

Daga Zailani Bappa, Al’ummar Arewa da dama za su tabbatar...

NLC

Mafi Karancin Albashi: Wata Kungiya Ta Yi Tir Da Kalaman NLC Akan Dan Majalisa Datti Babawo

by Muhammad
2 days ago
0

Daga Bello Hamza, Wata kungiya mai zaman kanta mai suna...

Abduljabbar

Abduljabbar Bai Kai Darajar A Yi Masa Gangami Ba –Sheikh Khalil

by Muhammad
3 days ago
0

Ya Ce, Dalilin Da Ya Sa Sarkin Musulmi Ya Hana...

Next Post

Masu Ruwa Da Tsaki Sun Kaɗa Ƙuri’ar Amince Wa Shugabancin Buhari A Adamawa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version