Ɓarkewar Gobara A Tafa: Da Ma Ana Tsammanin Haka

Daga Ibrahim Iliyasu, Tafa

Al’umman garin Tafa da ke Ƙaramar Hukumar Kagarko, sun wayi gari a ranar Asabar ɗin ƙ arshen makon da ya gabata cikin jimami da alhinin ɓarkewar wata mummunar gobara. Gobarar da hasashe ke nuna cewa an daɗe ana tsammaninta.

Tafa gari ne da direbobin manyan mota suke ajiye motocinsu domin kashe dare, samun hutu, ko raba tafiya, kafin su kama hanya zuwa mabambantan wuraren da zasu kai ko ɗauko kaya.

Direbobin da ke tuƙ a motoci masu ɗauke da tankunan man fetur sun fi yawan tsaya wa a wannan gari na Tafa. Duk da kuwa akwai wasu direbobin manyan mota, waɗanda suke safarar wasu kayayyakin na daban ba man fetur ba.

Al’umman da ke zirga-zirga a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, sun fi kowa sanin irin haɗarin da ke tattare da garin Tafa; saboda yadda aka mayar da garin matattara ajiyan manyan motoci. A wasu lokutan, mai mota zai sako ta a guje, ba tare da ya shirya wa taka burki ba, babbar mota za ta turo kai kan titi.

Duk da irin wannan barazana na rashin tabbas dangane da ajiye manyan motoci da ake yi a bakin hanya a garin Tafa. Mafi fargaba, kuma wanda al’umma ke kwana da tashi da roƙ on Allah ya hana aukuwarsa, shi ne  ɓarkewar gobara. Domin dama ana tsammanin cewa duk inda man fetur yake, gobara ba za ta yi kyau ba.

Masana sun yi rubuce-rubuce da dama dangane da kuskuren ci gaba da ajiye manyan motoci da ake yi a garuruwan; Tafa ta hanyar Abuja zuwa Kaduna, da kuma Marabar Jos ta hanyar Kaduna zuwa Kano. Waɗannan wasu hanyoyi ne masu tada hankali, da sanya wa matafiya firgici, da rashin tabbas.

Sannan ƙ ungiyoyi, cibiyoyi da ɗaiɗaikun al’umma sun janyo hankalin gwamnati kan irin haɗurran da suke ƙumshe da irin ajiyar manyan motoci akan hanya da ake yi a garuruwan biyu. Amma abin har yanzu, shiru ake ji. Babu wani ƙ waƙ ƙ waran mataki.

Haɗarin da ake tsammanin a kowanne lokaci zai iya aukuwa a ɗayan biyun waɗannan garuruwa; Tafa da Marabar Jos, ya auku a garin Tafa a ranar Asabar. Yadda lamarin kuwa ya faru shi ne, wani mai ƙ aramar mota ne ya bugi bayan wata babban motar da ke ɗauke da man fetur. Karon da ya janyo babbar motar ta ɗan fashe kaɗan, har man fetur ɗin da ke cikinta ya fara zuba.

Ba a take motar ta kama da wuta ba. Yayin da jama’a suka ga yadda man fetur ɗin ke kwarara a ƙ asa, sai suka fara rububin wawaso. Wasu da galoli, wasu robobi da kwanuka. Haka suka far wa wannan man fetur da ke zuba a ƙ asa, ba tare da taraddadin cewa bala’in gobara na iya  ɓ arkewa ba.

A irin wannan hali na rububin man fetur ɗin tankard a ta fashe ɗin ne, sai wani ya ɗauko baro (irin wanda ake dakon kaya da shi) da zimmar zai zo ya zuba man fetur ɗin a cikin baron, idan ya so sai ya je ya samu wuri ya juye.

Wannan mai baron ne ya karci kan titi da baronsa, lamarin da ya haifar da tartsatsin wuta, sai gobara ta tashi. Gobarar ta afku ne sakamakon jiwo ƙ anshi wuta da tankar man ta yi daga tartsatsin kartar titi da baron nan yayi.

A take, tankar man fetur ɗin ta fashe, gobara ta  ɓarke. Sauran wuraren da ke maƙ wabtaka da inda motar take a jiya su ma suka amsa. Wani gida, wanda shi ne mafi kusa da motar ne ya fara ƙ onewa. Gidan na da ɗakuna 30 a cikinsa, da shagunan sama da 15. Shagunan waɗanda gaba ɗayansu shaƙ e suke da mabambantan kayan kasuwanci.

A hakan ma, shaidun gani da ido, sun shaida wa LEADERSHIP A Yau cewa, a hakan ma gobarar ta zo da sauƙ i, saboda lokacin da man fetur ɗin ke zubo wa daga tankar man, yana zuba ne a cikin wani kwalbati. Don haka ko da wutar ta tashi, sai ya zama kwalbatin ya hana yaɗuwar wutar zuwa sauran sassa-sasan garin, ko zuwa ga wasu ƙ arin motocin man fetur ɗin.

Wakilinmu ya bibiyi lamarin, inda ya samu tattaunawa da wasu da wannan lamari ya shafa kaitsaye. Sannan kuma ya zagaya zuwa asibitocin da aka kwantar da waɗanda suka samu raunuka. Da yake a na ci gaba da samun ƙ arin waɗanda suka rasa rai a sanadiyyar gobaran, sakamakon jama’a sun samu munanan raunuka, ya zuwa haɗa wannan rahoton mutum 3 ne aka samu tabbacin cikawarsu.

A gidan da gobarar ta cinye ɗakuna 30, da shaguna sama da 15. Wakilinmu ya samu zantawa da Hajiya Bebi mai tuwa, wacce ita ma shagunanta biyu suka yi ƙ urmus. Hajiya Bebi ta kasance tana da shaguna biyu a jikin gidan; ɗaya wanda take sana’a tuwo-tuwo, sai ɗaya shagon kuma tana siyasar da gwanjo.

Hajiya Bebi ta ce: “A lokacin da mai ƙ aramar motar ya bugi wannan motar tankin, babbar motar ta ɗan fashe, inda wani hayaƙ i ya tashi sama, sai dai ba kowa ne ya lura da wannan hayaƙ in ba. Man sai gangarowa yake yi ƙ asa, sai mutane suna zuwa suna ɗiban man. Ana ta gargaɗinsu, suka ƙ i sauraron kowa. Sai wani ya kawo irin baron tura ruwan nan. Toh ina ga baron na sa ne ya kankari ƙ asa, sai motar nan ta amsa. Da ta amsa ta kama, sai muka fara gudu. Wutar kuma ƙ ara tashi ta ke yi. Wannan ne ya sa wutar ta gangaro har zuwa shagunanmu. Ta cinye gidan da shagun nanmu suke.

“Da shagunan da ɗakunan cikin gidan babu abin da aka fita da shi, duk sun ƙ one. Haka nan muka fito tsurarmu. Akwai wani mutum da yake tiransifa na banki, shi yana cikin shagonsa ma abin ya rutsa da shi, ranga-ranga aka fita da shi zuwa asibitin gwagwalada. Mutane da yawa sun mutu, wasu an kai su asibitin Talba, wasu kuma sabuwar Wuse, wasu kuma an kai su Gwagwalada.

“Ni sai yanzu ma hankali ya dawo jikina. Mata da yara ƙ ananan wannan lamari ya rutsa dasu. Mutane da yawa basu ga ‘yan uwansu ba. Ko mu daga  ɓ angarenmu, an kai mutane bakwai zuwa asibiti.” Inji ta

Domin jin irin raɗaɗin da al’ummar garin Tafa suka tsinci kansu a ciki, da kuma irin koken da suke da shi a matsayinsu na mazauna wannan garin. Wakilinmu ya samu zantawa da dagacin garin Tafa mai suna Bitrus James, shi ne Dagacin Gundumar Tafa. Shi haifaffen garin Tafa ne, ya ma ce iyayensu ne usulin garin.

Da yake fashin baƙ i kan hasashen da ake yi na tsammanin yiwuwar afkuwar haɗari makamancin wannan a garin Tafa, dagacin ya bayyana cewa: “Lallai muna tsammanin irin haka, saboda mun kai ƙ orafi da dama. Saboda bamu jin daɗin abubuwan da masu manyan motocin nan suke yi mana, na ajiye motoci akan hanya, da shigar wa mutane kan hanya ba tare da lissafi ba.

“Wannan gaba ɗaya laifin gwamnati ne, saboda ta ƙ i kula wa. Tamkar ba ta san darajar al’ummar da kenan garin Tafa bane. Mu mutane ne masu biyayya ga gwamnati, amma ba ta kula mu. Mun ta ɓ a ba gwamnati wuri kyauta, don a gina wa masu manyan motocin nan wurin ajiye motocinsu. Amma har yanzun shiru.

“A lokacin gwamnatin baya, mun shaida ma tsohon gwamnan jihar Kaduna Ramalan Yero cewa mun gamsar da mutanenmu ne akan a ba gwamnati waɗannan filayen don a samar da wata kafa ta kiyaye ajiye motoci a kan hanya.har zuwan sabuwar gwamnatin nan, gwamna El-rufai ya zo ya yi mana alƙ awarin cewa za su yi ‘Trailer Park’ a garuruwan Tafa da Marabar Jos. Amma yanzu gashi abin ya zama tamkar wasan yara.

“A wannan hatsarin da ya auku, an tafka asarar da ya zuwa yanzu ba za a iya tantance ta. Akwai waɗanda sun fi shekara 10 suna tattalin jarinsu. Sannan an samu masu raunuka da dama, da asarar rayuka.

“Ina kira ga gwamnati da su taimaka su duba lamarinmu, su yi mana abin da ya kamata. Gwamnati ta kafa doka akan ajiye motoci akan hanya, amma wannan sai ta gina musu wuraren da zasu riƙ a ajiye mota. Sannan su ma direbobi su daina aikata abubuwan da basu dace ba, don suna  ɓ ata mana suna a wasu lokuta. Akan abu kaɗan sais u gicciye mota a kan hanya, wai don an  ɓ ata musu rai, wanda wannan ba ƙ aramin kuskure bane.” Inji dagacin

Domin jin ta bakin jami’an tsaro, wakilinmu ya samu tattaunawa da DPO ɗin Tafa, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai shi ma a nasa  ɓ angaren ya tabbatar da cewa dangane da adadin waɗanda suka rasu, ba za a iya faɗin adadi ba, har sai jami’ansu sun kammala bincike.

A shekaran jiya Lahadi ne tawagar gwamnan jihar Kaduna ta kai ziyarar gani da ido zuwa wannan gari na Tafa. Inda ya tattauna da masu ruwa da tsaki kan afkuwar lamarin. Duk wani ƙ oƙ ari da wakilinmu yayi don jin ta bakin mai magana da yawun gwamnan Jihar Kaduna, abin ya ci tura.

 

 

Exit mobile version